Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan Najeriya za su yi kewar Buhari idan ya gama mulki – Garba Shehu

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Saudiyya ta gargaɗi masu ɗaukar hoto a lokacin ziyarar ibada

    Hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta Saudiyya ta yi kira ga masu ziyarar ibada zuwa wurare masu alfarma da su martaba darajar wuraren.

    Sannan kuma su bi dokoki wajen ɗaurar hotunan.

    Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su ɓige da ɗaukar hotuna, a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su ƙasa mai tsarkin.

    Haka kuma hukumar ta gargaɗi masu ɗaukar hotunan da su guji haɗawa da wasu mutanen a cikin hoton nasu, ba tare da izini ba.

    Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don ɗaukar hoto a wuraren da jama'a da dama suka taru, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama'a a wuraren.

    A baya-bayan nan dai mutane sun ɓullo da salon ɗaukar hotuna a lokacin ziyarar ibada zuwa ƙasa mai tsarkin tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta.

    Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa zai iya zama 'Riya', abin da kuma a cewar malaman zai iya ɓata wa mutanen ibadar tasu.

  2. Za a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin Najeriya - Nimet

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a faɗin wasu jihohin ƙasar ƙasar.

    Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar.

    Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara.

    Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno.

    A cikin wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Lahadi a Abuja, ta ce hukumar ta lura da cewa yanayin zafin rana zai kai maki 40 a ma’aunin celcius a cikin kwanaki biyu masu zuwa.

    Nimet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun haɗa da wasu sassan Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa.

    NiMet ta yi gargaɗin cewa jihohi kamar a Bauchi da Gombe da kuma Adamawa na cikin haɗarin rashin jin daɗi musamman a ɓangaren lafiyarsu.

    Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin.

    Ta kuma shawarci masu azumi da kar su riƙa fita cikin ranar, sannan kuma su riƙa shan wadataccen ruwa a lokatan shan ruwa da sahur.

    Hukumar ta Nimet ta kuma tabbatar wa mutane cewa za ta ci gaba da bibiyar yanayi don sanar wa al’umma halin da ake ciki.

  3. Kwalara da Sanƙarau sun kashe mutum 88 a Najeriya

    Hukumar lafiya ta Duniya (WHO)ta ce kimanin mutum 922 ne aka bayyana cewa sun kamu da cutar kwalara ko amai da gudawa a Najeriya, yayin da mutum 32 suka mutu sakamon cutar a shakerar 2023 da muke ciki.

    A wani rahoton da WHO ta fitar, ta ce zuwa 5 ga watan Maris 2023 yawan mace-mace sakamakon cutar ya kai kashi 3.5 cikin 100

    WHO ɗin ta kuma ce alƙaluman sun haɗar da waɗanda suka bayyana alamun cutar, da kuma waɗanda aka tabbatar da cewa sun kamu a ɗakunan gwajin cutar da ke asibitocin ƙasar.

    Ta kuma ce alƙaluman ka iya sauyawa a kowanne lokaci sakamakon rahotonnin da ake samu a mabambantan wurare a faɗin ƙasar.

    Cutar Kwalara ko amai da gudawa, cuta ce da ake kamuwa da ita sakamakon ɗaukar ƙwayar cutar 'cholerae bacteria', mutum kan kamu da cutar idan ya ci abinci ko ya sha ruwan da ke ɗauke da ƙwayar cutar.

    Cutar dai kan zo da tsanani wanda a wasu lokutan ma take barazana ga rayuwar wanda ya kamu da ita, matuƙar bai samu kulawar gaggawa ba.

    A wani labarin na daban kuma wani rahoto da hukumar daƙile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta wallafa a shafinta na intanet, ya nuna cewa an tabbatar da samun mutum 157 da ke ɗauke da cutar sankarau tsakanin watan Oktoban bara zuwa watan Maris da muke ciki.

    Haka kuma an samu marasa lafiya da ake zargin sun kamu da cutar su kusan 628, ciki har da mutum 52 da suka mutu a jihohin ƙasar 21.

    Alamomin cutar sun haɗar da zazzaɓi da ciwon kai da tashin zuciya da amai, da sanƙarewar wuya.

  4. Koriya ta Arewa ta harba makaman linzami biyu zuwa tekun Japan

    Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami biyu zuwa tekun Japan.

    Wannan ne gwaji na baya-bayan nan cikin makwannin da suka wuce.

    Matakin na zuwa ne kwanaki bayan Koriya ta Kudu ta kammala gagarumin atisayen soji na haɗin gwiwwa da Amurka, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba cikin shekara biyar.

    To sai dai a matsayin martani ga wancan atisayen, Koriya ta Arewa ta ƙaddamar da nata gwajin sabon makamin nukiliya na ƙarƙashin teku mai ƙarfin gaske, kuma irinsa na biyu cikin wannna shakera.