Hukumar Alhazan Najeriya ta amince da ƙarin dala 250 kan kujerar aikin hajji

Wannan shafi yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Yadda ake zaɓen shugabannin majalisar dokokin Najeriya

    Yayin da ake dab da rantsar da sabuwar majalisar dokokin Najeriya ta 10, a yanzu hankali ya karkata kan shugabancin majalisar.

    Shin kun san matakan da ake bi domin zaɓar shugabannin majalisar dokokin Najeriya?

    A cikin wannan bidiyon mun kawo muku bayanai dalla-dalla kan yadda ake zaɓar shugabannin majalisar.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  2. An kwaso ƙarin 'yan Najeriya 125 daga Sudan

    "Yan Najeriya daga sudan

    Asalin hoton, NIDCOM/Twitter

    Wasu ƙarin 'yan Najeriya 125 sun isa ƙasar daga Sudan.

    Mutanen waɗanda jirgin Tarco B737-300 ya ɗauko daga Port Sudan sun sauka a filin jirgin saman Abuja da tsakar ranar Asabar.

    A yanzu adadin 'yan ƙasar da aka kwaso daga Sudan ya kai 2,371.

    Jami'an shige da fice da na hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA, da jami'an hukumar kula da 'yan gudun hijira ta ƙasar ne suka tarbe su a filin jirgin.

    A ranar uku ga watan Mayu ne jirgin farko ɗauke da 'yan ƙasar daga Sudan ya sauka a filin jirgin Abuja.

    Tun daga ranar ne kuma ake ta jigilar ƙwasar ɗaliban ƙasar waɗanda suka maƙale a ƙasar sakamakon faɗan da ya ɓarke tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF masu sanye da kayan sarki.

  3. Erdogan zai kammala yaƙin neman zaɓensa a masallacin Hagia Sophia

    Erdogan

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai kammala gangamin yaƙin neman zaɓensa da maraicen ranar Laraba a masallacin Hagia Sophia da ke birnin Santanbul.

    A shekarar 2019 majalisar ƙoli ta ƙasar ta hana yunƙurin mayar da Hagia Sophia wurin yawon buɗe ido

    Ana kallon Hagia Sophia - wanda aka gina kusan shekara 1500 da suka gabata - a matsayin wuri mai alfarma a ƙasar musamman ga mabiya addinin Musulunci da na Kirista.

  4. Hukumar Alhazai ta amince da ƙarin dala 250 kan kujerar aikin hajji

    Hausa

    Asalin hoton, NAHCON

    Hukumar Alhazai ta Najeriya ta amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajjn bana, kamar yadda kamfanonin jiragen aman da za su yi jigilar alhazan suka nema.

    Shugaban hukumar Alhzan ƙasar Zikrullah Hassan ne ya tabbatar da haka a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki na hukumar a Abuja babban birnin ƙasar.

    Ya ce ''Bayan tattaunawa mai zurfi tare da kamfanonin da za su yi jigilar maniyyatan mun amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajji ta wannan shekara''.

    Kwamishinan kuɗi da ma'aikata na hukumar Nura Hassan Yakasai, ya shaida wa BBC cewa kamfanonin jigilar alhazan ne suka buƙaci hakan saboda yaƙin da ake a Sudan, ya sanya dole sai sun zagaya, ba za su bi ta sararin samaniyar Sudan ba.

    Ya ce kamfanonin jiragen sun ce sai sun yi zagaye na ƙarin sa'o'i biyu, kuma a kowacce sa'a kamfanonin sun ce jiragen kan sha mai na kusan miliyan takwas.

    A don haka ne hukumar da kamfanonin jiragen suka amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujera.

    Haka kuma ya tabbatar da ƙarin kuɗin biza da aka yi na wajen dala 65.

    To sai dai ya ce hukumar na tattaunawa da gwamnati domin ganin yadda za a biya ƙarin ƙuɗaɗen.

  5. Keke mai ƙafa uku da mahaya dawaki a cikin hotunan Afirka

  6. Firaministan Pakistan ya bayar da umarnin kama masu zanga-zanga

    Shahbaz Sharif

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ya umarci hukumomi su gano tare da kama wadanda ke da hannu a rikicin da ya ɓarke a cikin makon da ya gabata bayan kama tsohon firaministan ƙasar Imran Khan.

    Kamfanin dillancin labarai na Retuers ya ruwaito Mista Sharif na cewa tarzomar da ta ɓarke ta haddasa asarari rai a ƙasar.

    Da maraicen ranar Juma'a ne dai Khan ya nufi birnin Lahore mahaifarsa jim kaɗan bayan da kotu ta bayar da belinsa.

    Kama shi da aka yi ranar Talatar da ta gabata ya haddasa barkewar zanga-zangar magoya bayansa a faɗin ƙasar.

  7. Gane Mini Hanya: Hira da shugaban Nijar Bazoum Mohamed

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin Sauraron shirin
  8. Firaministar Finland da ke son kashe aurenta

  9. FRSC ta karyata fara amfani da dokokin Shari'a wajen hukunta masu karya dokar hanya

    Dauda BIU

    Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Najeriya FRSC ta nesanta kanta da wani labari da ke cewa hukumar na shirin fara amfanin da dokokin shari'ar musulunci wajen hukunta masu karya dokokin tuƙi da amfani da hanya

    A cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Bisi Kazeem, aka kuma wallafa a shafin hukumar na Tuwita , ta ce wannan labari ba shi da alaƙa da hukumar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    A cikin makon da ya gabata ne dai wasu jaridun ƙasar suka ruwaito wani kwamandan hukumar reshen wata jiha a ƙasar na kira da fara amfani da dokokin shari'ar musulunci ga masu karya dokokin tuƙi a ƙasar.

    Yana mai cewa dokokin hukumar sun gaza ta fuskar hukunta masu laifukan, a don haka ne yake kira da hukumar ta fara amfani da dokokin shari'ar musulunci.

    To sai dai a sanarwar hukumar ta fitar, ta ce babban kwamandan hukumar na ƙasa Dauda Ali Biu ya umarci kwamandan da ya yi wannan furuci da ya hallara a shalkwatar hukumar da ke Abuja, domin a cewar sanarwar kalaman nasa sun saɓa dokokin hukumar.

    Sanarwar ta ce dokoki da ƙa'idojin da suka kafa hukumar ba dokoki ba ne na wani addini ko wani yanki na ƙasar.

    A don haka hukumar ke kira ga al'umma da su yi watsi da furucin da jami'in ya yi , tana mai cewa ya saɓa wa dokoki da ƙa'idojin hukumar

  10. Za a ci gaba da tattaunawar sulhu Sudan

    A ƙarshen mako ake sa ran komawa teburin sulhu domin ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓagarori biyun da ke faɗa da juna a ƙasar Sudan.

    Duk da yarjejeniyar kare fararen hula da barin kayan agaji kai wa garesu, an ci gaba da faɗa a wasu sassan birnin Khartoum.

    Inda Jiragen sama ke ta ruwan harsasai ta sama, sannan sojoji na ta ɓarin wuta a wasu titunan birnin.

    Bangaren lafiyar ƙasar ya samu koma baya, yayin da asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya suka daina aiki.

    Farashin magunguna ya yi tashin gwauron zabo, sakamakon ƙarancinsa, yayin da mutane ke cikin mayuwacin hali.

    An zargi duka ɓangarori biyun da ke yaƙi da juna da take haƙƙin bil-adama a lokacin yaƙin.

  11. Zelensky ya isa Italiya domin ganawa da Fafaroma Francis

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya isa birnin Rome domin ganawa da shugabannin siyasa, tare kuma ga ziyartar fafaroma Francis a fadarsa ta Vatican.

    Mista Zelensky ya wallafa a shafinsa na Tuwita, jim kaɗan bayan saukar a birnin Rome cewa ''ziyara ce mai matuƙar muhimmanci a yayin da Ukraine ke tunkarar nasara''.

    A yayin ziyarar an tsara shugaban na Ukraine zai gana da firaministan ƙasar Giorgia Meloni, da shugaban ƙasa Sergio Mattarella, sannan zai je fadar Vatican domin ganawa da Fafaroma Francis.

    An tsaurara matakan tsaro a birnin yayin ziyarar, inda aka jibge 'yan sanda sama da 1,000, sannan an hana jiragen sama a shawagi a sararin samaniyar birnin.

    Fafaroma Francis ya sha cewa fadarsa a shirye take domin shiga tsakani a tattaunawar sulhu tsakanin Ukraine da Rasha.

    Ganawar da Zelensky zai yi fa Fafaroma Francis ranar Asabar ita ce ta farko tun bayan mamayar Rasha a Ukraine.

    Ziyarar na zuwa ne bayan da Rasha ta ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama zuwa birnin Kyiv da sauran biranen Ukraine cikin daren da ya gabata.

  12. Mummunar guguwa ta tilasta kwashe kusan mutum 500,000 daga muhallansu

    Bangladesh

    An kwashe kusan mutum 500,000 daga kudu maso gabashin Bangladesh sakamakon mummunar guguwar da ta afka wa yankin, lamarin da ke zama babbar barazana ga sansanonin 'yan gudun hijira da ke wurin.

    Mahaukaciyar guguwar da aka yi wa laƙabi da 'Mocha' mai saurin gaske, wadda tuni har ta tsallaka kusa da bakin ruwa da ke Bengal.

    Lamarin da masu hasashe ke fargabar cewar zai iya janyo ambaliya

    A gobe Lahadi ake hasashen mummunar guguwar za ta isa iyakar Bangladesh da Myanmar, inda za ta yi tafiyar kilomita 170 cikin sa’a guda.

    Haka kuma ana cike da fargabar cewa guguwar za ta fada wa wani sansanin ‘yan gudun hijirar ƙabilar Rohingya ke fakewa.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce tuni ta aike da dubban ma’ikatan sa kai domin taimaka wa ‘yan gudun hijirar.

  13. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da wannan lokaci.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sasan duniya.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.