Gwamna Mai Mala Buni ya yi wa fursunoni 115 afuwa

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Lahadi - idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Jami'an Ukraine sun ce sojojin ƙasar sun shirya kai farmaki kan Rasha

    Sojojin Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an Ukraine sun ce sojojin kasar sun shirya kai farmaki kan Rasha.

    Ba su bayar da cikakken bayani ba da wa'adin da aka ɗiba na aiwatar da hakan amma sun ce tuni suka soma yin samame inda aka lalata wuraren ajiyar Rasha.

    Sun kuma ce a yan makonni masu zuwa za a iya ganin karin kutse daga yan Rasha da ke fada a bangaren yan Ukraine.

    Wani bidiyo da kwamandan sojoji ya wallafa ya sake karfafa sakon cewa lokaci ya yi da al'ummar Ukraine za su kwato abin da mallakinsu ne.

    A watannin da suka gabata, kasashen yamma sun kara yawan tallafin makaman da suke bai wa Ukraine.

  3. Kadoji sun afka tare da kashe mai kula da su

    Kadoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani mai gadin kadoji a arewacin Cambodia ya gamu da ajalinsa, bayan da ya faɗa komar wasu kadoji 40, a cewar 'yan sandan yankin.

    Luan Nam, mai shekaru 72, ya yi kokarin ɓare kwai a wajen shingen da kadjin suke, inda wata kada ta kama sandarsa tare da jawo shi cikinsu, a cewar 'yan sanda.

    Shugaban ‘yan sandan yankin Mey Savry, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, “Daga nan sauran kaoji suka yi tsalle tare far masa har ta kai ga mutuwarsa.

    Lamarin ya faru ne a kusa da garin Siem Reap a ranar Juma'a.

    An samu raunukan cizo a jikin Nam, inda har ta kai ba a iya gano ɗaya daga cikin hannayensa ba, in ji Mista Savry.

    Luan ya kasance shugaban kungiyar masu kiwon kadoji a yankin.

    A shekarar 2019, wata yarinya ‘yar shekara biyu ta mutu a lokacin da kadaji suka cinye ta a wata gona da ke yankin, kusa da shahararren gidan bauta na Angkor Wat.

  4. Yan takarar zagaye na biyu na zaɓen shugaban Turkiyya na ci gaba da caccakar juna

    Zaɓen shugaban Turkiyya

    Asalin hoton, CEMAL YURTTAS/DIA/GETTY IMAGES

    Yan takarar da za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban Turkiyya a gobe Lahadi na ci gaba da caccaka tare da zargin juna.

    Shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan ya zargi abokin hamayyarsa da ganawa da mayakan Kurdawa da aka haramta ba tare da bayar da wata hujja ba.

    Kemal Kılıçdaroğlu kuwa ya kira shugaban kasar a matsayin makaryaci kuma matsoraci.

    Wakilin BBC ya ce mista Erdogan na gudun kar magoya bayansa su ga kamar ta faru ta kare, yana jaddada musu cewa idan ba su fita zabe a gobe ba, toh kuwa ba zai yi nasara ba.

  5. Shugaba Buhari zai yi jawabin bankwana a ranar Lahadi

    Shugaba Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Ƙasa

    Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabin bankwana ga ƙasa baki-ɗaya a matsayin na shugaban ƙasa a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ya fitar, ta ce Buhari zai yi jawabin ne da misalin karfe 7 na safe.

    Sanarwar ta kuma buƙaci dukkan gidajen talabijin da radio da kuma sauran kafofin yaɗa labaru na zamani da su nuna jawabin ta hanyar haɗa tashoshinsu da gidan talabijin na ƙasa NTA da kuma gidan rediyon tarayya FRCN.

    A ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne, shugaba Buhari zai miƙa mulki ga sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, a daidai lokacin da yake kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu na shekara takwas.

  6. Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga karo na 11 a jere

    Bundesliga

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga karo na 11 a jere bayan da ta doke Cologne, inda ta sha gaban Borussia Dortmund a ranar karshe ta Gasar.

    Dortmund ta tashi kunnen doki 2-2 da Mainz, inda da ta samu nasara, za ta lashe kofinta na farko tun 2011-12.

    Jamal Musiala ne ya ci Bayern kwallon da ya ba ta nasara a minti na 89.

    Cologne ta dawo cikin wasan ne a fenaritin da ta samu bayan da Kingsley Coman ya ci kwallo, amma daga bisani Musiala ya ci mata kwallon da ya ba ta nasara.

    'Yan wasan Dortmund da magoya bayansu sun ji takaicin rashin lashe Bundesliga duk da tashi 2-2 da ta yi.

    Hakan ya kawo karshen kakar wasanni cikin nasara ga kociyan kungiyar Thomas Tuchel, wanda ya maye gurbin Julian Nagelsmann a watan Maris.

  7. Gwamna Mai Mala Buni ya yi wa fursunoni 115 afuwa

    Mai Mala Buni

    Asalin hoton, Mai Mala Buni

    Gwamnan Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya yi wa fursunoni 115 afuwa, waɗanda aka zaɓo daga gidajen yari daban-daban da ke faɗin jihar.

    Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa afuwar ta biyo bayan wani nazari da kwamitin da aka kafa kan hakkin jin kai karkashin jagorancin tsohon babban lauyan gwamnati kuma babban mai taimakawa gwamna na musamman kan harkokin shari’a, Barista Sale Samanja ya yi.

    Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Samanja ya ce afuwar da gwamnan ya yi ya, ta yi daidai da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin 1999 ya ba shi wanda aka yi wa kwaskwarima.

    Barista Samanja ya ce mutanen da aka yi wa afuwar sun yi farin ciki da kuma gode wa gwamnan, inda suka yi alkawarin amfani da ‘yancin da suka samu wajen gyara kura-kuran da suka yi a baya.

    Da yake karɓar rahoton kwamitin a gidan gwamnati da ke Damaturu, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana rahoton afuwar da aka yi wa fursunonin a matsayin muhimmin abu da kuma kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen rage cinkoso a gidajen gyaran hali.

    Buni ya ce irin waɗannan matakai da za su saukaka wajen gyaran halin fursunonin, inda ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wajen biyan ƙananan tarar da ke sanya da dama zuwa gidajen yari saboda babu halin biya.

    Gwamnan ya yi fatan cewa waɗanda aka sako sun koyi darasi kuma za su kaucewa maimaita abin da ya jefa su gidan yari.

    Ya yaba wa kwamitin bisa kokarinta wanda ya kai ga samun nasarar tantance fursunonin 115 da aka yi wa afuwa.

  8. Rasha ta lalata wani asibiti a birnin Dnipro na Ukraine a harin makami mai linzami

    Ƴakin Ukraine

    Akalla mutum biyu ne suka mutu yayin da wasu fiye da 30 suka jikkata a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan wani asibiti da ke birnin Dnipro na gabashin Ukraine, a cewar jami'an ƙasar.

    Shugaban yankin Serhiy Lysak, ya ce akwai yara maza biyu ƴan shekara uku da kuma shida cikin waɗanda suka jikkata.

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana harin a matsayin zalunci.

    Hare-haren da Rasha ke kai wa Ukraine sun ƙaru a 'yan makonnin nan.

  9. Hatsarin mota ya hallaka mutum huɗu a kan hanyar Lagos-Ibadan

    Hatsarin mota

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar mutum huɗu a wani hatsarin mota da ya afku kusa da wata jami'a a jihar a kan babban hanyar Legas zuwa Ibadan.

    An kuma samu mutum biyu da suka tsira a hatsrin.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa hatsarin ya afku ne da sanyin safiyar yau Asabar lokacin da wata moto ƙirar Lexus da kuma babbar motar dakon kaya suka garu.

    Shugabar wayar da kai da kuma kula da hanyoyi na hukumar, Florence Okpe, ta ce gudu fiye da ƙima da kuma amfani da wayar salula na cikin abubuwan da suka janyo hatsarin, bayan da mota ta ƙwace wa direban Lexus, inda ya afka wa babbar motar ta dakon kaya.

    Ya zuwa yanzu dai an ɗauki gawawwakin waɗanda suka mutu zuwa ɗakin hutu na wani asibiti da ke jihar.

  10. Dalilin da ya sa Majalisar Dattawan Najeriya ta yi zaman gaggawa ranar Asabar

    Ahmad Lawan

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya ce sun yi zaman gaggawa ne a yau Asabar da zimmar amincewa da ƙudirin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi da gwamnati ta gabatar musu.

    "Wannan ba zama ne da muka saba yi ba," in ji shi. "Abin da muke son yi shi ne amincewa da sabon ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi saboda tanadin dokar [ta yanzu] zai ƙare a ƙarshen watan Yuni.

    "Abubuwan da ke cikin dokar su ne tituna da gadoji, waɗanda ambaliyar ruwa da aka yi a 2022 ta rusa. Idan ba mu yi sauri ba ruwa ya sake lalata su, abu ne mai wuya a iya ceto su."

    Ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu da na uku, duka a zaman na yau. Sai dai Ahmad Lawan ya ce suna so su amince da shi tare da Majalisar Wakilai don a samu damar aiwatar da shi bayan wa'adin watan Yuni.

    Kazalika, sanatocin sun amince da ƙudirin yi wa Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) kwaskwarima, wanda shi ma ya tsallake karatu na ɗaya da na biyu da na uku.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Aikin kare gwamnatin Buhari da daɗi da kuma wuya - Garba Shehu

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Gane Mini Hanya

    Filin Gane Mini Hanya a wannan makon ya karɓi baƙuncin Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

  12. Dabbobin daji sun tilasta wa mutum 1,000 barin gidajensu a Mozambique

    Kada

    Asalin hoton, AFP

    Aƙalla mutum 1,000 ne ake sa ran za su bar gidajensu a tsakiyar Mozambique sakamakon hare-haren da suke fuskanta daga dabbobin daji.

    Gwamnan gundumar Marromeu da ke yankin Sofala ya ce gwamnati za ta kwashe iyalai 1,500 da suka fi shiga haɗarin hare-haren.

    Henriqueta de Rosário ta ce sun tabbatar da mutuwar mutum uku a wata ukun farko na wannan shekarar saboda harin dabbobin masu haɗari.

    "Rikici tsakanin 'yan Adam da dabbobin daji na ƙaruwa," a cewar Ms Rosano.

    Ta ƙara da cewa aƙalla mutum 400 ne zuwa yanzu suka saka amince su bar gidajen nasu da ke yankin.

  13. Jami'an tsaro sun kama mutum 10 kan 'satar' ɗanyen man fetur a Najeriya

    Mota ɗauke da ɗanyen man fetur

    Asalin hoton, @official_NSCDC

    Hukumar tsaro ta Civil Defense a Najeriya ta ce ta kama mutum 10 da zargin satar ɗanyen man fetur a Jihar Rivers da ke kudancin ƙasar.

    Kazalika, jami'an leƙen asiri na hukumar sun kama wata babbar mota da ke jigilar man, kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na Twitter.

    Bugu da ƙari, jami'an Civil Defense sun yi nasarar rusa wani rumbun ajiyar ɗanyen mai da ke yankin Borokiri na jihar ta Rivers.

    Najeriya na asarar biliyoyin naira duk wata saboda satar mai a yankin Neja-Delta, abin da ya sa Angola ta zarce ta wajen fitar da mai kasuwar duniya daga Nahiyar Afirka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Mun shekara takwas muna ceto yaran da 'yan bindiga suka sace - Buhari

    Buhari

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shafe shekara takwas tana yunƙurin ceto yaran da 'yan bindiga suka sace a wurare daban-daban.

    Buhari ya bayyana haka cikin saƙonsa na bikin Ranar Yara ta Duniya da ake yi a yau Asabar, yana mai cewa yana jin "raɗaɗin da iyaye ke ji" sakamakon matsalar tsaro da ta jawo yin garkuwa da ɗaliban.

    "Kuma ina jin raɗaɗi na rashi, da zaƙuwa, da ɓacin rai da matsalar tsaro ta jawo, wadda muka yi aiki tuƙuru don shawo kanta tsawon shekara takwas," a cewarsa cikin wasu jerin saƙonni a Twitter.

    Ya ƙara da cewa: "Cikin shekara takwas, mun mayar da hankali kan yara wajen tattaunawa da kuma yunƙurin ceto da yawa daga cikinsu bayan an yi garkuwa da su, kuma muka ci gaba da neman inda sauran suke."

    Shugaban ya ce "da ikon Allah sauran da ba a saka ba za su dawo".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Hanyoyin da za ki guje wa ciwon baya yayin goyon ciki

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Lafiya Zinariya:

    Filin Lafiya Zinariya na wannan makon ya tattauna kan matsalar ciwon baya ga mata masu ciki da kuma yadda za a guje mata.

  16. Majalisar Dattawan Najeriya na yin zaman gaggawa

    Ahmad Lawan

    Asalin hoton, Nigeria Senate

    'Yan Majalisar Dattawan Najeriya na gudanar zama na gaggawa a yau Asabar yayin da ya rage 'yan sa'o'i a rantsar da sabuwar gwamnati.

    Kamar yadda aka saba, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ne ke jagorantar zaman, inda tuni aka fara ƙaddamarwa da kuma nazari kan sababbi da tsofaffin ƙudirori.

    Cikin ƙudirorin da aka ƙaddamar a hantsin yau har da na yi wa dokar kasafin kuɗi kwaskwarima, inda ɓangaren gwamnati ya gabatar da buƙatar yin ƙwarya-ƙwaryan kasafin. Ya tsallake karatu na farko.

    Kazalika, akwai ƙudirin yi wa Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) kwaskwarima, wanda shi kuma ya tsallake karatu na ɗaya da na biyu da na uku. Hakan na nufin Majalisa ta amince da ƙudirin.

    Birnin Abuja ya cika da jami'an tsaro a shirye-shiryen rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Rushe masallaci ya jawo kisan mutum biyu a Habasha

    Ƙur'anai

    Asalin hoton, Getty Images

    An kashe mutum biyu a Addis Ababa, babban birnin Habasha, yayin zanga-zangar Allah-wadai da rushe masallacin birnin saboda wasu ayyuka a birnin.

    A cewar rahotanni, arangama ta ɓarke tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar a harabar Masallacin Anwar da ke arewacin birnin bayan Sallar Juma'a.

    Baya ga mutum biyu da aka kashe, an kuma jikkata wasu da dama ciki har da 'yan sanda a yankin Gas Tira.

    Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa mutanen sun yi ta ihun Allah-wadai da ayyukan.

    "Jami'an tsaro sun tsaurara tsaro a ƙofar shiga masallatai kafin fara zanga-zangar," in ji shaidun. "Abin da ya harzuƙa mutanen ke nan, inda suka fara jifan su da duwatsu."

    A shekarar da ta gabata ne hukumomi suka kaddamar da aikin haɗe garuruwa shiga da ke kewaye da birnin Addis Ababa wuri ɗaya, wanda suka yi wa laƙabi da "Chigar City". Hakan ya sa hukumomi fara rushe-rushe don gudanar da aikin.

  18. Rantsar da Tinubu: An bai wa ma'aikata hutu a Najeriya

    Tinubu da Buhari

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Shugaba mai jiran-gado Bola Tinubu ke nan (a hagu) da Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar 29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutun ma'aikata sakamakon bikin rantsar da shugaban ƙasa mai jiran-gado, Bola Ahmed Tinubu.

    Ministan Harkokin Cikin Gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya ce an ba da hutun ne saboda bikin murnar dimokuraɗiyya.

    Rabon da a yi hutu a ranar 29 ga watan Mayu tun 2018 - bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da Ranar Dimokuraɗiyya zuwa 12 ga watan Yuni - inda sai a ranar ake yin hutun.

    Babu tabbas ko ma'aikata za su sake samun hutun a 12 ga watan Yuni mai zuwa.

    Buhari ya ce ya ɗauki matakin ne don girmamawa da kuma tunawa da Moshood Abiola, wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga watan Yunin 1993 amma gwamnatin soja ta soke zaɓen.

    Tuni jami'an tsaro suka tsaurara tsaro a birnin Abuja kafin bikin rantsar da Bola Tinubu a ranar Litinin a matsayin shugaban Najeriya na 16.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Mun shirya ƙaddamar da harin ramuwar gayya kan Rasha - Ukraine

    Sojan Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Babban jami'in tsaron Ukraine ya ce ƙasarsa ta shirya kaddamar da manya hare-haren da aka dade ana jira a kan dakarun Rasha.

    Oleksiy Danilov ya shaida wa BBC cewa harin da aka shirya kaiwar zai bai wa Ukraine damar samun nasara a kan sojojin Rashar a yayin da take kokarin kwato yankunanta da aka mamaye.

    Bai bayyana ranar da za a kaddamar da hare-haren ba, amma ya ce za a iya ƙaddamar da su daga gobe Lahadi ko jibi, ko kuma nan da mako guda.

    An bai wa dubban sojojin Ukraine horo a kan harin ramuwar gayya, sannan aka ba su tankunan yaki da kuma manyan makamai wadanda aka shigarwa kasar daga kasashen Yamma.

  20. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi Umar Mikail ne ke muku barka da hantsin Asabar.

    Maraba da haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotanni daga sassan duniya.