Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan sanda sun kama matashin da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano

Wannan shafi ne da zai riƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Buhari Muhammad Fagge

  1. Jakadan Sudan ya roƙi ƴan Najeriya su koma ƙasar idan ƙura ta lafa

    Jakadan Sudan a Najeriya, Muhammad Yusuf, ya roki ‘yan Najeriya da ke dawowa daga ƙasar da ke fama da rikici da su yi hakuri su koma idan al’amura suka lafa.

    Da yake magana a ranar Alhamis bayan dawowar wasu ‘yan Najeriya daga ƙasar, Mista Yusuf ya bukace su da su koma karatu tare da buɗe sana’o’insu bayan an kawo karshen faɗan da ake yi tsakanin sojoji da dakarun RSF.

    Ya bukace su da su ɗauki Sudan a matsayin kasarsu ta biyu, yana mai nuna ƙwarin gwiwar cewa za a shawo kan faɗan nan ba da daɗewa ba.

    A yau Juma’a ne ake sa ran wasu ‘yan Najeriya da suka maƙale a Sudan ɗin za su koma gida.

  2. Japan ta yi alkawarin taimaka wa Mozambique a yaƙi da ta'addanci

    Firaministan Japan Fumio Kishida ya ce ƙasarsa a shirye take ta taimaka wa Mozambique wajen yaki da ta'addanci.

    Firaministan Japan na ziyara a Mozambique a wani ɓangare na rangadin kwanaki shida da ya kai wasu ƙasashen Afirka uku wato Ghana da Kenya da kuma Masar.

    Ya ce ƙasar Japan na da shirye wajen bayar da kuɗaɗe a yaki da ta'addanci a arewacin lardin Cabo Delgado, wanda zai bai wa kamfanonin ƙasar Japan da ke cikin haɗin gwiwar kamfanonin da ke amfani da iskar gas a rafin Rovuma damar gudanar da ayyukansu cikin yanayi mai kyau.

    Masu iƙirarin jihadi sun shafe shekaru da dama suna yi wa lardin da ke arewacin ƙasar ƙawanya.

    Mista Kishida da shugaban Mozambique Filipe Nyusi sun yi magana game da bukatar masu zuba jari daga Japan a ɓangaren tattalin arziki, da nufin karafafa alaƙar ƙasashen biyu.

    Mista Nyusi ya bukaci ƴan Japan da su duba yiwuwar zuba jari a fannin sufuri da noma da masana'antu da kuma yawon buɗe ido.

  3. Kotu a Birtaniya za ta yanke wa Ekweremadu da matarsa hukunci a yau

    A yau ne kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey da ke Birtaniya za ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa ​​Beatrice Ekweremadu da wani likita hukunci.

    Wannan ya biyo bayan samun ɗan majalisar dattijan da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam a watan Maris.

    Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda, inda ake sa ran yanke musu hukunci a karon farko a irin dokokin bauta ta zamani.

    Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.

    An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London.

    Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya.

  4. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar wannan shafi barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj Babbar Rana.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Ahmad Tijjani Bawage.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.