Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Iran da Saudiyya sun amince su sake kulla hulɗar diflomasiya

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Taliban ta kama wani da ake zargin ya yi uwa da 'yarta fyaɗe

    Taliban ta tabbatar da kama wani da ake zargin ya yi wa wata mata da 'yarta 'yar shekara 12 a kauyen Khanqah da ke lardin Sarpul fyaɗe.

    A cewar rahotanni da bayanan da matar ta bayar, ta ce a yammacin ranar 9 ga watan Maris, lokacin da mijinta ya fita wajen aiki, wasu ’yan Taliban biyu sun shiga gidansu da sunan bincike bayan sun rufe musu hannaye, sannan suka ƙeta musu haddi.

    An ce waɗannan mutane biyu sun bar gidan lokacin da yanayi ya ragu, inda makwaɓta suka ɗauki yarinyar zuwa asibiti bayan da ta yi ta zubar da jini.

    Mako guda da bayar da rahoton faruwar lamarin, jami’in yaɗa labarai na ‘yan sandan Samangan, ya tabbatar da aikata fyaɗen, ya kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗannan mutane, amma bai bayyana waɗanda ake tuhuma ba.

  2. Shugaba Ramaphosa ya gargaɗi ma'aikatan da ke yajin aiki

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce ya damu da yajin aikin da ma'aikatan gwamnati ke ci gaba da yi wanda ke shafar muhimman ayyuka a ƙasar.

    Yajin aikin da kungiyar ma’aikatan ilimi da lafiya ta ƙasa Nehawu ta fara a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda suka ce suna bukatar a ƙara musu albashi da kashi 10 bayan da suka ki amincewa da karin kashi 3 da gwamnati ta yi.

    Mutane akalla huɗu ne suka mutu yayin da rahotanni suka ce masu zanga-zangar sun hana majinyata shiga asibitoci da dama a ƙasar, in ji ministan lafiya Joe Phahla.

    Shugaban kasar ya faɗa a ranar Alhamis cewa duk da cewa ma’aikata na da ‘yancin yin yajin aiki, ba za a amince da ayyukan tashin hankali ba.

    “Dukkanmu mun damu da irin tashin hankali da yajin aikin ya haifar. Ma'aikata a ƙasarmu suna da 'yancin yin aiki tare kuma da yajin aiki.” in ji Shugaba Ramaphosa.

  3. An kashe mutum 25 a wani hari a jihar Borno

    'Yan sanda a Najeriya sun ce akalla mutum 25 ne aka kashe a wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    An kai harin ne a garin Dikwa wanda ke kusa da garuruwan da 'yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram ke da karfi.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce tun 2009, hare-haren kungiyoyi masu tsassaurar ra'ayi ya kashe mutane sama da 350, 000 da ɗaiɗaita miliyoyi.

  4. Barkan mu da Juma'a - Hajj Babbar Rana

    Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da safiya.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da sauran sassan duniya.

    Ahmad Tijjani Bawage ne zai kasance da ku a wannan lokaci kafin daga bisani na miƙa ku ga abokiyar aikina Nabeela Mukhtar Uba.