Wannan shafi yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
'Na zaɓi Kilicdaroglu ne don makomar jikokina'
Asalin hoton, Shutterstock
Daruruwan magoyan bayan ɗan takarar ƙawancen jam'iyyun adawa Kemal Kilicdaroglu ne suka taru a rumfar da ɗan takarar ya kaɗa ƙuri'arsa a birnin Ankara, domin nuna goyon baya a gare shi.
Yayin da ya hallara rumfar zaɓen sun riƙa murna da shewa, tare da daukar hotunan mutumin da suke ganin zai farfado da dimokradiyyar ƙasar.
Wata dattijuwa da ta kaɗa ƙuri'arta a rumfar ta shaida wa BBC cewa ''Mun yi zaɓe ne saboda jikokinmu, su ne makomar ƙasarmu''.
''Idan jam'iyyar AKP (ta Erdogan) ta yi nasara to ƙasarmu za ta koma ƙasar Musulunci, kamar Afghanistan. Muna da yaƙinin cewa gobe za ta kasance ranar nasara ga Turkawa kuma zan yi rawa sosai, saboda murna'', in ji dattijuwar mai shekara 65
Mutum biyu sun yi ba-hayar ƙulli 193 na hodar ibilis a hannun NDLEA
Jami'an Hukumar da ke Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama mutum 185 a Abuja da Kano kan laifukan da suka shafi safarar ƙwaya.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce wasu 'yan kasuwa biyu da ke tsare a hannunta, kwana uku bayan kama su a filin jirgin saman Abuja, sun yi ba-hayar ƙulli 193 na hodar ibilis.
Haka kuma hukumar ta ce ta samu nasarar ƙwace wasu ƙullin hodar ibilis da aka yi niyyar fasa-ƙwaurinsu zuwa Saudiyya daga Canadana.
Hukumar ta kuma bayyana nasarar kamen da ta yi a fadin wasu jihohin ƙasar cikin makon da ya gabata.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Na yaba da yadda zaɓe ya gudana - Erdogan
Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yaba da yadda zaɓen shugaban ƙasar da na majalisar dokokin ƙasar ya gudana a yau
Mista Erdogan ya wallafa ashafinsa na Tuwita cewa ''An gudanar da zaɓen bisa tsarin da zai ƙarfafa dimokraɗiyyar ƙasarmu, muna godiya ga Allah''.
Ana hasashen cewa zafafatawar za ta fi zafi tsakanin Erdogan da ɗan takarar kawancen jam'iyyun adawa Kemal Kilicdaroglu.
Maki uku Man City ke bukata ta lashe Premier League
Rikicin Sudan: An kashe fiye da mutum 100 a yankin Darfur
Mummunan faɗa ya ɓarke a yankin Darfur na ƙasar Sudan, yayin da rahotonni ke cewa fiye da mutum 100 aka kashe a birnin El Geneina.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan wakilan ɓangarorin da ke yaki da juna a ƙasar sun amince da kare fararen hula tare da barin kayan agaji kaiwa zuwa gare su.
Kungiyar kare haƙƙin bil-dama a yankin na Darfur ta ce babban limamin birnin El Geneina na daga cikin gwamman mutanen da suka mutu a rikicin da ya ɓarke a birnin.
Hotuna sun nuna yadda gine-gine suka lalace bayan da aka yi musu ruwan hare-hare da ta sama.
Ana zargin wata ƙungiyar Larabawa mai alaƙa da dakarun RSF da ƙaddamar da hare-hare kan gidaje a birnin.
Kusan shekara 20 bayan kisan kiyashin da aka tafka a yankin, har yanzu Darfur na ci gaba da fuskantar rikice-rikice.
Kungiyoyin bayar da agaji na ci gaba da janyewa yayin da cibiyoyin lafiya suka kasance a rufe, sakamakon faɗan da ya ɓarke a tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.
Zaɓen Turkiyya: Su wane ne 'yan takarar da ke fafatawa da Erdogan?
Asalin hoton, Getty Images
Recep Tayyip Erdogan: Shi ne shugaban ƙasar na yanzu, ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Turkiyya a shekarar 2014, bayan ya kwashe shekara 11 a matsayin firaministan ƙasar tun daga shekarar 2003, lokacin da jam'iyyarsa ta AKP ta samu rinjaye a zaɓen majalisar dokokin ƙasar.
Kemal Kilicdaroglu: Dan takarar ƙawancen jam'iyyun adawa shida da ke da manyan 'yan takarkaru a muƙaman majalisar dokokin ƙasar. Tun shekarar 2010 ne Mista Kilicdaroglu ke jagorantar haɗakar jam'iyyun adawa a ƙasar.
Sinan Ogan: Dan gwagwarmayar kishin ƙasa, damarsa ta yin nasara a zaɓen ba ta da yawa.
Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Zaɓen Ghana: Jam'iyyar NDC ta zaɓi Mahama a matsayin ɗan takararta
Asalin hoton, FACEBOOK/JOHN DRAMANI MAHAMA
An zaɓi tsohon shugaban ƙasar Ghana John Mahama a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar adawa ta NDC a babban zaɓen ƙasar da ke tafe cikin shekara mai zuwa.
A ranar Lahadi ne aka ayyana John Mahama a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani da jam'iyyar ta gudanar, inda ya samu kashi 98.9 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen da aka gudanar jiya Asabar
John Mahamaya samu nasara ne a kan abokin takararsa tsohon magajin garin Kumasi Kojo Bonsu.
Shi kuwa ɗan takara na uku a zaɓen Dakta Kwabena Dufour janyewa ya yi daga takarar bayan da ya yi zargin aikata ba daidai ba atsarin gudanar da zaɓen.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita bayan samun nasara, Mista Mahama ya yi kiran samun haɗin kai a jam'iyyar.
Wannan shi ne karo na uku da Mista Mahama ke takara, a yunƙurin da yake yi na komawa kan mulki, tun bayan shan kaye da ya yi a shekarar 2016 a hannun shugaban ƙasar na yanzu Nana Akufo Addo, wanda zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu a shekara mai zuwa.
John Mahama ɗan siyasa ne da ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, sannan ya zama shugaban ƙasa bayan rasuwar shugaban ƙasar na wancan lokaci John Evans Atta Mills.
Ya tsaya takara a zaɓen 2012, inda ya yi nasara, sai dai wa'adi ɗaya kawai ya yi, kafin ya sha kaye a zaɓe 2016.
Najeriya ta kammala kwashe ɗalibanta da ke Sudan
Asalin hoton, NIDCOM/Twitter
Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da kammala aikin kwashe ɗalibai 'yan ƙasar da ke karatu a ƙasar Sudan Waɗanda ɓarkewar rikici tsakanin sojojin gwamnati da na RSF ya rutsa da su.
Ma'aikatar jin kai da kare afkuwar bala'i ta Najeriya da ta yi aikin kwashe daliban da haɗin gwiwar hukumar agajin gaggawa ta NEMA, da ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashen Sudan da Masar ne suka sanar da hakan.
Babban sakatare a ma'aikatar jin kai da kare afkuwar bala'i a Najeriya Dakta Nasiru Sani Gwarzo ya shaida wa BBC cewa sai da aka bi matakan da suka dace domin tabbatar da kariyar ɗaliban, kafin a fara kwashe su.
Ya ce jirgin da ya sauka a ranar Asabar shi ne jirgi na 15 kuma shi ne na ƙarshe da ya ƙwaso ɗaliban Najeriyar da ke karatu a Sudan.
''Jirage huɗu na farko da suka kwaso ɗailbai kusan 800, sun taso ne daga 'Aswan' na ƙasar Masar, sai kuma ragowar 14 da suka taso daga Port Sudan'', in ji shi.
Dakta Gwarzo ya ce sun kwaso duka wani ɗan Najeriya da ke Sudan wanda ya nemi taimakonsu, kuma ya kasance yana da takardu.
Ya ce kashi 95 cikin 100 na mutanen da suka kwaso Dalibai ne da ke karatu a ƙasar ta Sudan.kashi 95 cikin 100 na mutanen da suka kwaso Dalibai ne da ke karatu a ƙasar ta Sudan.
Dakta gwarzo ya ce ''matsalar da muka samu da masu motocin bas-bas ce ta haddasa tsaikon da aka samu wajen ƙwashe ɗaliban a kan lokaci''.
Amma duk da haka a cewarsa babu ƙasar da ta iya kwaso adadin mutanen da suka kai na Najeriya a cikin wannan lokacin.
Game da matsayin karatun ɗaliban kuma dakta gwarzo ya ce sun tattauna da ma'aikatar ilimi ta ƙasar, wadda ya ce ta aiko musu da wani jadawali da za su rubuta sunayen ɗaliban, domin duba yiwuwar yadda za a tallafa wa ɗaliban.
Shin me ake nufi da matakin tsuke bakin aljihu?
Bayanan sautilatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Makiyaya sun kashe zakuna shida da suka addabi ƙauyensu
Makiyaya sun kashe wasu zakuna shida a gundumar Kajiado na ƙasar Kenya, bayan da zakunan suka kwashe tsawon daren Asabar suna far wa mazauna ƙauyen Nashipa.
Rahotonni sun ce zakuna 11 da suka tsere daga gandun dajin 'Amboseli National park', suka afka wa ƙauyen tare da addabar al'ummar ƙauyen na tsawon dare guda.
Zakunan sun yi ta far wa gidajen mutane inda suka kashe tumaki 11 tare da kare guda, a wani lamari da wani mazaunin ƙauyen ya bayyana da 'daren subhana'.
"Yunkurin da masu tumakin suka yi na ƙubutar da su ya ci-tura, tumaki ne da suka tsallake-rijiya-da-baya daga masifar fari da ƙasarmu ke fuskanta, amma sai ga shi sun ƙare a matsayin kalacin zakuna,'' in ji wani mazaunin ƙauyen.
A ranar Asabar da safe ne gwamman mazauna ƙauyen suka ɗauke da kwari da baka da wasu makaman suka ƙaddamar da farautar zakunan tare da kashe shida daga cikinsu.
Jami'an kula da gandun dajin ƙasar da jagororin kauyen da sauran masu ruwa da tsaki sun gudanar da ganawar gaggawa kan lamarin da maraicen ranar Asabar.
Ukraine ba ta da burin kai hari cikin Rasha - Zelensky
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ƙasarsa ba ta da burin kai hare-hare cikin Rasha.
Mista Zelensky na wannan magana ne a lokacin da ya kai wata ziyara ƙasar Jamus, wadda ta bai wa ƙasarsa tallafin manyan kayayyakin tsaro.
"Ba ma kai hari cikin ƙasar Rasha," kamar yadda ya bayyana jim-kaɗan bayan ganawarsa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz.
"Muna kai hare-hare ne kan garuruwanmu da ke hannunsu domin mu ƙwato su'', in ji Mista Zelensky.
A nasa ɓangare shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sha alwashin mara wa Ukraine baya, tare da alƙawarta wa ƙasar makamai da kuɗinsu ya kai dala biliyan 2.4.
Wannna ya haɗa da manyan tankoki da jiragen yaƙi domin kare Ukraine daga hare-haren yau-da-kullum da Rasha ake kai mata da jirage marasa matuƙa.
Mista Zelensky ya bayyana wannan sabon alƙawari da cewa ''babban tallafi tun bayan mamayar Rasha a Ukraine a watan Fabrairun bara.
Zaɓen Turkiyya: Manyan 'yan takara sun kaɗa ƙuri'unsu
Asalin hoton, Getty Images
Sugaban ƙasar Turkiyya kuma ɗan takarar jam'iyyar 'People's Alliance', Recep Tayyip Erdoğan, ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen shugaban ƙasar da ke gudana a faɗin ƙasar.
Shi ma babban abokin hamayyarsa ɗan takarar jam'iyyar 'National Alliance' Kemal Kılıçdaroğlu, ya kaɗa tasa ƙuri'ar a birnin Ankara.
Erdogan tare da matarsa Emine Erdoğan sun kaɗa tasu ƙuri'ar ne a gundumar Üsküdar da ke birnin Santanbul.
Bayan kaɗa ƙuri'ar tasa Mista Erdogan ya ce ya samu labari daga ministan cikin gida na ƙasar cewa zaɓen yana tafiya yadda ya kamata.
Kimanin masu zaɓe kusan miliyan 64 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen.
'Halin da muka shiga daga Sudan zuwa Najeriya'
A yayin da Najeriya ta kammala ƙwasar ɗalibanta da ke Turkiyya, wasu ɗaliban da suka koma ƙasar sun bayyana irin halin da suka shiga a lokacin da suke Sudan.
Muhammad Kabiru ɗaya ne daga cikin ɗaliban Najeriya da suka koma ƙasar daga Sudan ya ce sun ga abubuwa daban-daban a kan hanyarsu ta barin Sudan
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
An kashe fitacciyar mawaƙiyar Sudan Shaden Gardood
Asalin hoton, SHADEN GARDOOD/FACEBOOK
An kashe ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Sudan Shaden Gardood, a wata musayar wuta tsakanin ɓangarori biyun da ke faɗa da juna a ƙasar.
Misis Gardood ta rasa ranta ranar Juma'a a birnin Omdurman sakamakon faɗa tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.
Mutuwar mawaƙiyar mai shekara 37 na zuwa ne kwana guda bayan ɓangarorin da ke rikici da juna sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen wahalar da fararen hula ke fuskanta.
A cikin watan Afrilu ne dai faɗa ya ɓarke a ƙasar tsakanin ɓangarorin biyu.
Gardood dai na zaune ne a al-Hashmab, inda dakarun RSF ke ƙaruwa a 'yan kwanakin nan.
Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta an ga Gardoon na ɓuya tare da kiran ɗanta ya matsa daga kusa da taga domin kauce wa harsasai, yayin da ake ci gaba da luguden wuta a birnin.
Al'ummar Turkiyya na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa
Al'ummar ƙasar Turkiyya na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar mafi mahimmanci, wanda zai fayyace ko shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan zai ci gaba da mulki bayan kwashe shekarar 20 yana jagorantar ƙasar.
An samu rahotonnin fitowar amsu kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe tun kafin a fara kaɗa ƙuri'a.
Wani jami'a a birnin Santanbul ya ce Turkawa na cike da yunwar Dimokraɗiyya a wannen zaɓe.
Akwai masu zaɓe kusan miliyan 64 a ƙasar.
Hauhawar farashin kayayyaki na daga cikin abubuwan da suka kankane gangamin yaƙin neman zaɓen.
Babban abokin hamayyar shugaba Erdogan Kemal Kilicdaroglu, ya alƙawarta rage ƙarfin ikon da mista Erdogan ya samar wa kansa a ƙasar, bayan tsallake-rijiya-da-baya a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a shekrar 2016.
A cikin wani bidiyo da ka yaɗa an ga Mista Erdogan na jaddada dokokin zaɓen a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron masu ibada da maraicen ranar Asabar.
Domin samun nasarar zaɓen dole ne ɗan takara ya samu fiye da kshi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, ko kuma a je zagaye na biyu cikin mako biyu masu zuwa.
Sallama
Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sasan duniya.
Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.