Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Kotun Amurka ta yanke wa wani farar fata hukuncin ɗaurin rai-da-rai

    Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani matashi farar fata hukuncin ɗaurin rai da rai ,ba tare da afuwa ba game da kisan baƙar fata 10 a wani babban kanti a Buffalo da ke jihar New York a watan Mayun bara.

    Alƙalin kotun mai sharia Susan Eagan ta ce an yanke masa hukuncin da ake yanke wa manya duk da cewa shi matashi ne

    Ta ce idan aka dubi yadda aka shirya bincike tare da aiwatar da wannan aika aikar ta nuna ƙiyayya, idan aka yanke ma ka hukunci a matsayin matashi toh wannan tamakar rashin adalci ne

    Sai dai 'yan uwan mutanen da ya kashe, da suka fusata sun far wa matashin mai suna Payton Gendon inda ɗaya daga cikinsu ya yi ƙoƙarin kai masa naushi.

    Masu bincike sun gano cewa ya yi bincike ta intanet a kan adadin bakar fatar da ke zaune a unguwar da ya kai harin

  3. MDD ta nuna damuwa kan ƙaruwar 'yan ci-rani da ke tsallaka tekun Djibouti zuwa Yemen

    Shugaban hukumar kula da masu ƙaura ta Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa a kan ƙaruwar da aka samu a yawan 'yan ci-rani da ke ƙoƙarin tsallaka teku mai hatsarin gaske daga Djibouti zuwa Yemen.

    Shugaban hukumar ta IOM, Antonio Vitorino ya ce mutum 150,000 ne suka tsallaka tekun a bara.

    A cikin makon da ya gabata an kwaso ɗaruruwan baƙin haure a cikin wasu kwale kwalen da suka cika makil da mutane a gabar tekun Aden.

    'Yan ci-ranin na fatan zuwa Saudiyya ko sauran ƙasashen Larabawa masu arzikin mai, sai dai da dama daga cikinsu kan maƙale a Yemen.

    Hukumar ta IOM ta ce rayuwa cikin ƙunci da tashin hankali da sauyin yanayi na cikin abubuwan da suka sa yan ci-ranin na barin ƙasashensu

  4. 'Yan gudun hijirar Syria za su koma gida daga Turkiyya

    Dubban yan gudun hijirar Syria da suka tsere zuwa Turkiyya sun taru a kan iyakokin ƙasar domin su koma gida Syria bayan girgizar ƙasar da ta faru a makon daya gabata.

    Wannan ya biyo bayan rahotanni da ke cewa gwamnatin Turkiyyar za ta yi wa dokokin shige da fice sassauci.

    Gwamnatin Turkiyya ta ce yan Syria za su iya komawa Turkiyyar bayan watanni biyu sai dai da dama daga cikinsu sun ce sun rasa komai a dan haka da wuya su koma

    'Yan Syria fiye da miliyan huɗu ne ke zaune a Turkiyyar kuma wannan ne ya sa gwamnatin ƙasar ta tsaurara matakan tsaro akan iyakokinta a shekarun baya baya nan.

    Mutum fiye da 41,000 ne suka rasa rayukansu a ƙasashen biyu sanadin girgizar ƙasar

    Haɗɗaɗiyar daular Larabawa ta yi alƙawatin samar wa Syria da ƙarin tallafin dala miliyan hamsin

  5. Za mu gurfanar da wanda ya ƙi karɓar tsoffin kuɗi a gaban kotu - Gwaman Legas

    Gwaman jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya Babajide Sanwo-Olu ya gargaɗi duk waɗanda ke ƙin karbar tsofaffin takardun kuɗi a jihar da su daina yin hakan ko su fuskanci fushin shari'a.

    Ya ce ƙin karɓar tsoffin takardun kuɗin ya saɓa wa matakin kotun ƙolin ƙasar .

    Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da tsare-tsaren kuɗi na jihar ya fitar ranar Laraba.

    Gargaɗin na gwamnan na zuwa ne bayan kotun ƙolin ƙasar ta ɗage - sauraron ƙarar da wasu jihohin ƙasar suka shigar gabanta suna ƙalubalantar wa'adin Babban Bankin - zuwa 22 ga watan Fabrairu.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ''a lokacin da zaman kotun na farko ranar 8 ga watan Fabrairu , kotun ta ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci game da lamarin''.

    “Matakin yana nan bai sauya ba. Dan haka gwamnatin jiha ke gargaɗin mutanen da ke ƙin karɓar tofaffin kuɗin da su daina hakan, in ba haka ba kuma su fuskanci fushin shari'a''

    ''Saɓa doka ne ƙin karɓar tsofaffin kuɗin takardun kuɗi, kuma yin hakan ya saɓa wa matsayin umarnin kotu.''

  6. JAMB ta ƙara wa'adin rajista saboda ƙarancin kuɗi

    Hukumar da ke Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire a Najeriya (JAMB) ta ƙara wa'adin rajistar jarrabawar wannan shekara zuwa mako ɗaya.

    Hukumar ta ce ta ƙara wa'adin ne saboda wahalhalun da ɗalibai ke fuskanta wajen samun kuɗin rajistar, da kuma matsalolin amfanin da tsarin banki ta internet wajen sayen lambobin rajistar a yanar gizo.

    JAMB ɗin ta ce za a ci gaba da sayar da lambobin rajistar har zuwa ranar Litinin, yayin da rajistar za ta ci gaba har zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairun da muke ciki.

    Tun da farko dai hukumar ta JAMB ta sanya ranar 14 ga watan na Fabrairun a matsayin ranar da za ta rufe yin rajistar.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ya fitar ya ce zuwa ranar Talata hukumar ta samu mutum 1,527,068 da suka yi rajistar jarrabawar, ciki har da ɗalibai 168,748 da suka nuna sha'awarsu ta yin jarrabawar gwaji ta Mock-UTME.

    Ya ƙara da cewa hukumar ta faɗaɗa ƙarfinta, ta yadda take yi wa mutum 100,000 rajista a kowacce rana.

    “Da wannan, za mu iya yi wa duka mutanen da suke da sha'awar rubuta jarrabwar ta bana rajista a cikin mako gudan da muka ƙara'', in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa ''Saboda ƙasa da mutum 50,000 ne ke buƙatar rajistar a kowacce rana, wanda ya yi ƙasa da adadin da hukumarmu za ta iya yi wa rajista ne a kullum ne''.

  7. Muna da ƙwarin gwiwar gudanar da zaɓe - INEC

    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta ce tana da cikakken ƙwarin gwiwa, wajen gudanar da zaɓen a watan da muke ciki.

    Yayin da wasu 'yan ƙasar ke ci gaba da nuna shakku kan ko ƙarancin kuɗin da Najeriya ke fama da shi, zai iya shafar zaɓukan ƙasar da za a fara a watan da muke ciki.

    Hukumar zaɓen ta INEC ta ce bayanan da suka samu daga gwamnan babban bankin ƙasar ya ƙara musu ƙarfin guiwar cewar CBN ɗin zai ba su kuɗaɗen da ake buƙata,kafin fara gudanar da zaɓukan ƙasar a makon gobe.

    Mai magana da yawun hukumar zaɓen ƙasar, Zainab Aminu ta shaida wa BBC cewa a kwanakin baya shugaban INEC ya ziyarci gwamnan babban bankin ƙasar inda gwamnan ya alƙawarta samar wa hukumarmu kuɗin da za mu gudanar da babban zaɓen ƙasar.

    Ta ƙara da cewa mutanen ƙasar ya nawan kambama matsala, a maimakon su jira su ga abin da lokaci zai nuna, tana mai cewa suna fatan samun kuɗin da hukumar za ta gudanar da zaɓen.

  8. Yadda masu mayar da tsofaffin kuɗi suka yi wa ofishin CBN da ke Abuja tsinke

    Gwamman mutane ne suka taru a harabar shalkwatar Babban Bankin Najeriya CBN da ke Abuja babban birnin ƙasar, domin musanya tsofaffin takardun kuɗinsu.

    CBN ɗin dai ya bayar da wani adireshin intanet da ya ce mutane suke shiga domin cike bayanansu, kafin su je bankin domin a sauya musu kuɗaden nasu.

    To sai dai mutanen sun ce tun safe suke gwada adireshin da CBN ɗin ya bayar amma kuma adireshin baya shiguwa

    Lamarin da ta sa suka taru a harabar ginin domin jin ta bakin banki, haka kuma sun yi ƙorafin cewa ma'aikatan bankin ba su saurare su ba.

    To amma wata majiya daga CBN ɗin ta shaida wa BBC cewa ba a ba su umarnin fara sauya wa mutanen kuɗin ba.

    Daga baya ne kuma wata jami'ar yan sanda ta yi wa mutanen jawabi, inda ta yi kira a gare su da su kwantar da hankula tare da ci gaba da gwada wannan adireshi da CBN din ya bayar.

  9. An samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

    Farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 21.82 a watan Janairun 2023, bayan da a watan Disamba ya sauka zuwa 21.34.

    A wani rahoto da hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar ranar Laraba ta ce an samu ƙaruwar farashin ne bayan da aka samu tsaiko wajen safarar abinci, da ƙaruwar kuɗin shigar da kaya ƙasar saboda faɗuwar darajar kuɗin ƙasar da kuma ƙaruwar tsadar kayayyaki a matsayin abubuwan da suka haddasa ƙaruwar farashin.

    Sauka da tashin farashi kayayyaki da ake samu cikin wata biyu na zuwa ne bayan matakin babban bankin ƙasar ya fito da tsarin sauya fasalin kuɗi, matakin da CBN din ya ce zai taimaka wajen raguwar farashin kayayyaki a ƙasar.

    Rahoton ya ce ''ƙaruwar farashin kayyaki ya ƙaru da kashin 0.47 cikin 100 a watan Janairu idan aka kwantanta da watan Disambar bara''

    Sannan kuma rahoton ya nuna cewa an samu ƙaruwar farashin idan kayayyaki da kashi 6.22 idan aka kwantata da watan Janairun 2022.”

  10. Tarzoma ta barke a wasu jihohin Najeriya kan ƙarancin takardun naira

    Tarzoma ta barke a biranen Najeriya masu dama da ke kudancin kasar biyo bayan sauya fasalin takardun naira na kasar da gwamnati ke kaddamarwa.

    Rahotanni na cewa wasu fusatattun masu hulda da bankuna a Warri, babban birnin jihar Delta da kuma a Benin City na jihar Edo sun kai wa bankuna a biranen biyu hari, har sun cinna wa wasu bankuna biyu wuta.

    Akwai kuma rahoton barkewar tarzoma a birnin Ibadan da ke kudu maso yammacin Najeriya, har wasu mutane sun toshe wasu manyan hanyoyin mota domin bayyana bacin ransu kan karancin sababbin takardun kudi a jihar.

    Barkewar tarzomar na zuwa ne bayan da Kotun Ƙolin Najeriya ta ta ɗage zaman sauraren shari'ar da wasu jihohin ƙasar 10 suka shigar kan dakatar da amfani da tsofaffin takardun kudin da babban bankin kasar CBN ya fara aiwatarwa.

  11. Tashin farashin kaya ya ragu a Ghana a karon farko cikin wata 19

    Tashin farashin kayayyaki da ayyuka ya ragu a karon farko a Ghana a cikin wata 19 kamar yadda alƙaluman hukuma suka nuna.

    Yawan tashin a watan Janairu kashi 53.6 ne idan aka kwatanta da kashi 54.1 cikin ɗari a watan da ya gabata.

    Sai dai kuma tashin farashin kayan abinci ya ƙaru kaɗan zuwa kashi 61.0 cikin ɗari a watan Janairu yayin da tashin farashin kayan da ba na abinci ba ya yi ƙasa zuwa kashi 47.9 cikin ɗari, kamar yadda alƙaluman hukumar ƙididdiga ta Ghana ta fitar.

    Wannan na nufin ana samun ƙaruwar tashin farashi amma dai ba da sauri ba kamar a da.

    Ragin farashin mai ya sa kuɗin mota ya ragu, kamar yadda shafin intanet na gidan rediyon Joy FM ya wallafa.

    Tattalin arzikin Ghana na cikin matsala inda bayanai suka nuna cewa ƙarfin biyan bashi na ƙasar ya ragu matuƙa.

  12. Cutar Marburg da ta ɓarke a Equatorial Guinea ta ɓulla a Kamaru

    Hukumomin lafiya a Kamaru sun ce san gano mutum biyu da suke ganin kamar suna ɗauke da cutar Marburg a wani yanke da ke kusa da iyaka da Equatorial Guinea, inda cutar mai kisa ta ɓarke.

    Ba wanda daga cikin mutanen biyu ya yi tafiyar da ya tsallaka iyaka zuwa inda cutar ta ɓarke a maƙwabciyar ƙasar.

    A yanzu jami'ai na ƙoƙarin gano duk wani da mutanen suka yi mu'amulla da shi domin a gwada a ga ba ya ɗauke da cutar don gudun yaɗa ta.

    Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta tura ƙarin jami'ai domin gano mutanen da suka yi mu'amulla da waɗanda suka kamu da cutar a Equatorial Guinea domin daƙile ta.

    Ana ganin mutum tara ne cutar ta hallaka a Equatorial Guinea, inda ake da ƙarin wasu mutum 16 da ake fargabar sun kamu da cutar.

    Tuni aka sanya dokar taƙaita zirga-zirga a yankin kan iyaka a kudancin Kamaru.

  13. An yi zanga-zanga kan ƙarancin mai da naira a Oyo

    An yi sabuwar zanga-zanga a kan ƙarancin naira da man fetur a babban birnin jihar Oyo, Ibadan, da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Jama'a sun yi dafifi inda suka yi tattaki tare da nuna damuwarsu a kan wahalar da suke ci gaba da sha kamar a sauran wasu sassan ƙasar kan ƙarancin sababbin takardun kuɗin ƙasar na naira 200 da 500 da 1,000 da kuma ƙarancin man fetur.

    Jaridar The Nation ta ruwaito cewa masu motocin sufuri sun jagoranci zanga-zangar a yankin Eleyele/Ologuneru da ke babban birnin.

    Sauran wasu wuraren da aka ɗanyi zanga-zangar in ji jaridar sun hada da Gbopa da Ologuneru da Apete da Sango da titin Poly da kuma yankin titin Mokola da kuma titin Iwo.

    Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Eleyele/Eruwa, a dalilin hakan mafiya suka kasa wucewa ta babbar hanyar.

    Zanga-zangar ta shammaci dubban mutane ganin yadda suka kasa samun wucewa ta tituna da dama.

    An ce masu sufurin da suka shirya zanga-zangar sun damu ne kan ƙarancin kuɗin na naira inda fasinjoji da masu gidan mai ke ƙin karɓar tsofaffin takardun 200 da 500 da 1,000.

  14. 'Yan ci-rani sama da 70 sun nutse a tekun Libya

    Akalla 'yan ci-rani 73 ne suka ɓace kuma ake fargabar sun mutu bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya nutse a gabar tekun Libya a jiya Talata kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya (IMO) ta sanya a shafin Twitter.

    Rahotanni sun ce mutum bakwai ne kawai suka iya tsira zuwa bakin gaɓa a yanayi mai tsananin gaske kuma tuni aka kwantar da su a asibiti in ji sanarwar.

    An ce jirgin ruwan nasu ya kama hanyar zuwa Turai ne in ji hukumar 'yan gudun hijirar ta duniya.

    Sau da dama 'yan gudun hijira da 'yan ci rani kan rasa rayukansu a irin wannan tafiya mai haɗarin gaske da sukan yi a ƙananan jiragen ruwa marassa inganci zuwa Turai.

  15. Somalia ta sanya doka kan kamfanonin waya domin toshe hanyoyin samar da kuɗi ga 'yan ta'adda

    Gwamnatin Somalia ta umarci kamfanonin waya da bankuna da sauran masu hada-hadar kasuwanci da su yi rijistar harkokinsu da kuma mutanen da suke mu'amullar kudi da su domin magance matsalar halatta kuɗin haram da kuma samar da kuɗi ga 'yan ta'adda.

    Tashar talabijin ta ƙasar ce ta sanar da haka, kuma a wani taron manema labarai ministan yaɗa labarai Daud Aweis shi ma ya jaddada haka sannan ya umarci kamfanonin waya da su yi rijistar kwastomominsu tare da ɗaukar hotunansu da na zanen yatsunsu.

    Ministan ya kuma gargaɗi jama'a a kan taimaka wa 'yan ta'adda da sauran 'yan ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya.

    Mista Aweis ya kuma yi gargaɗin cewa duk kamfanin da aka samu na mu'amulla da 'yan bindiga ko 'yan ta'adda za a soke shi.

    Bugu da ƙari ya ce duk kamfanin da aka samu ya ƙi bin umarnin gwamnatin to za a soke lasisinsa.

    Ya ce an ɗauki waɗannan matakai ne domin toshe hanyoyin da 'yan ta'adda da 'yan bindiga ke samun kuɗaɗe.

    A jiya Talata hukumar leƙen asiri ta ƙasar ta gargaɗi 'yan kasuwa da su guji zuwa yankunan da ke hannun 'yan kungiyar al-Shabab a matsayin wani martani ga gayyatar da ƙungiyar ke yi.

  16. Labarai da dumi-dumi, Canjin kuɗi: Kotun Ƙoli ta ɗage zama zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabarairu

    Kotun Ƙolin Najeriya ta ɗage zaman sauraren shari'ar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka shigar kan ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar na takardar naira 200 da 500 da 1,000.

    Kotun ta ɗage zaman ne bayan da wasu jihohi guda tara suka bi sahun gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara waɗanda suka shigar da ƙarar tun da farko.

    Jihohin da ke ɓangaren masu ƙarar bayan guda ukun na farko su ne Kano da Katsina da Sokoto da Lagos da Ondo da Ogun da Ekiti da Rivers.

    Ita ma a ɓangarenta gwamnatin ƙasar ta samu jihohin Edo da Bayelsa a matsayin waɗanda ke kare kai a shariar.

    Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai da takwaransa na jihar Kogi Yahaya Bello sun halarci Kotun a yau.

    Yanzu dai al’ummar Najeriya za su ci gaba da jira har zuwa 22 ga watan Na Fabrairu kafin sanin matsaya game da ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin ko kuma a’a.

    Gwamnatocin jihohin Kaduna, da Zamfa da kuma Kogi ne suka shigar da ƙarar, inda tun farko kotun ta bayar da umurnin jingine wa’adin daina amfani da takardun kuɗin na 10 ga watan Fabrairu, wanda bankin ya bayar a farko.

    Mutane dai a Najeriya sun shiga ruɗani a kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin na naira 1,000, da 500, da 200 duk da umurnin da kotu ta bayar na jingine wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.

    Haka nan rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, suna bayar da hujjar cewa umurni ne suka samu daga Babban Bankin na Najeriya.

    Bugu da ƙari wasu masu ƙananan sana’o’in da dama sun daina amsar tsofaffin kuɗaɗen.

  17. An kori 'yar majalisar dattawa daga majalisa saboda jinin al'ada a Kenya

    An kori wata sanata daga zauren majalisar dattawa saboda ta halarci zaman majalisar da kayan da jinin al'ada ya bata, a wata fafutuka da take yi ta neman kyautata wa mata masu al'ada.

    Sanata Gloria Orwoba, ta haɗakar jam'iyya mai mulki na shirin gabatar da wani ƙuduri a majalisar a yau Laraba, wanda zai nemi da a riƙa bai wa mata masu al'ada auduga kyauta a wani yunƙuri na yaƙi da matsalar talauci da ke hana wasu matan amfani da auduga lokacin jinin al'ada saboda rashin hali.

    A yayin zaman majalisar ne a jiya Talata 'yan majalisar suka janyo hankalin shugabansu a kan kayan da ta sa kwat da wando farare kuma jinin al'ada ya bata wandon.

    'Yar majalisar ta mayar da martani da cewa abin ya bata mamaki matuƙa, '' a ce wani zai tashi a nan ya ce na kunyata majalisa saboda kawai al'ada ta zo wa mace.''

    Daga nan shugaban majalisar Amason Kingi ya uamrce ta ta je ta sauya kayanta kafin ta dawo da shiga zauren.

  18. Tsohon shugaban Kenya zai jagoranci masu sa ido na ƙungiyar AU a zaɓen Najeriya

    Ƙungiyar Tarayyar ƙasashen Afirka, AU ta naɗa tsohon shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta domin ya jagoranci tawagar jami'anta da za su yi aikin sa ido a zaɓukan da ke tafe a Najeriya.

    Tawagar masu sanya idon ta ƙunshi wakilan hukumoimin zaɓe na ƙasashen ƙungiyar ta AU da ƙungiyoyin farar hula da ƙwararru masu zaman kansu da kuma wasu hukumomi na ƙungiyar ta AU.

    Aikin tawagar zai ƙunshi sanya ido tare da bayar da bayanai masu inganci a kan zaɓukan da kuma bayar da shawara kan yadda za a inganta zaɓen a nan gaba bisa abubuwan da suka gani.

    Ana kuma sa ran tawagar ta nuna goyon bayanta da tallafa wa dorewar tsarin dumukuraɗiyya da zaman lafiya da ci-gaba a Najeriya.

    A ranar 25 ga watan nan na Fabarairu ne 'yan Najeriya za su yi zaɓen shugaban ƙasa da 'yan majalisun dokoki na tarayya sannan kuma ranar 11 ga watan Maris su yi zaɓen gwamnoni da 'yan majalisun dokoki na jiha.

  19. An mayar da 'yan Najeriya kusan 150 gida daga Nijar

    Akalla 'yan Najeriya 150 ne aka mayar kasarsu jiya Talata daga Yamai babban birnin Nijar, inda hukumar bayar da gajin gaggawa ta karbe su a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen wadanda suka koma gida don radin kansu sun sauka ne a wani jirgin sama da aka yi shatarsa na kasar Mali da kusan karfe 11:20 na safe.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya da hadin guiwar hukumar shige da fice ta Najeriya da sauran hukumomi na Najeriya suka shirya mayar da mutanen kasar tasu.

    Mutanen sun hada da maza 98 da yara maza 11 da kananan yara maza biyu sai mata manya 24 da yara maza 13 da kuma jarirai mata biyu.

  20. Tsofaffin kuɗi: Kotun ƙolin Najeriya za ta saurari ƙarar da aka shigar kan soke wa'adin CBN

    A yau Laraba ne ake sa ran kotun ƙolin Najeriya za ta saurari dukkanin ɓangarori a ƙarar da wasu gwamnonin johohi suka shigar domin hana Babban Bankin Najeriya aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin naira na 1,000, da 500, da kuma 200.

    Gwamnatocin jihohin Kaduna, da Zamfa da kuma Kogi ne suka shigar da ƙarar, inda tun farko kotun ta bayar da umurnin jingine wa’adin daina amfani da takardun kuɗin na 10 ga watan Fabrairu, wanda bankin ya bayar a farko.

    Mutane dai a Najeriya sun shiga ruɗani a kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin na naira 1,000, da 500, da 200 duk da umurnin da kotu ta bayar na jingine wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.

    Haka nan rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, suna bayar da hujjar cewa umurni ne suka samu daga Babban Bankin na Najeriya.

    Haka nan ma wasu masu ƙananan sana’o’in da dama sun daina amsar tsofaffin kuɗaɗen.

    Jama'ar ƙasar na sanya ido kan abin da kotun za ta ce a zamanta na yau, wanda zai iya yin tasiri kan halin da al'ummar ke ciki na ruɗani game da ci gaba ko kuma daina amfani da tsofaffin kuɗaɗen.