Hukumar zaben Najeriya ta ce har yanzu ba ta sanya ranar gudanar da zabukan cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka soke ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun shugaban sashen yada labaru na hukumar Festus Okoye, INEC ta ce babu gaskiya game da bayanan da ake yadawa kan cewa za a gudanar da zabukan a lokaci daya da zaben gwamnoni da na majalisar wakilan jiha da za a yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.
An dai samu wurare da dama da aka soke zabe ko kuma aka ayyana su a matsayin wadanda ba su kammala ba, bayan zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabarairu.
Cikin irin wadannan gundumomi har da daukacin zabukan majalisar dattijai daga jihar Sokoto.
Hukumar ta ce sai nan gaba ne za ta sanya ranar gudanar da wadannan zabuka bayan zaben gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi.
Sai dai ta ce akwai wasu zabuka guda biyu na majalisar dokokin tarayya wadanda ta jinkirta, wadanda a cewar sanarwar su za su gudana ne tare da na jihohi.
Na farko shi ne na mazabar majalisar dattijai ta Enugu ta gabas, wanda aka jinkirta domin bai wa jam’iyyar LP damar gudanar da zaben fitar da gwani.
Na biyu kuma shi ne zaben dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Esan Central/Esan West/Igueben da ke jihar Edo wanda aka dage saboda matsalar da aka samu da takardun kada kuri’a.
Hukumar ta ce wadannan ne kawai zabukan cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da za a yi a lokaci guda da zaben gwamnonin jiha.