Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad and Abdullahi Bello Diginza

  1. INEC ta sauya shawara ta ajiye muhimman kayan zaben Najeriya a CBN

    Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce za ta adana muhimman kayan zaben 2023 a Babban Bankin kasar, bayan da a baya ta ce ba za ta yi hakan ba.

    Idan dai ba a manta ba a 2022 sakamakon damuwa da jama'a da kungiyoyi suka nuna da kuma matsin lamba da aka yi wa hukumar ta INEC, kan adana kayan a CBN, bayan da Gwamnan bankin Godwin Emefiele ya nuna sha'awarsa ta yin takarar shiugabancin kasar, hukumar ta nuna cewa ba za ta ajiye kayan a can ba.

    Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar 4 ga watan Yuni 2022, ya ce a lokacin ba za a kai muhimman kayan zaben CBN ba.

    A jiya Talata ne Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar ta INEC Festus Okoye ya bayyana cewa wasu daga cikin muhimman kayan zaben suna Babban Bankin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Okoye ya ce yuni hukumar ta samar tare da kai muhimman kayan zaben kamar su takardar rubuta sakamako da takardar zabe kuma ta adana su a bankin inda daga can za ta kai su ofisoshin INEC da ke kananan hukumomin kasar.

  2. Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba ta Bawa ranar samu in ji Bahaushe. Muhammad Annur Muhammad ne zai kasance da ku, daga yanzu zuwa wani lokaci, a wannan shafi da ke kawo muku labarai kai tsaye na Najeriya da sauran sassan duniya.

    Mu fara wannan karin maganar, ''Matar Na-tuba ba ta rasa miji''

    Ga wani hoton gashin tsire nan ko ya sa muku sha'awarsa idan an jima

  3. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  4. Saudiyya za ta karɓi baƙuncin gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi

    An zaɓi ƙasar Saudiyya a matsayin ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi a karon farko.

    An bayyana matakin ne kwana uku bayan da Real Madrid ta ɗauki kofin a Morocco, bayan da ta casa Al- Hilal da ci 5-3, ƙungiyar Saudiyya ta farko da ta kai wasan ƙarshe a gasar.

    Saudiyya da za ta kasance ƙasa ta shida da ta ɗauki baƙuncin gasar tun bayan ɓullo da ita a shekarar 2000.

    Ministan wasanni na ƙasar ya ce ɗaukar nauyin gasar alama ce da ke nuna cewa ''karanmu ya kai tsaiko''.

    A 'yan shekarun baya-bayan nan dai ƙasar Saudiyya na ta zuba jari a ɓangaren wasanni, lamarin da ya sa wasu ke zarginta da zubar da martabar ƙasar.

    Haka kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam ciki har da Amnesty International na zargin ƙasar da take haƙƙin bil adama.

  5. Cutar Marburg: WHO zata aike da tawagar litoci zuwa Equatorial Guinea

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce za ta aike da tawagar ƙwararrun liktoci zuwa gabashin Equatorial Guinea domin taimakawa wajen daƙile cutar Marburg da ke kisan mutane a ƙasar.

    Fiye da mutum 4,000 ne suka aka killace a lardin Ntem bayan da aka samu mutuwar mutum tara tare da samun ƙarin mutum 16 da suka kamu.

    WHO na gudanar da taron gaggawa kan cutar Marburg a Geneva.

    Cutar wadda ke cikin dangin cutar Ebola, har yanzu ba a kai ga samar da riga-kafinta ba.

  6. Buhari ya rantsar da kwamitin miƙa mulki

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamitin miƙa mulki, wadda za ta gudanar da shirye-shiryen miƙa mulki zuwa wata sabuwar gwamnatin da za a zaɓa cikin wannan wata.

    Shugaban wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce dole a adana ci gaban da gwamnatinsa ta samar.

    A makon da ya gabata ne shugaban shugaban ƙasar ya amince da kafa kwamitin tare da sanya hannu kan dokar ta ta samar da kwamitin, domin halasta ayyukansa.

    Yayin da yake rantsar da mambobin kwamitin Boss Mustapha ya ce wannan wani abu ne na tarihi da gwamnatinsu ta samar wajen nuna yadda ta damu wajen bunƙasa harkokin dimokradiyya a ƙasar.

    A ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki ne dai 'yan ƙasar za su zaɓi sabon shugaban ƙasar na gaba, da zai gaji kujerar shugaba Buhari.

    Inda kuma za a miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin ranar 29 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.

  7. An umarci sanatoci biyu mata su fice daga majalisa kan 'tufafin da suka saka'

    Majalisar dattawan Kenya ta umarci sanatoci mata guda biyu da su fice daga zauren majalisar, saboda tufafin da suka sanya a lokacin da suka halarci zaman majalisar.

    Ɗaya daga cikinsu ta saka riga marar hannu, ɗayar kuma saboda ganin ɗigon jini a wandonta kasancewar tana al'ada.

    Sanata Gloria Orwoba ta shaida wa shugaban majalisar cewa lamarin jinin al'ada abu ne da ke aukuwa ga mata ba tare da sun shirya masa ba.

    To amma an umarce ta da ficewa daga majalisar kasancewar ba a amince da ganin ɗingon jini a tufafi ba, dan haka dole ta sauya tufafi.

    An kuma umarci takwararta Sanata Karen Nyamu da ta fice daga zauren majalisar sakamakon sanya riga marar hannu.

    Sanatocin ɓangaren adawa sun yi ƙorafin cewa Ms Nyamu ta sanya tufafin da zai kawo rashin kunya a majalisar.

    Shugaban Majalisar ya ce hakan saɓa wa dokar sanya tufafi ce ta majalisar, wadda ta tanadi cewa dole mata su sanya tufafin da za su kare mutuncinsu.

  8. EFCC ta kama wani mutum da ke iƙirarin shugabancin hukumar

    Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati a Najeriya EFCC ta kama wani mutum da ke iƙirarin shugabancin hukumar.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta Facebook, ta ce ta kama mutumin mai suna Salman Umar Hudu ne ranar Talata a wani otal da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    Sanarwar ta ce salman mai shekara 38 - wanda ɗan asalin jihar Kano ne da ke arewacin ƙasar – na ƙaryar gabatar da kansa a matsayin shugaban hukumar ta EFC Abdulrasheed Bawa, da kuma sauran jami’an hukumar.

    Haka kuma hukumar ta ce salman ya karɓi kusan naira 100,000 daga wani mutum da ya yaudara da cewa zai ji da kowacce irin matsala a EFCC.

    Hukumar ta kara da cewa mutumin ya bayar da cikakkun bayanai da za su taimaka wa hukumar, kuma EFCCn ta ce za ta gabatar da shi a gaban Kotu da zarar ta kammala bincike.

  9. An yi kira ga Zimbabwe ta yi watsi da dokar taƙaita ayyukan ƙungiyoyin fararen hula

    Manyan jami’an kare haƙƙin ɗan adam na Majalisar Dinkin Duniya sun umarci shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da kada ya sanya hannu kan sabuwar dokar da za ta taƙaita ayyukan ƙungiyoyin fararen hula a ƙasar.

    Dokar da majalisar dokokin ƙasar ta amince da ita a mako biyu da suka gabata ta haramta wa ƙungiyoyin agaji shiga harkokin siyasar ƙasar da kuma bai wa gwamnatin ƙasar damar lura da harkokin gudanarwa da kashe kuɗaɗen ƙungiyoyin.

    Gwamnatin ta ce hakan zai taimaka wajen hana halasta kuɗin haram da ƙaruwar ayyukan ta’addanci a ƙasar.

    To sai dai masana na cewa taƙaitawar za ta yi wa ayyukan ƙungiyoyin tarnaƙi musamman ga mutane masu ƙaramin ƙarfi.

    Kungiyoyin kare hakkin bil adama a ƙasar da ‘yan adawa na cewa gwamnatin ƙasar na ɗaukar matakin ne domin yin zagon ƙasa ga babban zaɓen ƙasar da ke tafe nan gaba cikin shekara.

  10. An yanke wa 'yan fashi biyu hukuncin kisa a Najeriya

    Bababr kotun Jihar Ondo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta yanke wa wasu 'yan fashi biyu hukuncin kisa bisa samunsu da laifin kashe wasu ma'aurata a jihar.

    Ana zargin mutanen biyu da kisan Mista Kwaku Richard Kwakye da matarsa Tope Kwakye a shekarar 2019 a Akure babban birnin jihar Ondo.

    Alƙalin kotun ya ce an kuma samu mutanen biyu da laifin haɗa baki wajen aikata laifin, wanda wannan ya sa aka yanke musu hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari.

    Sannan kotun ta same su da laifin kisan kai da laifin fashi da makami, a dan haka alƙalin kotun Williams Olamideya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

    Lauyan gwamnatin jihar John Dada ya ce suna zargin mutanen biyu da laifuka biyar, ciki har da kisan ma'auratan ranar 1 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 8:30 a birnin Akure.

    Dada ya faɗa wa kotun cewa mutanen da ake zargin waɗanda ke ɗauke da muggan makamai sun kashe ma'auratan.

  11. WHO za ta yi taron gaggawa kan ɓullar cutar marburg a Equatorial Guinea

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce za ta gudanar da taron gaggawa akan bullar kwayar cutar Marburg a kasar Equatorial Guinea.

    Mutum tara ne suka rasa rayukansu sanadin cutar da ke sa matsanancin zazzabi tare da zubar jini daga sassan jikin marasa lafiya.

    An kuma samu karin wasu mutum 16 da ake zargin sun kamu da kwayar cutar ta Maburg a lardin Kie Ntem da ke gabashi wanda a baya ba a taba samun wani da ya kamu da cutar ba.

    An danganta mace-macen akan jana'izar da aka yi a baya inda hudu daga cikin wadanda suka mutun 'yan gida daya ne.

  12. Ranar Masoya: Najeriya ce ta ɗaya a duniya a yawan masu bincike kan soyayya

    Shafin matambayi-ba-ya-ɓata na intanet mafi girma a duniya Google ya bayyana cewa Najeriya ce ta ɗaya a duk duniya a yawan mutanen da ke ziyartar shafin domin samun bayanai game da ranar Masoya ta Duniya

    Jami'in hulɗa da jama'a da sadarwa na shafin mai kula da Afirka ta yamma Taiwo Kola Ogunlade ne ya bayyana haka.

    Ya ƙara da cewa bayanan da suka samu sun nuna irin jerin tambayoyi da masu amfani da shafin suka yi dangane da bikin 'Ranar masoya ta Duniya', kuma Najeriya ce ta kasance ta ɗaya a duniya a wannan shekarar ta 2023 da kashi 200 cikin 100.

    Haka kuma rahoton ya nuna cewa a yanzu Najeriya ce ta farko da 'yan ƙasarta ke neman bayanai game da soyayya a 2023, kuma tun 2004 ita ce ƙasar da ta fi kowacce bincike game da manhajojin da suka jiɓanci soyayya a duniya da saƙonnin Ranar Masoya da saƙonnin soyayya.

    “A shafinmu na Google, manufarmu ita ce samar da bayanan da mutane ke nema a lokacin da suke buƙatarsu,'' in ji ” Taiwo a cikin wata sanrwa da ya fitar.

  13. Babban Bankin Najeriya ya yi gargaɗi kan sayar da Naira da liƙi a biki

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jaddada gargaɗinsa ga jama'a a kan yin liƙi da takardar kuɗin ƙasar ta Naira a lokacin biki.

    A sanarwar da hukumar bankin ta fitar ta Twitter ta ce, saɓa wa dokar bankin ta 2007 laifi ne da zai sa a ci tarar mutum naira dubu 50 ko kuma ɗaurin gidan yari da bai wuce wata shida ba ko kuma duka biyu.

    Wasu 'yan Najeriya suna da al'adar yin abubuwa kamar su kek da takardar kuɗin ƙasar ta Naira domin aika wa 'yan uwa da masoya a lokacin bikin ranar haihuwa ko kuma wani biki na aure da makamantansu.

    Haka kuma sukan yi liƙi da takardar ta Naira a lokacin bukukuwa.

    Laifukan da bankin ya zayyana da ake yi da takardar kuɗin sun haɗa da, liƙi da sayarwa da cukuikuyewa da rubutu ko zane ko tattaka su ko rawa a kansu da sauransu.

    Babban Bankin na Najeriya ya fitar da wannan gargaɗi ne a daidai lokacin da takardar kuɗin ke ƙaranci sakamakon canjin takardar naira ta 200 da 500 da kuma 1,000 da bankin ya yi.

  14. An kai samame a ofisoshin BBC da ke Indiya

    Jami'an haraji a Indiya sun kai samame a ofishohin BBC da ke Delhi da Mumbai inda suka ce sun zo domin tantance takardu harajin ma'aikata.

    Sun hana ma’aikata fita daga wurin aikinsu kuma rahotani sun ce sun kwace wayoyi.

    BBC ta ce tana bayar da cikakken hadin kai ga mahukuntan kasar.

    Samamen na zuwa makonni kadan bayan da BBC ta yadda wani shiri a kan rawar da firaministan Indiya Narendra Modi ya taka a tashin hankali mai nasaba da addini da ya faru shekaru ashirin da suka gabata.

    Sai dai Sakatare Janar na jam'iyyar hammaya ta Congress ya ce mahukunatan Indiya sun rasa na yi ne shi ya sa suka kai samamen.

    A dayan bangaren kakakin jam'iyyar BJP mai mulki ya bayyana BBC a matsayin kungiyar da ta fi aikata rashawa a duniya.

  15. Shugaba Buhari ya nemi Hadaddiyar Daular Larabawa ta dage dokar hana bai wa 'yan Najeria biza

    Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki a dambarwar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta kai ga ƙasar ta Gabas ta Tsakiya ta dakatar da bai wa 'yan Najeriya takardar izinin shiga cikinta, wato biza.

    A watan Oktoba na shekarar da ta wuce ne 2022 hukumomin Daular suka dauki matakin dakatar da bai wa 'yan Najeriya bizar, sai wadanda suke da fasfo na manya wato na diflomasiyya kawai.

    Duk da cewa hukumomin ƙasar ta Larabawa ba su bayyana dalilinsu na ɗaukar matakin ba, wasu na danganta shi ga rashin ɗa'a da bin doka da oda da wasu 'yan Najeriyar da ke zaune ko aiki a can suke yi.

    A wata tattaunawa ta waya da Shugaba Buhari ya yi ranar Litinin da takwaransa na Daular, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda kuma shi ne Sarkin Abu Dhabi ya yi maganar neman ɗage dakatarwar.

    Tattaunawar da Shugaba Buharin ya yi da Sheikh Al Nathan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban na Najeriya Mallam Garba Shehu, ya fitar yau Talata.

  16. Matawalle ya kori kungiyoyi masu zaman kansu a Zamfara

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta umarci dukkanin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar su tattara i-nasu-i-nasu su fice daga jihar ba tare da bata wani lokaci ba.

    Umarnin na cikin wata sanarwa ne da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Mamman Tsafe ya fitar.

    Sanarwar ta zargi kungiyoyin wadanda ba na gwamnati ba da gudanar da ayyukan da ke iya kara matsalar tsaro a jihar da makwabta.

    Gwamnatin ta ce ta lura da yadda kungiyoyin suke ta karuwa a jihar inda suke gudanar da ayyukan da suka saba wa doka.

    Kuma ta ce ta lura yawancin kungiyoyin ba su yi rijista a jihar ba kamar yadda doka ta tanada.

    Sanarwar ta umarci ma'aikatu da sassa da kuma hukumomin gwamnati da su daina duk wata mu'amulla da kowa ce kungiya, tare da gargadin cewa za a hukunta duk wata hukumar gwamnati da ta yi mua'mulla da kungiyoyin.

    Gwamnatin ta kuma bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su sanya ido domin gano duk wata kungiya da ke aiki ba tare da takardar izini daga hukumar da ta dace ba, domin gurfanar da ita a gaban kotu.

  17. Katafaren jirgin ruwan yaki na Rasha ya isa Afirka ta Kudu a shirin atisayen hadin guiwa

    Wani katafaren jirgin ruwan yaki na Rasha ya isa tashar jirgin ruwan Cape Town, da ke Afirka ta Kudu a shirye-shiryen atisayen hadin guiwa da China da kuma Afirka ta Kudu.

    Ofishin jakadancin Rasha da ke Cape Town ya sanya hoton jirgin mai suna Admiral Gorshkov a shafinsa na Twitter, inda yake nuna jirgin a tashar ruwan.

    Za su ye atisayen tsawon kawana goma daga ranar 17 ga watannan na Fabarairu zuwa 27 ga watan na Fabrairu a tashar ruwa ta Durban da kuma ta Richards Bay.

    Wasu na suka a kan shirin atisayen da cewa bai dace ba ganin cewa ya zo daidai da cika shekara daya da mamayen da Rasha ta yi wa Ukraine.

    To amma ma'aikatar tsaro ta Afirka ta Kudu ta kare matakin da cewa a baya Afirka ta Kudun ta yi irin wannan atisaye na hadin guiwa da Faransa da Amurka da kuma wasu kasashen na kungiyar tsaro ta Nato.

  18. Mutum 20 sun mutu a hadarin manyan motoci a Afirka ta Kudu

    Mutum ashirin sun rasa ransu wasu 61 kuma suka samu raunuka sakamakon wani hadarin manyan motoci biyu, bas da wata mai sulke a lardin Limpopo na Afirka ta Kudu.

    Motar safa din ta fadi daga gada ta tsunduma cikin ruwa a lokacin da hadarin ya auku a jiya Litinin, kamar yadda rahotanni suka ce.

    Yawancin wadanda suka mutu sun rasu ne a cikin bas din da ta fada ruwa, saboda ba ta yadda za su iya fita.

    Ana gudanar da bincike kan abin da ya haddasa hadarin.

    To amma rahotanni sun ce a lokacin ana ruwan sama sosai a yankin.

    Har zuwa safiyar yau Talata ma'aikatan agaji suna wurin, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ke haifar musu cikas ga aikin nasu.

  19. Hukumar lafiya ta duniya za ta yi taron gaggawa kan cutar Marburg da ta barke a kusa da Afirka ta Yamma

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce za ta yi taron gaggawa a kan barkewar cutar Marburg a Jamhuriyar Equatorial Guinea da ke yankin tsakiyar Afirka.

    Alkaluman hukuma sun nuna cewa zuwa yanzu cutar ta hallaka mutum tara, kuma akwai wasu mutum 16 da ake fargabar sun kamu da zazzabin a lardin Kie Ntem na gabashin kasar, inda a baya ba a samu bullar cutar ba.

    Bincike ya nuna an samu mutuwar ne sakamakon wata jana'iza da mutanen hudu 'yan gida daya suka halarta ta wanda cutar ta yi sanadin mutuwarsa.

    An yi amanna cutar na yaduwa ne zuwa mutane daga jimage da ke cin 'ya'yan itace, da kuma irin yadda Ebola ke yaduwa tsakanin mutane ta hanyar ruwa ko yawu ko majina ko jinin jikinsu.

    Ya zuwa yanzu cutar ta Marburg mai haddasa tsananin zazzabin ba ta da magani ko riga-kafi.

  20. Tanzania ta haramta amfani da wani littafin yara a makarantu saboda zargin kare 'yancin 'yan luwadi

    Gwamnatin Tanzania ta haramta amfani da sanannen littafin yaran nan mai suna Diary of Wimpy Kid wajen koyarwa a makarantun kasar saboda zargin kare 'yancin masu neman jinsi daya.

    Littafin yana da mujalladi da dama, kuma daga cikinsu yanzu gwamnatin ta haramta guda 16.

    Ministan ilimi na kasar Farfesa Adolf Mkenda ya ce littafin yana jefa ilimin yara cikin hadari kuma ya saba da al'adun Tanzania.

    Makenda ya bukaci iyaye da su rika duba jakar makaranta ta 'ya'aynsu akai-akai domin su tabbatar ba sa dauke da wadannan littattafai.

    Duk wata makaranta da ta ci gaba da amfani da jerin littattafan za ta fuskanci hukunci na ladabtarwa da kuma kotu, ciki har da soke rijistarta.

    Wadanda aka haramta sun hada da;

    • Diary of a Wimpy Kid: Rodrick Rules
    • Diary of a Wimpy Kid: The Last Straw,
    • Diary of a Wimpy Kid: The Ugly Truth
    • Diary of a Wimpy Kid: Cabin Fever.
    • Diary of a Wimpy Kid: The Third Wheel
    • Diary of a Wimpy Kid: Hard Luck
    • Diary of a Wimpy Kid: The Long Haul
    • Diary of a Wimpy Kid: Old School
    • Diary of a Wimpy Kid: Double Down
    • Diary of a Wimpy Kid: The Gateway.