'Yan bindiga sun kai hari tare da kashe DPO a Zamfara

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Pakistan ta haramta yaɗa jawaban tsohon firaministan ƙasar a kafofin yaɗa labarai

    Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Pakistan ta haramta wa gidajen talbijin yaɗa jawabai da hirarrakin tsohon firaministan ƙasar Imran Khan.

    Cikin wata sanarwa da PEMRA ta fitar, ta ce mista Khan ya sha yin zarge-zarge marasa tushe kan hukumomin ƙasar da kuma yaɗa kalaman ƙiyayya.

    Lamarin na faruwa ne yayin da Khan ɗin ya zargi gwamnati da kai shi Kotu kan tuhume-tuhume marasa tushe.

    Dubban magoya bayansa sun taru a kofar gidansa don daƙile yunƙurin 'yan sanda na kama shi kan zargin bayyana kyautukan da ya samu daga ƙasashen waje a lokacin da yake kan mulki.

  3. Liverpool ta casa Mancherter United 7-0

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool caskara Mancherter Uniterd da ci 7-0 a wasan mako na 26 a gasar Premier League da suka buga a filin wasa na Anfield.

    Saura minti biyu a je hutun rabin lokaci ne Cody Gakpo wanda United ta so ɗauka a lokacin cinikin 'yan wasa ya zura ƙwallo ta farko a wasan a ragar United.

    Dawowa daga hutun rabin lokacin ke da wuya sai Liverpool ta karɓi ragamar wasan inda Darwin Nunez ya fara da cin ƙwallo ta biyu da ka.

    Salah ya samu damar aika wa Gapko ƙwallo wanda shi kuma ya ɗaɗata a raga a matsayin ƙwallonsa ta biyu a wasan, kafin daga bi-sani Salah ɗin ya zura tasa daga wajen yadi na 18.

    Nunez ya zura ƙwallo ta biyar a wasan bayan da Jordan Henderson ya bugo masa ƙwallon

    Daga nan ne kuma Salah ya ci ta shida kuma ta biyu a wajensa wadda kuma ta sa ya zama ɗan wasan Liverpool da ya fi kowa zura wa ƙungiyar ƙwallo a gasar Premier inda ya ci ƙwallo 129.

    Sai kuma Firmino wanda ya shigo wasan daga baya ya zura ta bakwai a wasan.

  4. Shugaban Masar ya yi alƙawarin bai wa Tinubu Haɗin kai domin aiki tare

    El-Sisi

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah El-Sisi ya yi wa sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Tinubu alƙawarin ci gaba da ba shi goyon baya domin inganta alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

    A wata sanarwa da fadar shugaban Masar ɗin ta fitar ranar Lahadi, inda mista El-Sisi yake tsokaci kan zaɓukan ƙasar da suk gabata.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ''Shugaban ƙasar Masar, na miƙa saƙon taya murna ga al'umma da gwamnatin Najeriya bayan kammala zaɓukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki, wanda ya nuna irin ci gaban da 'yar uwarmu (Nijeriya) ta samu a fannin dimokraɗiyya''.

    El-Sisi ya ce a shirye yake ya yi aiki da sabon shugaban domin ciyar da alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu gaba, tare da al'umominsu da kuma nahiyar Afirka baki ɗaya.

    Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa ƙasashen biyu na da kyakkyawar dangantaka tun shekarar 1961 lokacin da aka samar da dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu a lokacin mulkin tsoffin shugabannin ƙasashen biyu na wancan lokaci, marigayi Gamal Abdel-Nasser, da kuma Abubakar Tafawa Balewa.

  5. Buhari ya yi kira ga shugabannin siyasa su taimaka wajen mayar da Chadi kan turbar dimokraɗiyya

    Buhari

    Asalin hoton, Nigerian Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira shugabanin ɓangarorin siyasa a Chadi da su nuna kishin ƙasa ta hanyar shiga harkokin mayar da ƙasar kan tafarkin dimokradiyya.

    Yayin da yake magana da shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Mehmet Idris Deby-Itno a wata ziyara da ya kai masa a gefe guda a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake ci gaba da gudanarwa a birnin Doha na ƙasar Qatar ranar Lahadi.

    Shugaba Buhari ya ce ''Ina ganin irin ci gaban da ake samu a ƙasarka, a matsayina na makwabci da batun ƙasarku nake kwana, kuma da shi nake tashi a zuciyata'', kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu ya fitar.

    “Na tausaya maka, ba wai dan kana matashi ba, sai dan saboda da matsayin da wasu ƙungiyoyin da ke ƙasashen waje irinsu Libya suke ɗauka, duk da cewa wannan matsala ce da ka gaje ta daga wajen mahaifinka'', in ji Buhari

    Ya kamata sauran ƙungiyoyin da ke tunanin cewa suna da ƙarfi su bayar da haɗin kai domin ceto ƙasarsu.''

    Shugaba Buhari ya gode wa shugaban mulkin sojin Chadin kan ziyarar da ya kai masa tare da tabbatar masa da cewa ''a matsayinka na makwabci a shirye nake kodayaushe wajen sauraron buƙatun shawarwarinka, kan siyasa da tsaro da sauran fannoni''.

    A nasa ɓangare shugaban mulkin sojin Chadin ya gode wa shugaba Buhari kan goyon bayan da yake ba shi tare da ƙasarsa a yayin da ƙasar ke shirin komawa tafarkin dimokradiyya, wanda ya ce shirin na tafiya kamar yadda ya kamata.

    Ya kuma yi wa Buhari fatan alkairi tare da taya shi murnar nasarar dimokraɗiyya a Najeriya, tare da cewa ''Muna fatan ci gaba da ganinka ko bayan saukarka daga mulki''.

  6. 'Yan sanda sun kashe mutum biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a Bauchi

    IGP

    Asalin hoton, NG POLICE

    Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ce jami'anta sun kashe wasu mutum biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a garin Rafin Gora da ke ƙaramar hukumar Ningi a jihar, tare da kuɓutar da wani mutum guda da ake zargi sun yi garkuwa da shi.

    A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar SP Ahmed Wakil ya fitar ranar Lahadi, ya ce mutanen ɗauke da makamai sun kai hari wani gida a garin Rafin Gora tare da yuƙurin sace wani mutum mai shekara 28.

    Sanarwar ta ce ''mutumin ya nuna turjiya ga masu garkuwar, lamarin ya janyo suka harbe shi a loƙacin da yake ƙoƙarin guduwa''.

    “Daga nan ne 'yan sanda tare da haɗin gwiwwar 'yan sa-kai suka kai ɗauki wurin da lamarin ke faruwa, inda suka yi musayar wuta da su, inda mutum biyu daga cikin maharan suka gamu da ajalinsu, tare da ƙwace bindiga ɗaya ƙirar AK47'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    SP Wakil ya ce 'yan sanda sun kuɓutar da mutumin da masu garkuwar suka yi yunƙurin sacewa, inda nan take aka garzaya da shi babban asibitin tarayya da ke Birnin Kudu domin yi masa magani.

    Ya ƙara da cewa rundunar 'yan sanda ta ƙaddamar da farautar mutanen domin su fuskanci hukunci.

  7. Amsoshin Takardunku

    Shin mece ce cutar mashaƙo? kuma ta yaya ake kamuwa da ita?

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  8. 'Yan bindiga sun kai hari tare da kashe DPO a Zamfara

    CP KOLo

    Asalin hoton, NG POLICE

    'Yan bindiga sun kai hari shalkwatar ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara da ke arewacin Najriya a daren ranar Asabar abin da ya kai ga kisan DPO da wasu jami'ai biyu.

    A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta fitar da tabbatar da kisan DOPn a lokacin harin.

    'Yan bindigar waɗanda suka shiga Maru da yawan gaske, sun riƙa harbin kan mai uwa da wabi, abin da ya janyo mutanen gari suka riƙa gudun neman ɗauki.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar CP Kolo Yusuf ya yi kira da al'ummar jihar da su kwantar da hankalinsu domin kuwa a cewarsa rundunar na ci gaba da aiki domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

    Kwamishinan ya kuma jajanta wa iyalan DPOn mai suna SP Kazeem Raheem wanda ke lura da ofishin rundunar da ke ƙaramar hukumar Maru, tare da iyalan ɗansanda ɗaya da kuma ɗan sintiri ɗaya da aka kashe lokacin harin.

    Sanarwar 'yan sandan ta ce da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar 5 ga watan Maris ne 'yan bindigar ɗauke da muggan makamai suka shiga garin domin kai wa ofishin 'yan sandan hari da nufin wargaza tsaron da garin ke da shi domin samun damar sace tare da yin garkuwa da mutanen garin.

    Daga nan ne kuma DPOn ya shirya dakaru domin tunkarar 'yan bindigar, to sai dai shi da wasu jami'ai biyu sun rasa rayukansu a ƙoƙarinsu na kare jama'ar garin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Rahotanni sun ce yanzu haka hukumomin jami'ai na cikin garin na Maru domin bibiyar abubuwan da suke faruwa.

    Daga ƙarshe kwamishinan 'yan sandan ya yi addu'ar neman gafara ga jami'an da suka rasa rayukansu tare da bai wa iyalansu haƙurin jure rashinsu.

  9. Hikayata 2022: Labarin 'Yancina

    A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alƙalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo, a yau za mu kawo muku labarin 'Yancina da Hafsata Abdul'aziz da ke unguwar Danmasaga a garin Hadejia jihar Jigawan Najeriya ta rubuta, kuma Nabila Mukhtar Uba ce kuma ta karanta:

    Bayanan sautiHikayata

    Da wannan labarin ne kuma muka kawo ƙarshen labaran Hikayata guda 15 wato na daya da na biyu da na uku da kuma 12 da alƙalan gasar suka ce sun cancanci yabo.

  10. 'Yan bindiga sun harbe wani basarake a Kano

    BBC

    An harbe dagacin ƙauyen Maigari da ke Ƙaramar Hukumar Rimin da ke Jihar Kano.

    Ɗansa, wanda shi ne shugaban Ƙaramar hukumar Barista Munira Dahiru Maigari ne ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamari.

    Barista Munir ya ce, "lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na dare. Suka zo suka yi abin da suka yi. yanzu muna shirin binne shi ne.

    "Ba za mu iya cewa komai ba game da dalilin faruwar lamarin, amma dai maganar shi ne ya mutu, kuma muna roƙar masa rahamar ubangiji."

    Ya ƙara da cewa sai da 'yan bindigar suka shiga gidan masaraucin suka ci mutuncinsa gabanin su kashe shi.

  11. Argentina ta gayyaci Messi wasa biyu na sada zumunta

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Lionel Messi na shirin buga wa tawagar Argentina tamaula a karon farko tun bayan lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

    Argentina ta samu daukar kofin duniya na uku jimilla, bayan da ta yi nasara a kan Faransa a bugun fenariti a wasan karshe.

    Koci, Lionel Scaloni ya gayyaci 'yan wasa 35, domin buga wa Argentina wasan sada zumunta, cikinsu har da dukkan 26 da suka buga kofin duniya a Qatar.

    An gayyaci Giovanni Lo Celso, wanda rauni ya hana shi zuwa Qatar da dan wasan Manchester United Alejandro Garnacho, wanda karon farko aka bashi goron gayyata.

    An kuma kira wasu 'yan kwallon a karon farko da ya hada da dan wasan Manchester City, Maximo Perrone da Facundo Buonanotte na Brighton da dan kwallon Inter Milan, Valentin Carboni.

    Argentina za ta karbi bakuncin Panama ranar 23 ga watan Maris Buenos Aires asannan ta kece raini da Curacao a Santiago del Estero kwana biyar tsakani.

    An yi ta rade-radin cewar Messi zai yi ritaya, bayan da dan wasan mai shekara 35 ya ja ragamar tawagar ta lashe kofin duniya a Qatar.

  12. Real Madrid za ta fafata da Real Betis

    REAL MADRID FC

    Asalin hoton, REAL MADRID FC

    Real Betis da Real Madrid za su buga wasan mako na 24 ranar Lahadi a gasar La Liga a filin wasa na Benito Villamarin.

    Ranar 3 ga watan Satumba Real ta ci Betis 2-1 a filin wasa na Santiago Bernabeu, kuma Vinicius da Rodrygo ne suka ci mata kwallaye.

    Yayin da Betis ta zare daya ta hannun Sergio Canales.

    Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona ta daya mai maki 59.

    Ita kuwa Betis mai maki 40 tana ta biyar a teburi da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid.

    Bayan da Real ta bayyana 'yan kwallon da za su kara da Betis daga baya ta bayar da sanarwar cewar Álvaro Odriozola ba zai buga fafatawar ba, wanda zai yi jinya.

    Tuni Carlos Ancelotti ya sanar da 'yan wasan Real da ya je da su Betis don buga karawar:

  13. A shirye muke da masu sa ido na MDD - Iran

    BBC

    Iran ta ce ta shirya tsaf domin bai wa masu sa ido na Majalisar Ɗinkin Duniya damar kai wa ga cibiyoyinta na nukiliya.

    Shugaban hukumar da ke sa ido kan makamin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ya shaida wa manema labarai cewa mahukuntan Iran sun amince da sanya kyamarori a cibiyoyin.

    Rafael Grossi,ya yi wata tattaunawa a Tehran, bayan da aka gano makamin Uranium a wata cibiyar nukiliya da ke Iran din.

    Iran dai ta ce shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.

    Wasu jami'an diplomasiyya sun yi gargaɗin cewa a baya Iran ta gaza cika alƙawarin da ta yi makamancin wannan na kyale masu sa ido su je cibiyoyinta na nukiliya.

  14. 'Kada Tinubu ya yi jinkirin naɗa ministoci kamar yadda Buhari ya yi'

    P

    Asalin hoton, Presidency

    Bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya , wanda Bola Ahmed Tinubu na jam'iyar APC ya yi nasarar zama shugaban kasar, yanzu kuma hankali ya koma kan irin ƙalubalen da ke gaban sabon zaɓaɓɓen shugaban mai jiran gado.

    Masana sun fara bayyana wasu jerin ƙalubala da ke kan gaban Tinubu, tare da kira gare shi da kada ya kalli ɓangaranci wajen yi wa Najeriya aiki.

    BBC ta tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir, wani massanin kimiyar siyasa da ke jami'ar jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, wanda ya ce akwai buƙatar Tinubu ya fara aiki cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

    "Ya kalli abubuwan da suka faru a 2015, kada ya sake ya maimaita abubuwan da Buhari ya yi a baya, kamar jinkiri wajen naɗa ministoci da shugabannin hukumomin gwanati.

    "Kada ya kalli ɓangaranci a shugabancinsa domin kuwa Najeriya zai shugabanta ba wani ɓangare ba," in Farfesa Tukur.

  15. 'Mun cire sama da mutum miliyan 100 daga talauci'

    MOH

    Asalin hoton, MOH

    Gwamnatin Tarayya ta ce ta kashe naira biliyan 35.5 kan shirye-shiryen taimakawa al'umma a Jihar Taraba tun lokacin da ta ci mulki.

    Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala'i ta Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana haka a Jalingo babban birnin jihar, yayin da take wata tattaunawa da waɗanda suka ci moriyar shirye-shiryen.

    Ministar wadda shugabar shirin a jihar Beatrice Kitchina ta wakilta ta ce mutum sama da miliyan 100 sun fita daga cikin matsanancin talauci dalilin wannan shiri, kuma ciki har da matasa da mata.

    Ta bayyana jerin wasu shirye-shirye kamar su N-Power da CCT da GEEP ga kuma shirin ciyar da 'yan makaranta shi ma.

    Sakataren shirin ciyar da 'yan makarantar Idris Goje, yace an yi maganin talauci a ƙasa da wannan shiri, haka kuma ya yi amfani a jihar Taraba.

  16. An sace ma'aikatan Red Cross a Mali

    BBC

    An sace ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Cross a Mali.

    Kungiyar ta ce an sace ma'aikatan ne a tsakanin hanyar birnin Gao da Kidal da ke arewacin kasar, wanda yanki ne da ke fama da rikicin masu kishin addinin islama.

    Tun shekarar 2012 Mali ke fama da matsalar tsaro, sannan kuma sace sacen mutane don neman kudin fansa da kuma mayarwar gwamnati martani a kan wani, ya zamo ruwan dare a kasar.

    Rikicin kasar dai ya fantsama zuwa makwabtanta kamar Burkina Faso da kuma Nijar, inda aka kashe dubban mutane da kuma raba wasu da dama da muhallansu.

  17. Dokar hana 'yan cirani shiga Birtaniya ta tayar da ƙura

    BBC

    Firaiministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya ce ya kuduri aniyar tabbatar da cewa babu wani mutum da zai shiga Birtaniya ba bisa ka'ida a kyale shi ya zauna.

    Da ya ke rubutu a cikin wata jaridar kasar mai suna The Mail on Sunday, Mr Sunak ya bayyana kokarinsa na dakatar da tsallakawar da 'yan ci rani ke yi ta ruwa a cikin kananan jiragen ruwa.

    Ana kyautata tsammanin gwamnatin zata sanar da wata doka nan da wasu makwanni masu zuwa wadda zata rinka mayar da wadanda suka shiga kasar ta ruwa zuwa Rwanda ko kuma wata kasar.

    Wasu kungiyoyi sun bayyana damuwa akan cewa ko wadannan dokoki sun ci karo da tsarin dokokin kare hakkin dan adam.

  18. Dubban mutane sun ƙara fitowa zanga-zanga a Isra'ila

    BBC

    Mutane dubu biyu ne suka bi sahunzanga-zangar da ake a sassan Israila, wadda zanga-zanga ce mafi girma da ake ta nuna kin amincewa da shirin gwamnati na yi wa bangaren shari'ar kasar garanbawul.

    Yawanci zanga-zangar ta lumana ce, to amma wasu bidiyo da aka dauka sun nuna yadda wasu masu zanga zangar a Tel Aviv, ke karya shingayen da 'yan sanda suka sanya don toshe tituna sannan suna kunna wuta da kuma toshe manyan hanyoyi.

    Masu zanga-zangar sun yi ta ihu a wajen,'Yan sanda dai sun yi amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

    An samu 'yar hatsaniya a Birnin Kudus.

    Yawanci 'yan adawa sun yi magana a wajen zanga-zangar inda suka bayyana damuwarsu a kan sauye sauyen da gwamnatin ke shirin yi a bangaren shari'ar kasar.

    Sauye sauyen sun hadar da ba wa ministoci damar zabar alkalan kotun kolin kasar da kuma ragewa kotun karfi.

  19. Barka da safiya

    Masu bibiyar mu da fatan an tashi lafiya Buhari Fagge ne ke fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da suke faruwa a duniya har da nahiyoyinku.