Ƴan Najeriya 30,000 na neman diyya kan matsalar malalar mai

Asalin hoton, PA Media
Alƙalai a Kotun Ƙolin London sun soma sauraron ƙarar da za ta tantance ko kusan ƴan Najeriya 30,000 suna iya neman diyya daga babban kamfanin mai na Shell saboda irin ɓarnar da malalar mai ya yi musu a 2011.
Al'ummar yankunan da ke gaɓar ruwa a jihohin Bayelsa da Delta sun ce filayensu sun lalace matuƙa sanadiyyar malalar man.
Wani hukunci da kotun ɗaukaka ƙara a London ta yanke tun farko ya ce an ɗauki lokaci mai tsawo wajen shigar da ƙarar tun bayan afkuwar lamarin.
A ƙarƙashin dokokin Ingila, mai ƙara na iya neman diyya kan ɓarnar da aka yi wa dukiyarsa amma kar ya wuce shekara shida da faruwar ɓarnar.
Kimanin gangar mai 40,000 ne ya malale a cikin teku abin da ya sa ya zama malalar mai mafi girma da aka taba samu a Najeriya.
Al'ummar sun yi iƙirarin cewa lamarin na ci gaba da haifar musu da ɓarna ga filayensu da kuma ruwan shansu a don haka ya kamata a ƙyale su nemi diyya.















