Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan sandan Najeriya sun kama Hudu Ari

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Ahmad Tijjani Bawage, Nabeela Mukhtar Uba and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Samar da ayyukan yi ba ya cikin haƙƙokin gwamnati – Adesina

    Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya ce samar da ayyukan yi ga 'yan ƙasa ba ya cikin haƙƙoƙin da suka rataya a wuyan gwamnati.

    Mista Adesina ya bayyana hakan ne a shirin ‘The Morning Show’ na gidan talbijin din Arise TV, lokacin da yake magana game da nasarorin da gwamnatin Shugaba Buhari ta samu a cikin shekara takwas.

    Adesina ya ce abin da kawai gwamnati za ta yi shi ne samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanoni masu zaman kansu don su samar da ayyuka.

    “Mafi yawan ayyukan da ake so ana samun su ne a kamfanoni masu zaman kansu. matuƙar aka samu kyakkyawan yanayi, kamfanoni masu zaman kansu ne za su samar da ayyukan yi''.

    Mista Adesina ya kuma ce gwamnatin Buhari ta cimma nasarori a ɓangarori da dama da suka haɗar da ɓagaren mai da albarkatun iskar gas, da ayyukan more rayuwa da samar da dokoki da tsaro.

  2. Rikicin Sudan: Fararen hula 100,000 sun tsere wa faɗa - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 100,000 ne suka tsere daga Sudan tun bayan ɓarkewar ƙazamin faɗa tsakanin dakarun da ke faɗa da juna a ƙasar.

    Jami`ai sun yi gargaɗin cewa za a fuskanci mummunan bala`i idan ba a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a kasar ba.

    Rahotonni sun ce wasu ƙarai mutum 334,000 sun rasa muhallansu a faɗin ƙasar.

    Ana ci gaba da gwabza faɗa a babban birnin ƙasar, Khartoum, tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF, duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wuta.

    A ranar Litinin, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Sudan, Volker Perthes, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, ɓangarorin biyu sun amince su shiga tattaunawar sulhu domin cimma dawwamamme kuma ingantaccen zaman lafiya a ƙasar.

    Ya ƙara da cewa akwai yiwuwar Saudiyya ta zama ƙasar da za ta karɓi baƙuncin tattaunawar sulhun.

    Idan har aka samu nasarar yin tattaunawar, za ta kasance ganawa ta farko da ɓangarorin biyu suka yi tun bayan ɓarkewar rikicin.

    Sama da mutum 500 ne aka kashe yayin da wasu sama da 4,000 suka jikkata a fadan, kamar yadda ma`aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana.

    An kasa yin aiki da yarjejeniyoyin tsagaita wuta da dama, yayin da sojoji ke ci gaba da yi wa birnin Khartoum luguden wuta ta sama a ƙoƙarin da suke yi na karya lagwan dakarun RSF

  3. Mutum 80,000 za su rubuta jarrabwar JAMB ranar 6 ga watan Mayu

    Kusan mutum 80,000 ne za su rubuta jarrabawar JAMB da aka sake tsara rubutawa ranar 6 ga watan Mayu.

    A cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama'a na hukumar Fabian Benjamin ya fitar, ya ce an samu jinkirin ne sakamakon aikin tantance sakamakon jarrabawar da aka rubuta.

    Sanarwar ta ce ɗaliban da aka tantance a cibiyoyin rubuta jarrabawar, amma ba su rubuta jarrabawar ba, da waɗanda ba a tantance bayanansu ba, da waɗanda aka samu saɓanin bayanansa za su samu saƙonnin rubuta jarrabawar.

    Sanarwar ta ce “Waɗanda suka samu matsaloli a lokacin rubuta jarrabawarsu, ba za su ga sakamakonsu ba, a maimakon haka za su samu saƙon sake rubuta jarrabawar.

    Hukumar ta ce sakamakon zaman gaggawa da ta yi ranar 30 ga watan Afrilu, ta saka ranar 6 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a sake rubuta jarrabawar ga waɗanda ba su rubuta jarrabarwa ba.

    Sanarwar ta kuma yi kira ga ɗaliban da abin ya shafa su fitar da takardun bayanansu na jarrabawar tsakanin 4 zuwa 5 ga watan Mayu, domin sanin lokaci da kuma wurin da za su rubuta jarrabawar.

  4. Legas ta wallafa sunaye da hotunan masu fyaɗe a jihar

    Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta wallafa sunayen wasu mutum uku da aka samu da laifukan fyaɗe a jihar.

    Hukumar Yaƙi da Laifukan cin Zarafi ta jihar ce ta wallafa sunayen mutanen uku a shafinta na Tuwita

    Hukumar ta wallafa sunaye da hotunan mutanen tare da irin nau'in laifukan da suka aikata da irin hukuncin da kotu ta yanke musu.

    Ɗaya daga cikinsu mai suna Idowu Daniel, an same shi da laifin cin zarafi ta hanyar lalata, inda kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai.

    Na biyun mai suna Moses Olawale wanda aka samu da laifin lalata ƙaramar yarinya, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekarar 37 a gidan yarin.

    Sai kuma Akin Isaac, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 21 bayan da aka same shi da laifin fyaɗen.

    Hukumar da ke Yaƙi da laifukan cin zarafi ta jihar ta kuma yi kira ga al'ummar jihar da su riƙa kai masu aikata irin wannan laifi gaban kotu don su girbi abin da suka shuka.

    “Mu ci gaba da nema wa kanmu da waɗada aka ɓata wa rayuwa adalci a gaban kotuna,” in ji hukumar.

    A watan Mayun shekarar 2022 ne hukumar ta bayyana aniyarta ta fara wallafa sunaye da hotunan masu aikata laifukan cin zarafi a shafukanta.

  5. Ban yi nadamar bayyana Binani a matsayin gwamna ba - Hudu Ari

  6. Wani fursuna ya mutu bayan yajin cin abinci na kwana 86

    Wani fursuna ɗan ƙasar Falasɗinu ya rasu a gidan yarin Isra'ila sakamakon yajin cin abinci na kwana 86.

    Khader Adnan babban ƙusa ne a ƙungiyar masu iƙirarin jihadi, wanda Isra'ila ta zarga da laifukan ta'addanci.

    Hukumomin gidan yarin Isra'ila sun ce fursunan ya ƙi amincewa a yi masa magani, kafin a same shi cikin mawuyacin hali a ɗakin da yake ɗaure a gidan yarin ranar Talata.

    Firaministan Falasɗinu ya zargi Isra'ila da kisan Adnan ''da gangan'' yayin da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta yi barazanar ɗaukar fansa a kan isra'ila.

    Adnan mai shekara 44 - wanda ke zaune a arewacin yamma da gaɓar kogin Jodan - ya kwashe fiye da shekara 20 ana ɗaure shi a gidajen yarin Isra'ila.

    Sau huɗu yana shiga yajin cin abinci a baya, lamarin da ya sa sunansa ya yi fice a Falasɗinu.

    Yajin cin abinci ga fursunonin Falasɗinu da ke ɗaure a gidajen yarin Isra'ila abu ne da aka saba gani, to sai dai a 'yan shekarun baya-bayan nan an samu raguwar mace-macensu, sakamakon taimakon magani da aka ba su.

  7. Dogarin minista ya harbe ubangidansa

    Wani sojan ƙasar Uganda ya harbe minista da yake karewa a ƙasar.

    An harbe ƙaramin ministan ƙwadagon ƙasar Kanal Charles Okello Engola mai ritaya, a gidansa da ke Kampala babban birnin ƙasar, ranar Talata da Safe.

    Kawo yanzu ba a samu rahoton wani saɓanin da ya shiga tsakanin sojan da kuma ubangidan nasa ba.

    Shaidun gani da ido sun ce sojan ya ci gaba da harbi a sama bayan harbe ministan, kafin daga bisani ya kashe kansa.

    Rahotonni sun ce mutane da dama sun jikkata a lamarin.

    Bidiyoyin da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane suka taru a wajen da lamarin ya faru cikin alhini.

  8. Ban yi nadamar aiki na a Adamawa ba - Hudu Ari

    Shugaban hukumar zaben ta INEC a jihar Adamawa da aka dakatar, Barrister Hudu Yunusa Ari ya musanta zargin da ake yi cewa ya karbi cin hanci na naira biliyan biyu don ayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaben na gwamnan jihar Adamawa.

    Hudu ya ce ba ya nadama ko kadan game da matakin da ya dauka na sanar da sakamakon zaben gwamnan da aka yi a jihar ana tsakiyar tattara sakamako.

    Barrister Hudu Yunusa wanda rundunar `yan sanda ke nema ya ce doka ce ta ba shi hurumin sanar da sakamakon.

    Ya kara da cewa a shirye yake ya mika kansa ga rundunar 'yan sandan Najeriya da ke nemansa nan ba da jimawa ba.

  9. Cutar Lassa ta kashe mutum 154 a Najeriya - NCDC

    Cibiyar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce cutar zazzaɓin lassa ta halaka mutum 154 a cikin jihohin ƙasar 26 tun farkon shekarar da muke ciki.

    A cikin rahoton yanayin cutar da cibiyar ta fitar ranar Litinin, NCDC ta ce a cikin watanni huɗun farko na shekarar 2023, an samu masu ɗauke da cutar 897.

    Cibiyar ta ce jihohin da aka samu cutar sun haɗar da Ondo da Edo da Bauchi da Taraba da Benue da Plateau da Ebonyi da Nassarawa da Kogi da Taraba da Gombe da Enugu da Kano da Jigawa da sauransu.

    Rahoton ya ce, “tun daga satin farko zuwa 16 a wannan shekarar an samu mutuwar mutum 154''.

    NCDC ta ce an samu kashi 72 cikin 100 da cutar a jihohi uku da suka haɗar da Ondo da Edo da kuma Bauchi, inda ka samu kashi 28 daga jihohi 23.

    Rahoton ya ce adadin masu ɗauke da cutar ya ƙaru idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci a shekarar 2022.

  10. Hukumar Abinci ta MDD za ta ci gaba da ayyukanta a Sudan

    Hukumar Abinci ta majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta maido da ayyukanta a Sudan yayin da yaƙi a ƙasar ke yi wa miliyoyin mutane barazanar faɗawa ƙangin yunwa.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin hukumar ta ce tana sa ran fara rabar da abinci a jihohin Gedaref da Gezira da Kassala da kuma jihar White Nile a cikin kwanaki masu zuwa.

    “Za mu ɗauki matakai domin tabbatar da kare lafiyar ma'aikatanmu da ƙawayenmu yayin da muƙe ƙoƙarin taimaka miliyoyin mutane da ke cikin tsananin buƙatar taimakon'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Hukumar ta dakatar da ayyukanta a ƙasar ne tun a ranar farko da aka fara yaƙin bayan da aka kashe ma'aikatanta uku.

    Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana cewa mutum miliyan 15 na cikin tsananin buƙatar abinci da rashin tsaro, tun kafin ɓarkewar rikicin.

    Ta kuma bayyana cewa adadin zai ƙara yayin da ake ci gaba da faɗan.

  11. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa tare da ku a daidai wannan lokaci.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa