Bankwana
Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.
Muhammad Buhari Fagge ke fatan asuba ta gari.
Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza
Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.
Muhammad Buhari Fagge ke fatan asuba ta gari.

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris ta isa Ghana a farkon rangadin da ta soma zuwa wasu ƙasashen Afirka uku.
Ta samu tarba daga masu kaɗe-kaɗe da raye-raye a filin jirgin saman Kotoko.
Ta bayyana ziyarar a matsayin wani ɓangare na daɗaɗɗen zumunicin da ke tsakanin Amurka da Afirka.
Fadar White House na neman tabbatar da tasirin Amurka a Afirka inda kasashe da dama suka yi maraba da hannun jari daga China.
Rasha ma tana faɗaɗa nata tasirin ta ɓangaren tsaro a ƙasashen na Afirka.

Babban jami'in rundunar yan sandan Kenya ya haramta wa yan hamayya yin zanga-zangar da suka shirya yi a gobe Litinin inda ya ce gangamin da aka yi a makon da ya gabata ya juye zuwa tashin hankali.
Babban sifetan yan sandan kasar, Japhet Koome ya fada wa yan jarida cewa zanga-zangar da aka shirya ba ta bisa doka kuma ba a lamunce a yi ta ba.
Jagoran yan hamayya Raila Odinga ya bukaci mutane su fantsama titunan kasar su yi zanga-zanga domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwar da suke fuskanta.
Shugaba William Ruto ya karbi ragamar shugabancin kasar a shekarar da ta gabata a wani zaɓe da Mista Odinga yake ikirarin an murde ma shi.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Tunisia na cewa kimanin yan ci-rani 29 ne suka nitse a ruwa bayan da kwale-kwale biyu suka yi hadari a kokarinsu na tsallaka tekun Mediteriya zuwa Italiya.
Kwanaki hudu da suka gabata ma, an samu jiragen ruwa guda biyar da suka nutse a ruwa.
Hukumomin Tunisia sun ce sun dakile wasu jirage takwas tare da tsare mutum kusan dubu uku a tsukin lokacin.
Mace-macen baya-bayan nan da aka samu a tekun Mediteriya na zuwa ne sakamakon matakin da Tunisia ke dauka kan yan ci-rani.
Jami'ai a tsibirin Lampedusa sun ce sun samu rahoton isar mutum dubu biyu da dari biyar cikin sa'a 24 da ta gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa ta sakl wata 'yar Isra'ila bayan zaman kaso da ta yi na shekara guda saboda kamata da aka yi da ta'ammali da kwayoyi.
Fidaa Kiwan ta koma Isra'ila a ranar Lahadi. Hukumomin ƙasar sun kira matakin a matsayin 'wata ahuwa ta musamman' saboda shugaba Isaac Herzog ne ya nemi a sake ta.
An kama Mis Kiwan a watan Afrilun 2021 da laifin shiga ƙasar da hodar iblis.
Tun fari an yanke mata hukuncin kisa ne, aka mayar da shi na ɗaurin rai da rai bayan ɗaukaka ƙara da ta yi.
Isra'ila da UAE sun sabunta alaƙar diflomasiyyarsu ne ƙarƙashin wata yarjejeniya da Amurka ta jagoranta a 2020.

Asalin hoton, AFP
Kungiyar tsaro ta Nato ta yi Allah-wadai d mtakin da Rasha na kafa wata tashar makamin nukilya a Belarus.
Kungiyar na bibiyar lamuran da suke faruwa sau da ƙafa, kuma matakin Rashan ba zai sa ta sauya manufofinta ba kan makaman nukiliya.
Amurka ta ce ita ba ta yarda ba, kawai Rasha na son amfani da makaman ne.
Belarus ta yi iyaka da Ukraine da kuma wasu ƙasashe da ke ƙungiyar Nato da suka haɗa da Poland da Lithuania da kuma Latvia.
Tuni Ukraine ta yi kiran wata tattaunawar gaggawa da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya kan wannan sabuwar barazana da shugaba Putin ya sanar a ranar Asabar.

Asalin hoton, Getty Images
Dakarun rundunar Haɗin Kai da haɗin gwiwar CJTF sun kashe mayaƙan ISWAP 41 a yankin ƙaramar hukumar Dikwa da ke jihar Borno.
A cewar Zagazola Makama, wanda shi ne ke kula da harkokin wallafe-wallafe a yankin tafkin Chadi, Abu Zahra wanda babban kwamanda ne a kungiyar ta ISWAP na daga cikin mutanen da suka kashe.
Zagazola ya ce babban janar na da ke lura da shiyya ta 7 Sha’aibu Waidi ne ya jagoranci samamen, wanda tamkar martani ne ga hare-haren da ISWAP suka kai Ƙauyen Mukdolo.
“Kwamandan ‘yan ta’addan (Amir Jaysh) Abu Mohammed, tare da rakiyar wasu mayaƙa an ce sun tsere saboda ba ta kashi da suka yi da soji, sun gudu sun bar kayayyakinsu na miliyoyin naira a gidan da suke zama wanda dakarunmu suka lalata,” kamar yadda suka wallafa.
Wata motar bindiga, da wasu motoci uku, da wasu kayan sojoji masu yawa.

Asalin hoton, BUHARI SALLAU
Hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriya ta ce ranar 3 ga watan Mayu za a fara ƙidayar mutane da kuma ta gidaje.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da kamfanmin dillancin labarai na Najeriya, babban daraktan hukumar Garba Abari ne ya bayyana hakan, yana cewa za a yi ƙidayar tsakanin 3 zuwa 5 ga watan na Mayu.
A watan Afrilun 2022 ne, gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta shirya ƙidaya da zarar an kammala zaɓuka.
Abari ya ce babu wanda za a bari a baya a wannan aiki, kama daga matan gida da magidanta da yara da sauran mutane.
Ya ce tun farko an samu sauyin lokacin da aka sa ne, biyo bayan ɗage zaɓen gwamnoni da aka yi a Najeriya.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ƙasarsa ba za ta ci gaba da kai hare-haren take da kai wa dakarun rasha ba, har sai ƙasashen yamma sun aike mata da ƙarin tallafin tallafin soji.
Mista Zelensky ya shaida wa wata Jaridar ƙasar Japan cewa ba zai sake tura dakarun sojin ƙasarsa fagen daga ba, ba tare da samun ƙarin tankokin yaƙi da makaman atilari da ƙarin rokoki ba.
A tattaunawar tasa da Jaridar Yomiuri Shimbun, shugaba Zelensky ya ce lamari a gabashin ƙasar na ƙara munana.
''Muna jiran ƙarin tallafin makamai daga ƙawayenmu'', in ji Zelensky.
Da aka tambaye shi yaushe yake sa ran sake tura sojojin ƙasar zuwa fagen daga sai ya ce ''ba za mu sake tura dakarunmu zuwa fagen daga ba, har sai mun samu ƙarin tallafin tankokin yaƙi da makaman atilari masu cin dogon zongo''.

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wani hamshaƙin ɗan kasuwa da hodar ibilis da kuma tabar wiwi a kan hanyarsa ta zuwa ƙasahen Vietnam da Brazil da kuma Italiya.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa shafinta na twitter ta ce ta kama ɗan kasuwar mai suna Molokwu Nwachukwu, wanda ke yawan ziyartar ƙasashen China da Dubai da Pakistan da kuma Vietnam, a filin jirgin sama na Legas.
Inda aka same shi da ƙulli 36 na hodar ibilis a cikin jakankunsa da takalmansa, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa ƙasashen kudancin asiya.
A wani labarin kuma hukumar ta ce ta kama ƙwayoyin tramadol kusan 164,750 a jihar Taraba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Nig Police
Rundunar 'yan sandan birnin tarayya da ke Abuja ta kama wani mutum mai suna Adekola Adeshina mai shakara 48, bisa zargin lalata wata ƙaramar yarinya 'yar shekara 10.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ofishin hukumar da ke yankin unguwar Apo a babban birnin tarayyar ƙasar ya samu ƙorafi daga wata mata da ke zaune a unguwar.
Inda ta yi zargin cewa makwabcinta yana yi wa 'yarta fyaɗe.
Nan take kuma rundunar ta kai samame tare da kama mutumin, inda bayan da aka tuhume shi, ya rubuta da kansa cewa ya sha yin lalata da yarinyar.
A yanzu dai yarinyar mai shekara 10 na asibiti, inda ake kula da lafiyarta.
Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayyar CP Sadiq Idris Abubakar ya yi kira da iyaye da su riƙa lura sosai a kan 'ya'yansu da mutane da ke kewaye da su, tare da ɗaukar matakan da suka dace don magance yawaitar fyade a cikin al'umma.

Asalin hoton, Nig Army
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ƙaryata rahotonni da ke zargin dakarun sojojin ƙasar da kashe ƙananan yara a yaƙin da rundunar ke yi da mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.
A watan Disamban bara ne kamfanin dillancin labarai na Reuters a wani rahoton bincike da ya fitar ya zargi sojojin Najeriyar da gudanar da wani shiri a asirce na zubar wa da aƙalla mata 10,000 ciki.
Waɗanda suka kuɓuta daga hannun mayaƙan Boko Haram a yankin arewa maso gabshin ƙasar.
Rahoton ya ce tun a shekarar 2018, sojojin Najeriyar ke gudanar da shirin a asirce na zubar wa da matan ciki ba bisa ƙa'ida ba a yankin.
Lamarin da rahoton ya ce ya sa an zubar wa da mata akallan 10,000 ciki tsakanin manyan mata da 'yan mata, waɗanda mayakon Boko Hama suka yi wa fyade bayan yin garkuwa da su.
Rahoton dai ya ja hankalin ƙasashen duniya, inda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta gudanar da gagarumin bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace don hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
To sai babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce sojojin Najeriya na ɗaya daga cikin rundunonin soji mafi inganci a faɗin duniya, wadanda ya ce suna gudanar da ayyukansu ta hanyar bin doka tare da kare 'yancin ɗan adam.
Yayin da yake magana a wajen ƙaddamar kwamitin bincike na musamman kan tauye haƙƙin ɗan adam a lokacin yaƙi da ta'addanci na yankin arewa maso gabashin ƙasar da aka yi wa laƙabi da (SIIP-North East).
Janar Yahaya ya ce ''dakarun sojin ƙasar ƙwararrun dakaru ne waɗanda ke aiki bisa turbar doka, kuma ƙarƙashin zaɓaɓɓiyar gwamnatin, inda shugaban ƙasa da sauran hukumomin tsaro duka suke nan, don martaba doka, duka mun san wannan.''
Yayin da yake ƙaryata rahoton zubar wa da matan cikin, Janar Yahaya ya zargi kamfanin dillancin labaran da rashin bayyana haƙiƙanin abin da ke faruwa na mamayar da sojojin suka yi ƙungiyar a shekarun baya-bayan nan.
Ya ƙara da cewa yankunan da rahoton ya ambato cewa an aikata wannan laifi, wurare ne da ke cikin matsanancin tsaro, waɗanda ake buƙatar rakiyar soji kafin shiga cikinsu.
Shirin namu na wannan mako - da Khalifa Shehu Dokaji ya gabatar - ya amsa tambaya kan cutar mashaƙo da hanyoyin da ake ɗaukarta, da kuma matakan kariya.
Sannan kuma shirin ya duba tarihin tsohon ma'aikacin BBC Shehu Saulawa, wanda ya rasu cikin makwannin da suka gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ce ta saka ranakun da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun gwamnoni a jihohin ƙasar da aka gudanar da zaɓen gwamna.
A wata sanarwar da hukumar INEC din ta fitar mai ɗauke da sa- hannun shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu kada ƙuri'a na hukumar Festu Okoye, ta ce sashe na 72 (1) na dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ya ɗora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun 'yan takara a cikin kwana 14 da yin zaɓen.
A kan haka ne hukumar ta ce ta saka ranar Laraba 29 ga watan Maris da kuma 31 ga watan na Maris a matsayin ranar da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓun gwamnoni da mataimakansu, tare kuma 'yan majalisun dokokin jihohi.
Sanarwar ta ce za a bayar da takardar shaidar cin zaɓen ne a harabar ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin ƙasar.
Hukumar zaɓen ta ce kwamishinonin INEC na jihohi da ma'aikatan hukumar za su sanar da zaɓaɓɓun takamammiyar ranar da za su karɓi takardun shaidar.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa za ta girke makaman nukiliya a maƙabciyarta Belarus.
Kafofin yaɗa labaran Rasha sun ruwaito Mista Putin na cewa matakin ba zai saɓa wa yarjejeniyar ƙasa-da-ƙasa ta taƙaita yaɗuwar makaman nukiliyar ba, kamar yadda Amurka ta girke nata makaman a nahiyar Turai.
Shugaba Putin ya ce Rasha ba za ta mayar da ikon sarrafa makaman zuwa Belarus ɗin ba.
To sai dai Amurka ta bayyana damuwarta game da matakin, tana mai cewa ba ta ga dalilin yin hakan ba, a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin tsaron ƙasar ta fitar.
Amurkan ta ce a shirye take wajen kare tsaron ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO.
Ƙasar Belarus dai ta haɗa iyaka da Ukraine, da kuma ƙasashen Polan da Lithuania da Latvia, waɗanda mambobin NATO ne.
Wannan shi ne karon farko tun shekarun 1990, da Rasha za ta girke makamin nukiliyarta a wata ƙasar.
Bayan wargajewar tarayyar Soviet a shekarar 1991, duka makaman da ke ƙasashen Ukraine, da Belarus da kuma Kazakhstan - waɗanda duka suka samu 'yancin gashin kai - an mayar da su zuwa Rasha a shekarar 1996.
Belarus ta kasance babbar ƙawar Rasha da ke goyon bayan mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.
A wani jawabi da ya yi wa 'yan ƙasar ta talbijin ranar Asabar shugaba Putin ya ce shugaban Belarus Alexander Lukashenko, ya daɗe yana kiran Rasha da ta girke makaman nukiliyarta a ƙasarsa.
Ahmad Abba Abdullahi tare da Salihu Adamu Usman ne suka gabatar da shirin na wannan makon

Asalin hoton, DIYA'S FAMILY
Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya a zamanin mulkin janar sani Abacha, Laftanar Janar Oladipo Oyeyinka Diya ya rasu.
Oladipo Diya wanda shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a zamanin mulkin sani Sani Abacha, a cikin watan Afrilu mai zuwa ne zai cika shekara 79 a duniya.
A wata sanarwa da ɗansa Barrister Oyesinmilola Diya, ya fitar a madadin sauran iyalansa, ya tabbatar da mutuwar tsohon babban jami'in sojin da safiyar ranar Lahadi.
An dai haifi Janar Oladipo Diya a garin Odogbolu na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, yana daga cikin dakarun da suka yi yaƙin basasar ƙaras, kafin ya zama babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar, a shekarar 1993.
Ya kuma riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar a shakerar 1994.

Asalin hoton, others
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam a Tunisiya sun ce mutum 19 ne suka mutu, waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Italiya.
Rahatani daga ƙasar sun ce kwale-kwalen maƙare da 'yan ci-rani ya nutse ne, kim kaɗan bayan tashinsa daga ƙasar.
Wannan ne karo na shida da ake samun nutsewar kwale-kwale a Tunusiya cikin kwaraki uku.
Masu gadin tekun ƙasar sun ce sun ceto kusan 'yan ci-rani 3000 da jiragensu suka yi karo ko suka nutse a tekun cikin kwanakin uku.
A ɓangare guda kums hukumomi a tsuburin Lampadusa, sun ce wurin ya cika sakamakon zuwan 'yan ci-rani dubu 250 cikin saa 24

Asalin hoton, TRUMP
Toshon shugaban Amurka Donald Trump ya ce magauta sun saka shi a gaba, a daidai lokacin da ya buɗe gangamin yaƙin sake dawowa muƙamin shugaban Amurrka
A gangamin da ya yi a jihar Texes Mista Trump ya yin iƙirarin cewa binciken ƙwaƙwaf da ake yi masa, ba wani abu ba ne face bi-ta-da-ƙullin siyasa.
Ɓacin ransa ya fi karkata kan tsohon lauyansa Michael Cohen .
Mista Trump da ya shafe tsawon makon da ya gabata yana ta magana kan binciken da ake yi masa a New York, na badaƙalar bai wa mai fina-finan baɗalar nan Stormy Daniels maƙudan daloli, inda ya kafe cewa bai san da wannan maganar ba.
Ko da yake yawancin maganganun da yake yi ba sababbi ba ne ga magoya bayansa ba, amma ya ce zai yi iya bakin ƙoƙarinsa don kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine cikin sa'a 24.
Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako, ya aka ji da azumi?
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, don kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Amma za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da makwabtan ƙasashe.
Kar ku manta kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.
mu je zuwa...