Rufewa
Masu bibiyar mu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza ke cewa sai da safenku
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza
Masu bibiyar mu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza ke cewa sai da safenku
Rundunar 'yan sandan jihar Naija da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama mutum biyu da take zargi da garkuwa da mutane a yankin ƙaramar hukumar Gurara da ke jihar, tare da kuɓutar da mutum bakwai , adanda suka haɗar da maza shida da mace ɗaya.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun ya ce an kama masu garkuwar ranar Juma'a sakamakon bayanan sirri da rundunar ta samu.
Inda nan take rundunar ta tura jami'anta zuwa yankin tare da haɗin gwiwwar jami'an sa kai.
Sanarwar ta ce jami'an 'yan sandan sun yi musayar wuta da masu garkuwar a cikin daji, daga nan ne kuma masu garkuwar suka gudu tare da barin mutum shida da ke ɓoye a hannunsu.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta tsawaita wa'adin karɓar katin zaɓe da a ke gudanawar a halin yanzu a fadin ƙasar.
A wata sanarwa da kwamishinan hukumar kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri'a Festu Okoye ya fitar ranar Asabar ya ce hukumar ta ƙara wa'adin karɓar katin zaɓen daga 29 ga watan Janairu zuwa biyar ga watan Fabrairu.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Hukumar Zaɓe ta zauna a yau Asabar 28 ga watan Janairu kwana guda bayan ta gana da kwamishinoninta na jihohi 36 da Abuja, ta kuma yanke hukunci game da tarin matsalolin da aka gabatar mata , ciki har da batun yadda karɓar katin ke gudana a ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar''.
“Sakamakon rahotonnin tsaikon da aka samu na karɓar katin zaɓen da kwamishinonin zaɓen na jihohi suka tattauna hukumar ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin karɓar katin zaben zuwa mako guda''.
Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar zaɓen ƙasar ke sauya ranar rufe karɓar katin zaɓen, wanda a baya ta saka ranar 12 ga watan Disamban 2022 kafin ta ɗaga shi zuwa ranar 29 ga watan Janairun da muke ciki.
A ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ne dai hukumar zaɓen ƙasar za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, da na 'yan majalisun dokokin ƙasar.
Amurka ta bayyana harin da aka kai kan ofishin jakadancin Azerbaijan a birnin Tehran na ƙasar Iran da cewa abu ne da ba za a ''lamunta'' ba, tare da kira ga Iran in da ta kare ofisoshin jakandan ƙasashen waje.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya ce Amurka ta yi Allah-wadai da harin wanda aka kai kan ofishin jakadancin Azerbaijan.
Mista Price ya ce Amurka za ta taimaka wa shugaban Azerbaijan game da buƙatar da ya yi na gaggauta gudanar da bincike game da harin.
Ya ƙara da cewa ''muna tunasar da gwamnatin Iran cewa a ƙarƙashin dokar Geneva, ƙasar ce ke da alhakin kare duka ofisoshin jakandancin ƙasashen waje da ke ƙasar''.
Sa'a ɗaya bayan harin ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da sanarwar cewa binciken farko ya nuna cewa maharin ba ya wakiltar wata ƙungiya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da 'yan ƙasar cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa 'yan ƙasar ba su wahala ba ta fuskar kasuwancinsu, da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofiin takardun kuɗinsu da sabbi a yayin da wa'adin da babban bankin ƙasar ya saka ke ƙara ƙaratowa.
Yayin da yake martani game da rahotonni dogayen layukan mutanen da ke shafe sa'o'i domin samun musanya tsoffin kuɗinsu a bankuna, lamarin da ya janyo suka daga ɓangarorin adawa a ƙasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya jaddada cewa an fito da batun sauya fasalin kuɗin ƙasar ne domin yin maganin mutanen da suka ɓoye kuɗin haram, ba don cutar da talaka ba.
Ya kuma ce hakan zai magance matsalar cin hanci da rashawa da ɗaukar nauyin ta'addanci da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Shugaba Buhari ya kuma ce tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar
Game da wahalhalun da talakawa ke sha na musanya kuɗaɗensu kuwa, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin taimaka musu wajen musanya kuɗaɗensu.
Ya kuma jaddada cewa babban bankin ƙasar da sauran bankunan ƙasar sun ƙara haɓaka hanyoyin musanya wa mutane kuɗaɗensu domin tabbatar da cewa an musanya wa kowa kuɗinsa kafin cikar wa'adin.
Babban bankin ƙasar dai ya saka ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar ƙarshe ta daina amfani da tsoffin takardun kuɗi na 200 da 500 da kuma 1000 a faɗin ƙasar.
Ƙungiyar Likitoci da ƙasa-da-ƙasa 'Doctors Without Borders International' ta sanar da dakatar da ayyukanta a wani asibiti a ƙasar Haiti bayan da wasu gungun 'yan bindiga suka harbe wani marar lafiya bayan sun sace shi daga ɗakin masu buƙatar kulawar gaggawa inda yake kwance.
Ƙungiyar ta ce wannan shi ne karo na biyu da irin hakan take faruwa a asibiti cikin wata shida a Port-au-Prince babban birnin ƙasar
MSF ta ce za ta koma aiki a cikin ƙasar ne kawai idan ta samu tabbacin tsaron lafiyar majinyata tare da ma'aikatanta.
Ƙasar Haiti na fama da tashe-tashen hankula daga masu ɗauke da makamai waɗanda ke iko da wasu yankunan babban birnin ƙasar.
An dakatar da 'yan wasa huɗu na Uruguay bayan ca da suka yi wa alƙalin wasan da ya busa wasansu na ƙarshe a kofin duniya da suka fafata da Ghana.
Fernando Muslera da Jose Maria Gimenez an dakatar da su wasanni huɗu, yayin da Diego Godin da Edinson Cavani an da katar da kowannensu wasa guda.
'Yan wasan ƙasar sun fusata ne bayan da alƙali ya gaza basu bugun fenareti.
Sun ci 2-0 amma duk da haka an kore su daga gasar saboda kwallayen da suka sha a baya.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta 'The Lancet' ta nuna cewa an samu rage fiye da rabin mutuwar mata, a sanadiyyar zuban jini bayan haihuwa a jamhuriyyar Nijar.
An cimma hakan ne bayan daukar wasu matakai uku da wasu masu bincike suka yi, da suka hada da amfani da wani magani mara tsada.
Matsalar zuban jini bayan haihuwa, ita ce matsalar da ta fi kowacce janyo mace-macen mata a kasashe masu karancin kudin shiga.
Inda mafiya yawan mace-macen ke faruwa a kasashen da ke kudu da hamadar Saharar Afrika da kuma kudancin Asiya.
Ita ma Najeriya da ke yankin yammacin Afrika tana fuskantar matsalar mace-macen mata sakamakon zuban jini bayan haihuwa.
Jami'ai a jihar Kaduna da ke arewacin kasar sun ce jihar ita ke kan gaba wajen samun matsalar a Najeriya.
Sai dai sun ce hukumomi na yungurin ganin an magance matsalar.
Tsohon Babban hafsan sojin kasa na Nigeria Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana kwarin gwiwa game da zaben Nigeria da za a fara cikin watan gobe.
Janar Buratai, wanda dan kwamitin yakin neman zaben Cif Bola Ahmed Tinubu ne na APC a zaben , yayin wata ziyara a sashen Hausa na BBC, ya shaida wa Ahmad Abba Abdullahi cewa yawancin masu barazanar hana zabe, magana ce kawai ta fatar baki , ba da gaske suke yi ba.
Wasu majiyoyi daga Isra'ila sun ce an jikkata mutum biyu a wani harin bindiga da aka kai Birnin Ƙudus.
Kakakin 'yan sandan Isra'ila ya ce wannan "harin ta'addanci ne"
An yi harbe-harben ne bayan ƙaruwar rikici da kashe-kashe Isra'ilawa bakwai Ƙudus da kuma Falasɗinawa tara a Jenin.
Jiragen sojin saman Indiya biyu kirar Rasha Sukhoi Su-30 da na Faransa sun yi haɗari.
Haɗarin ya faru ne a tsakiyar Jihar Madyha Pradesh.
Duka jiragen sun ta shi ne daga Gwalior, wani fili da suke atisayen jiragensu.
An shi gaba da bincike da kuma aikin ceto a inda abin ya faru.
Babu ko mutum daya da aka mabato ya jikkata ko ya rasa rayuwarsa.
Rahotannin cikin gida sun ambato cewa jirgin tsakiya ne ya janyo haɗarin.
Yayin haɗarin akwai matuƙa biyu a jirgin Su-30, yayin da ɗayan ke ɗauke da kwamanda guda.
An yi amannar cewa duka matuƙan na nan lafiya.
Da yiyuwar an wasan gaban Manchester United Jadon Sancho ya buga wasan da ungiyar za ta fafata da Reading a gasar FA a yau Asabar, bayan shafe watanni uku yana jinya.
Wasan arshe da an wasan mai shekara 22 ya buga shi ne wanda United ta yi 1-1 da Chelsea a watan Oktoba.
Kocin ungiyar Erik ten Hag ya ce dan wasan ya dawo kan karagar wasa, kuma ya fara atisaye da tawagar manyan ƙungiyar a a makon jiya.
"Yana atisaye da tawagarmu kuma za mu gani", kamar yadda Ten Hag ya bayyana.
"Na ce yana nan kan hanyarsa ta dawowa wasa sosai."
Manchester United za ta buga wasa tara a cikin kwanaki 30 masu zuwa.
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi kira ga Babban Bankin Najeriya CBN da ya ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗin da aka sauya a ƙasar.
Cikin wani bidiyo da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce idan aka yi duba da halin matsi da al'umma ke ciki ya kamata a ƙara wa'adin zuwa wani ɗan lokaci.
A cewar Atiku sauya fasalin kuɗi ba wani sabon abu ba ne a fadin duniya, ka zalika matakin ba sabo ba ne ga Najeriya, sai dai wa'adin da aka tsayar na 31 ga watan Janairun da muke ciki na jefa mutane cikin mawuyacin hali.
"Da yawan 'yan Najeriya musamman manoma da masu sana'ar hannu da mazauna ƙauyuka ba su da asusun banki, dan haka lokacin da aka ka'ide na daina karbar tsofaffin kuɗi ba mai yiwuwa ba ne," in ji Atiku Abubakar.
'Yan Najeriya da dama na ta kiraye-kirayen CBN ya sake nazari kan wannan wa'adi, la'akari da ƙarancin sabbin takardun kuɗin da ake da su a ƙasar.
Shugaba Biden na Amurka ya kira Benjamin Neyanyahu na Isra'ila a wayar tarho bayan kisan da aka yiwa yahudawa a wajen bautarsu.
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce zata bai wa Isra'ila duk wani taiamakon daya dace a cikin kwanaki masu zuwa.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, wanda ke shirin ziyartar Isra'ila a mako mai zuwa, ya ce kisan abin damuwa ne matuka.
Sakatare Janar na MDD, Antoniu Guterres, shi ma ya yi alla-wadai da harin, kazalika kasashen Burtaniya da Faransa da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kwalarar da ta ɓarke a yankuna da yawa na ƙasar Kenya, ta ɓalle a yankin Mandera.
A baya kwalarar ta ɓulla a yankunan Garissa da Wajir.
A tsakiyar watan Janairun da muke ciki, mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar an kwantar da shi a Asibiti.
Dr Mohamud Adan Mohamed, wanda shi ne shugaban ofishin lafiya na Mandera ya ce, sun ta aiki a baya domin kare yaɗuwar cutar.
Bayan nan likitoci suka tabbatar da cewa a ranar 15 ga watan Janairu, sai suka samu rahoton ɓullar cutar a Mandera.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun aika wa fadar shugaban ƙasar Najeriya cewa, sun ɗage ziyarar da aka tsara Shugaba Muhammadu Buhari zai yi a Jihar domin buɗe wasu manyan ayyukan raya ƙasa.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan Abba Anwar ya fitar ranar Asabar, ya ce Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wani taro da malamai da shugabannin siyasada sauran masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati, ya ce an dauki matakin ne domin kaucewa faruwar abin da ba zai yi daɗi ba.
A cewar Gwamnatin, akwai buƙatar lura da halin da ake ciki na matsi saboda wa'adin daina amfani da tsofaffin kuɗi da CBN ya gindayawa mutanen Najeriya, akwai kuma matsalar tsaro, duka sai an yi nazari a kansu.
A ziyarar da Shugaba Buhari ya je Katsina ne aka samu wani rikici da ya ja aka riƙa jifan motoci da kuma ƙona tayoyi a kan titi, nuna fushi ga matsalolin da ake ciki na ƙarancin man fetur da kuma wa'adin tsofaffin kuɗaɗe.
'Yan majalisa a Peru na tafka muhawara, domin duba yiwuwar ko kasar za ta iya gudanar da sabon zaɓe a wannan shekarar, a ƙoƙarin shawo kan rikicin siyasar ƙasar da ya yi tsanani.
Shugabar ƙasar da ke cikin matsi, Dina Boluarte ta bukaci 'yan majalisar su amince da sauyin.
Shirya zaben gaggawa na daga cikin buƙatar masu zanga-zangar da suka fusata, bayan hamɓarar da gwamnatin, Pedro Castillo, mai sassaucin ra'ayi.
An kashe gwamman mutane a arangama tsakanin masu bore da jami'an tsaro a cikin 'yan makonni, sannan datse manyan tittuna na kassara tattalin arzikin ƙasar.
Bankunan kasuwanci a Najeriya sun mayar da martani kan iƙirarin babban bankin Najeriya CBN kan cewa ya bai wa bankunan kasuwanci isassun sababbin kuɗaɗe kawai sun riƙe su ne.
Babban bankin a cikin makon da ya gabata ya ce ya bai wa bankunan kasuwanci isassun kuɗin da za su wadatar da buƙatar abokan hulɗarsu.
Ko da yake babu cikakken bayani kan adadin kuɗin da CBN ya buga domin maye tsofaffin da aka sanya 31 ga watan Janairu a matsayin lokacin da za a daina amfani da su.
Tuni dai wasu jihohi a ƙasar suka daina karɓar kuɗaɗen saboda wahalar da ake fuskanta a bankuna lokacin mai da tsofaffin.
A fadin Najeriya dai ana ta fama da ƙarancin sabbin kuɗaɗen da za a ci gaba da amfani da su a nan gaba.
'Yan sanda a Landan na tuhumar wani sojan Burtaniya da laifin ta'addanci.
Sanarwar da aka fitar ta ce Daniel Abed Khalife, mazaunin tsakiyar birnin Landan, ana zarginsa da kwarmata bayanai mai muhimmanci ga wani da yake aikata ko shirin kai harin ta'addanci a shekara ta 2021.
Wannan ta kasance Tuhuma ta biyu da ke da alaka da wannan zargi da ake yi, bayan ta farko a farkon wannan wata.
A yau Asabar za a gabatar da matashin mai shekara 21 a gaban kotu da ke Landan.