'Yan fashi sun tare hanyar Minna zuwa Abuja tare da kashe DPO

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Bankwana

    Nan muka kawo ƙarshen labarai da harotannin namu na yau.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan mu kwana lafiya daga nan BBC.

  2. Ba a kai wa Mai Mala hari ba - Gwamnatin Yobe

    j

    Asalin hoton, Mai Mala Facebook

    Gwamnan jihar Yobe da ke arewacin Najeriya Mai Mala Buni ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin yaƙin neman zaɓe a shiyyar Gashua da ke ƙaramar hukumar Bade.

    Sai dai gwamnatin jihar Yobe ta musanta Ikirarin tana cewa sai da gwamna ya bar wurin hayaniya ta ɓarke.

    Amma gidan Talabijin na ChannelsDubban magoya bayan APC ɗin ne da suka je yakin neman zaɓen suka riƙa yi wa gwamnan ihu suna cewa "ba ma yi, ba ma son Mai Mala Buni".

    An fara rikicin ne lokacin da gwamnan zai miƙa tuta ga 'yan takarar APC gabanin zaɓen 2023, kawai sai aka fara jifa da dutse da wasu abubuwan na daban.

    Sai da aka fitar da Gwamnan daga taron tare da taimakon jami'an tsaro.

    Yana yin dai haka ya tilastawa gwamnan da magoya bayansa barin yankin tare da komawa Damaturu ba tare da shiri ba.

    Mamman Mohammed wanda shi ne daraktan kula da kafafen yaɗa labari ya ce babu wani abu mai kama da wannan da ya faru.

    "Mambarin da ake gudanar da taron ne ya cika, lokacin da Sanata Ahmed Lawal ke bayani, sai aka ce kowa ya sauka kada ya ƙarye, har gwamna da shi sanata.

    "Dalilin barin wurin taron da wuri kenan. Muna zuwa wani gidan mai muka ji rikici ya ɓarke tsakanin mabiya jam'iyyar tamu," in ji Mamman.

  3. Manchester City ta doke Aston Villa ta koma matsayinta na biyu

    G

    Asalin hoton, Getty Images

    Man City ta samu nasara a kan Villa a wasan farko tun bayan zargin da aka yi mata ka karya dokoki sama da 100 na gasar Premier.

    City ta samu nasara ne da ci 3-1 a wasan da ta buga a Etihad, ta kuma koma matsayinta na biyu da maki 48.

    Gabanin buga wasan da ta yi nasara, City ta koma ta uku bayan Manchester United ta doke Leeds da ci biyu babu ko ɗaya ta hada maki 46 yayin da City take da 45.

    Yanzu dai maki uku ne tsakanin Arsenal da ke matsayi na daya da Man City da ke matsayi na biyu, kuma za su buga wasa tsakaninsu a ranar Laraba.

    Idan City ta samu nasara za ta yi kunnen doki da Arsenal da maki 51 dukkansu, kwallaye kuma za su raba tsakin kungiyoyin biyu.

  4. Hukumomin yankin Somaliland na zargin gwamnatin Somalia da goyon bayan 'yan tawaye

    BBC

    Hukumomi a yankin Somaliland mai iƙirarin cin gashin kai, sun zargi gwamnatin Somalia da tura dakaru don tallafa wa 'yan tawayen da ke son komawa cikin ƙasar.

    Sun kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su matsa wa ƙasar kan ta janye hannunta daga rikicin da ake yi a garin Las Anod, wanda ya shiga kwana na bakwai.

    Zuwa yanzu jami'ai a Somalia ba su ce komai ba.

  5. Cikin kwana 43 Falasɗinawa 46 aka kashe a rikicinsu da Isra'ila

    BBC

    Jami'an lafiya a Falasɗinu sun ce dakarun Isra'ila sun harbe wani yaro ɗan shekara goma sha huɗu yayin wani hari a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Wani kakakin sojan Isra'ila ya ce an buɗe wa dakarunsu wuta a lokacin da suke kokarin kama wani ɗan gwagwarmaya a birnin Jenin, su kuma suka mayar da martani.

    Rikici tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa ya ƙara ƙamari a 'yan watannin nan.

    Tun bayan shigarmu sabuwar shekara, an kashe Falasɗinawa arba'in da shida - ciki har da masu kai hare-hare, da fararen hula da kuma 'yan gwagwarmaya.

    Kazalika, an kashe fararen hular Isra'ila tara da kuma wani ɗan Ukraine a ɗan tsakanin.

    Suma dai Falasɗinawan sun kashe Isra'ilawa da dama a wannan yaƙin da suke yi, cikin waɗan nan kwanaki.

  6. An kai wa gwamnan Yobe Mai Mala Buni hari yayin yaƙin neman zaɓe a Gashua

    M

    Asalin hoton, MAi

    Gwamnan jihar Yobe da ke arewacin Najeriya Mai Mala Buni ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin yaƙin neman zaɓe a shiyyar Gashua da ke ƙaramar hukumar Bade.

    Gidan Talabijin na Channels Dubban magoya bayan APC ɗin ne da suka je yakin neman zaɓen suka riƙa yi wa gwamnan ihu suna cewa "ba ma yi, ba ma son Mai Mala Buni".

    An fara rikicin ne lokacin da gwamnan zai miƙa tuta ga 'yan takarar APC gabanin zaɓen 2023, kawai sai aka fara jifa da dutse da wasu abubuwan na daban.

    Sai da aka fitar da Gwamnan daga taron tare da taimakon jami'an tsaro.

    Yana yin dai haka ya tilastawa gwamnan da magoya bayansa barin yankin tare da komawa Damaturu ba tare da shiri ba.

  7. Rihanna ta dawo waƙa bayan hutun shekara bakwai

    BBC

    Magoya bayan Rihanna na hasashen cewa wqasan da za ta yi a lokacin hutun rabin lokaci a gasar Super Bowl, zai iya zama daga daga cikin manyan casu a fagen waƙa.

    Rihanna ba ta saki wani faifan kiɗa nata na kanta ba tun 2016, dan haka ana da kyakkyawan tsammani, musamman bayan haihuwarta a bara.

    Magoya bayan na fatan mawaƙiyar 'yar shekara 34 za ta dawo fagen da ƙarfinta a ƙarshen wannan shekara.

    1. Kadara

    Darajar kadarorin mawakiyar ta kai dalar Amurka bliyan 1.7. Kimanin dala biliyan 1.4 ba a harkokin waƙa ta same su ba, ta same su ne daga kamfaninta na sayar da kayan kwalliya, Fenty Beauty.

    2. Shuhura

    An haifeta shekara 34 baya, a Saint Michel, da ke tsuburin Barbados.

    Shuhurarta ta fara ne a 2003 lokacin da ita da ƙawayenta suka yi Evan Rodgers.

  8. Man United ta samu nasara kan Leeds ta koma matsayi na biyu

    BBC

    Manchester United ta koma ta biyu a Premier League, bayan cin Leeds United 2-0 a wasan mako na 23 ranar Lahadi.

    Marcus Rashford ya fara cin kwallo a minti na 80, kuma na 13 da ya zura a raga tun bayan kammala gasar kofin duniya.

    Ba dan wasan da ya kai Rashford yawan zura kwallaye a raga tun bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

    Sauran minti biyar a tashi daga wasan a Elland Road, United ta kara na biyu ta hannun Alejandro Garnacho, wanda hakan ya sa ta hada maki uku.

  9. Turkiyya ta bayar da izinin kama mutum 113 kan laifukan gine-gine

    hoton ginin da ya rufta

    Asalin hoton, EPA

    Jami'an Turkiyya sun ce sun bayar da izinin kama mutum 113 saboda hannu a aikin gine-ginen da suka rufta a lokacin girgizar ƙasar da ta afku ranar Litinin.

    'Yan sandan ƙasar sun kama akalla mutum 12, ciki har da masu kwangilar gine-ginen.

    Tashe-tashen hankula na kawo tsaiko ga aikin ceton a wasu sassan kudancin Turkiyya,

    Adadin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu a Turkiyya da Siriya ya zarta 30,000.

    Ana sa ran samun ƙarin mutanen da za a kama a ƙasar, lamarin da ake ganin tamkar ɗora alhakin bala'in kan wasu mutane daban.

    Masana sun kwashe shekaru suna gargaɗin cewa sabbin gine-gine a ƙasar suna cikin hatsari sakamakon wasu tsare-tsaren gwamnati da ke kunshe da rashawa a cikinsu.

    Waɗannan tsare-tsare suna yi wa 'yan kwangila afuwa waɗanda a wasu lokuta ke yi wa dokokin gine-ginen ƙasar karan-tseye, a ƙoƙarinsu na haɓaka gine-gine, ciki har da yankunan da ke da hatsarin samun girgizar ƙasa.

    Dubban gine-gine ne dai suka rushe a lokacin girgizar ƙasar da ta afku a ƙasar, lamarin da ya sa ake ɗiga ayar tamabaya game da cewa ko rashin bin ƙa'idar gine-gine ce ta haddasa munana bala'ain.

  10. 'Yan fashi sun tare hanyar Minna zuwa Abuja tare da kashe Baturen 'yan sanda

    'yan fashi

    Asalin hoton, AFP

    Wasu 'yan fashin daji a jihar Niger da ke arewacin Najeriya sun ƙaddamar da wasu hare-hare a ƙarshen mako, lamarin da ya kai ga kisan baturen 'yan sanda na Paiko da wasu 'yan sanda huɗu a ƙaramar hukumar Paikoro a jihar.

    Rahotonni sun ce an harbe tare da kashe jami'an 'yan sandan a daidai ƙauyen Kwakuti da ke kan hanyar Minna zuwa Suleja ranar Asabar.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da mutuwar Baturen 'yan sandan da kuma jami'ansa huɗu a lokacin musayar wuta da 'yan fashin.

    Ya ƙara da cewa “Da misalan ƙarfe 11:00, muka samu rahotonnin da ke cewa an ga wasu 'yan fashi a wajen ƙauyukan Kwakuti da Dajigbe da ke yankin Lambata, suna ƙoƙarin kai wa wasu garuruwa hari a ƙaramar hukumar Gurara a jihar'', in ji shi.

    “Daga nan aka haɗa runduna da ta ƙunshi jami'an 'yan sanda daga ofisoshin 'yan sanda na Gawu-Babangida da kuma Paiko, da kuma jami'an soji da da 'yan sa kai domin zuwa wajen da aka samu rahoton ganin 'yan fashin'', in ji mista Abiodun

    DSP Abiodun ya ci gaba da cewa daga nan ne suka far wa 'yan fashin dajin inda suka kshe da da,ma daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga a jikinsu.

  11. NDLEA ta kama jagoran coci da wasu mutum biyu kan safarar ƙwaya

    Kwaya

    Asalin hoton, NDLEA

    Jami'an Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama jagoran cocin Seraphic and Sabbath Assembly da ke jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya. tare da wasu mutum biyu bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

    A wata sanarawa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Femi Babafemi, ya sanya wa hannu aka kuma wallafa ta a shafin hukumar na Tuwita, ta ce an kama mutanen ne bisa zargin safarar kwaya da tabar wiwi zuwa Dubai.

    Jagoran cocin mai suna Priest Nnodu Azuka Kenrick an kama shi ne bayan da ka kama wani ɗalibin kwalejin addinai ta Samanda da ke Ibadan a jihar Oyo tare da dillaliyar ƙwayar mai suna Oyoyo Mary Obasi.

    Hukumar ta ce an kama mutanen ne kan yunƙurin fitar da ƙwayar 'methamphetamine' da tabar wiwi da aka ƙunshe cikin jarakunan manja a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke birnin Legas, domin kai su ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. An yanke wa sojoji bakwai hukuncin kisa bayan tserewa daga fagen daga

    Hoton sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke wa sojojin DR Kongo bakwai hukuncin kisa saboda 'tsorata a gaban abokan gaba' lamarin da ya sa suka gudu, a fagen daga da suke fafatawa da 'yan tawayen M23.

    Lamarin da kuma ya haifar tsoro da razani a zukatan al'ummar yankin.

    Ranar Alhamis ne sojojin suka wuce ta tsakiyar garin Sake, kilomita 25 yamma da garin Goma da ke gabashin ƙasar .

    ''Suna ta harbi a iska bayan da suka guje wa abokan gaba a fagen daga'', kamar yadda mai shigar da ƙara a kotun sojin ƙasar ya bayana wa kotu ranar Asabar.

    Hukumomi a lardin Kivu sun ce sojojin masu muƙamin Kofur sun musanta zargin, kuma lauyansu ya ce za su ɗaukaka ƙara game da hukuncin.

    Mai gabatar da ƙarar ya zarge su da janyo kisan kai, bayan da fararen hula biyu suka mutu wasu huɗu kuma suka samu munanan raunuka, saboda razanarwar da sojojin suka janyo wa mutane.

    A baya-bayan nan dai dubban mutane ne suka tsere wa muhallansu a garuruwan Goma da Minova yayin da 'yan tawayen M23 ke ci gaba kusantar garuruwan daga garin Masisi da ke yammaci.

    A watan Nuwamban bara, kotun sojin ƙasar ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin kisa saboda ''guduwa a filin daga'' a lokacin faɗa da 'yan tawayen, lamarin da ya haifar da tsoro da razana da kuma tarwatsewar fararen hula.

    A DR Kongo ana yanke hukuncin kisa, to sai dai rabon da a zartar da hukuncin tun shekarar 2003, a maimakon haka ana sassauta hukuncin zuwa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

  13. Amsoshin Takardunku

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  14. Matakan da za a bi domin kaɗa ƙuri'a ranar zaɓe - INEC

    Hoton shugaban INEC

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar Zaɓe mai zaman Kanta a Najeriya INEC ta bayyana matakan da za a bi domin kaɗa ƙuri'a a ranar zaɓe.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta bayyana matakai bakwai da ta ce za a bi domin kaɗa ƙuri'a ranar zaɓen.

    A ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokokin ƙasar.

    Matakin farko shi ne lokacin fara zaɓen wanda hukumar ta ce zai fara da misalin ƙarfe 8:30 na safe.

    Mataki na biyu shi ne gabatar da katin zaɓe ga jami'an zaɓe domin tantance shi ta hanyar amfani da na'urar BVAS.

    Daga nan sai a duba ko sunan mutum na cikin rajistar masu kaɗa ƙuri'a a wannan rumfar zaɓen.

    Mataki na gaba shi ne na'urar BVAS za ta tantance mutum ta hanyar saka ɗan yatsarsa a jikinta, daga nan sai a bai wa mutum ƙuri'ar da zai kaɗa.

    Sai matakin kaɗa ƙuri'a wanda hukumar ta ce ta ware wuri na musamman da za a shiga domin kaɗa ƙuri'ar a asirce.

    Matakin ƙarshe shi ne bayan kaɗa ƙuri'a mutum zai bar rumfar zaɓen, ko ya yi nesa da rumfar zaɓen na akalla mita 300.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Saudiyya ta aike da kayan tallafi zuwa Turkiyya da Siriya

    kayan agaji

    Asalin hoton, SPA

    Jiragen Saudiyya shida ɗauke da kayan agaji sun isa Turkiyya dpomin tallafa wa waɗanda iftila'in girgizar ƙasa ya shafa.

    Kayan agajin mai nauyin tan 98 ya ƙunshi kayan abinci da tantuna da barguna da kuma magunguna.

    Sarkin Saudiyya Salman bin Abdula'ziz tare da yarima mai jiran gadon sarauta Mohammed Bin Salman suka bayr da umarni kai kayan tallafin.

    Ana sa ran rarraba kayan tallafin uwa wuraren da girgizar ƙasar ta shafa a ƙasashen Turkiyya da Siriya.

    Kayan agaji

    Asalin hoton, SPA

  16. Hikataya: Labarin Wannan Rayuwa

    A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alƙalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo.

    A yau mun kawo muku labarin 'Wannan Rayuwa' wanda Fatima Rabi'u Janyau da ke Tudun Wada sabuwar hanya birnin Gusau jihar Zamfara ta rubuta.

    Badariyya Tijjani kalarawi kuma ta karanta.

    Bayanan sautilatsa lasifikar da ke sama domin sauraron labarin
  17. China za ta riƙa tallafa wa 'yan ƙasar domin ƙara haihuwa

    China

    Asalin hoton, VCG

    China za ta ƙara bai wa mutanen ƙasar tallafi domin ƙara yawan haihuwa, a yayin da raguwar yawan al'umma ke yin barazana ga tattalin arzikin ƙasar, kamar yadda wani jami'in tsarin iyalin ƙasar ya bayyana.

    A watan da ya gabata gamnatin ƙasar ta ce a shekarar da ta gabata yawan al'ummar China ya ragu da 850,000 raguwa ta farko da aka samu tun shekarar 1961.

    A ƙarshen shekarar da ta gabata ne hasashen cibiyar ƙididdigar yawan jama'a ta duniya WPR ya nuna cewa Indiya ta zarta china a yawan al'umma a duniya.

    Lamarin da Chinan ke kallo a matsayin babbar barazana ga tatalin arzikinta.

    Wani babban jami'i a hukumar tsarin iyalin ƙasar ya ce za a samar da wani tallafi ga iyalai domin haɓaka yawan haihuwa a ƙasar.

    A shekarar 1979 gwamnatin China ta kafa wata doka ta tsarin haifar ɗa ɗaya ga ma'aurata da nufin rage yawan al'ummar da take fama da shi.

    Duk iyalai ko ma'auratan da suka karya wannan doka, gwamnati na cin su tara, wasu kan rasa aikin su baki ɗaya a wasu lokutan kuma ana tirsasa mata zubar da cikin.

    Wannan tsari dai ya fuskanci suka daga sassa daban-daban na ƙasar, daga bisani kuma aka fara ɗora alhakin tsarin na gwamnati da cewa shi ne ya janyo aka samu ƙarin giɓi tsakanin mata da maza da ƙididdigar shekarar da ta gabata ta nuna maza sun fi matan China yawa da miliyan 30.

    A shekarar 2015 ne gwamnati ta kawo ƙarshen tsarin haihuwa ɗa ɗaya tilo ga ma'aurata, inda aka amince da haihuwar 'ya'ya biyu ga waɗanda ba su taba haihuwa ba.

    Shekara da shekaru kenan China ke fuskantar raguwar haihuwa, wanda hakan babbar barazana ce ga ƙasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

  18. ASUU ta soki gwamnatin tarayya kan ƙarancin Naira da man fetur

    ASUU

    Asalin hoton, FESTUS KEYAMO/TWITTER

    Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta soki gwamnatin tarayya kan ƙarancin Kuɗi da na man fetur da ake fama da shi a faɗin ƙasar.

    A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Emmanuel Osodeke ya fitar ya ce gwamnatin ƙasar a matakan tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomi na aiwatar da tsare-tsaren da suke wahalar da talakawan ƙasar.

    Ya ƙara da cewa matakin da Kotun Ƙolin ƙasar ta ɗauka na dakatar da aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi, zai taimaka wajen sauƙaka wa 'yan ƙasar halin matsin da suke ciki.

    Mista Osodeke ya ƙara da cewa tsarin da gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ɓullo da shi na ''hana walwalar kuɗi'' an taɓa yin sa a Indiya a shekarar 2016 wanda ya haifar da wahalhalu a ƙasar.

    “Dan haka, ASUU tana yaba wa Kotun Ƙoli da wannan hukunci ta hanyar la'akari da halin da talaka ke ciki wanda Emefiele ya jefa su ciki'', in ji Osodeke.

    A makon da ya gabata ne dai Kotun Kolin ƙasar ta dakatar da Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin kuɗin, bayan da wasu jihohin ƙasar uku suka shigar da ƙara gaban kotun.

  19. Girgizar ƙasar Turkiyya da Syria: Sama da mutum 28,000 sun mutu

    Hoton masu aikin ceto

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon bala'in girgizar ƙasar da ya afka wa ƙasashen Turkiyya da Siriya ya zarta 28,000, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

    To sai dai fatan samun ƙarin masu numfashi na gamuwa da cikas yayin da ake samun rahotonnin rashin zaman lafiya a wasu yankunan kudancin Turkiyya, lamarin da ke yin barazana ga masu aikin ceton kamar yadda wasu ƙungiyoyin agaji uku suka bayyana..

    Ƙungiyar agaji ta ƙasar Jamus da takwararta ta ƙasar Austria sun dakatar da ayyukansu ranar Asabar, sakamakon abin da suka kira rikici tsakanin wasu ƙungiyoyi a yankin.

    Wani jami'in ceto ya ce ana fargabar ƙaruwar tabarɓarewar tsaro, yayin da jigilar kayan abinci zuwa yankin ke gamuwa da cikas.

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce zai yi amfani da ƙarfi wajen ladabtar da duk wanda yake ƙoƙarin karya doka.

    Aƙalla gidaje 6,000 ne suka rushe a Turkiyya, lamarin da ke ɗiga ayar tambaya game gwamnatin Recep Tayyip Erdogan za ta iya yin abin da ya kamata domin kare rayuka.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana girgizar ƙasar da 'mummunan bala'in' da yankin ya taɓa gani cikin shekarar 100.

  20. Marabanku

    Diginza

    Asalin hoton, Diginza

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutunkun ƙarshen mako, da fatan kun wayi gari lafiya.

    Abdullahi Bello Diginza ne zai kasance tare da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Amma za mu fi mayar da hankali kan abin da ke faruwa a Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.