Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mun sauya fasalin kuɗi ne don maganin waɗanda suka ɓoye kuɗin haram - Buhari

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza

  1. Dole Isra'ilawa su kaucewa ɗaukar doka a hannu - Netanyahu

    Wani Bafalasdine ya bindige yahudawan Isra'ila a harabar wajen bautarsu da ke gabashin birnin Kudus da aka mamaye, lokacin da yahudawan suka taru domin gudanar da ibadarsu.

    Nan take dai 'yan sandan Isra'ila suka kashe dan bindigar.

    A wani jawabi da ya gabatar a talabiji bayan faruwar al'amarin, Firaminista Benjamin Netanyahu ya umarci 'yan Isra'ila su kaucewa daukan doka a hannunsu.

    Netanyahu ya ce yanayi ne irinsa mafi muni a tsawon shekaru, sai dai Yana mai jadada musu cewa gwamnatinsa za ta sanar da matakan gaggawa na martani.

    Mayakan Falasdinu sun yi murnar kai wannan hari, sai dai ba su bayyana ko akwai hannusu a harin ba.

  2. Barka da hantsi

    Buhari MUhammad Fagge ke fatan an tashi lafiya.

    Ni ne zan kasance da ku a wannan yini da zan kawo muku labarai da rahotanni daga ko ina sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu.