Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ana yi wa zaɓen 2023 zagon ƙasa – Tinubu

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Yan jarida a Kamaru na neman kariya saboda yawan kashe su da ake yi

    'Yan jarida a Kamaru sun yi kira da a ƙara basu kariya biyo bayan kisan da aka yi wa abokin aikinsu Martinez Zogo, wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnati.

    An tsinci gawar Mista Zogo wadda aka yi kaca-kaca da ita a kusa da Yawunde babban birnin ƙasar, kwana biyar bayan wasu mutane da ba a sani ba sun sace shi.

    Gabanin mutuwarsa, ya yi barazanar zai fasa kwai game da cin hantsi a gwamnatence.

    Kungiyar 'yan jarida ta Reporters Without Bordersta yi kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike kan wannan kisa, inda suka kira kasar da "ramin kabari ga 'yancin 'yan jarida".

  2. An sako magoya bayan Arsenal da aka kama kan murnar sun ci Manchester

    An saki magoya bayan Arsenal takwas da aka kama a garin Jinja na Uganda, lokacin da suke murnar nasarar da ƙungiyarsu ta samu a wasan hamayya da Manchester United a gasar Premier Ingila.

    Lokacin da aka kama su a ranar Litinin, suna sanye da rigunan Arsenal da kuma wani kofi a hannunsu.

    'Yan sanda sun ce babu wanda ya basu umarnin yin wannan murna wadda za ta iya haifar da rikici a cikin al'umma.

    Kakakin 'yan sanda na yankin James Mubi, yace bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin jami'an tsaro, an amince a sake su kowa ya kama gabansa amma an ginda ya musu sharuɗa.

    Ɗaya daga cikin magoya bayan ya faɗawa 'yan jarida cewa "sun nemi umarni gabanin wannan murna da suka gudanar da nasara kan Man United".

  3. Za a rufe kasuwanci a Kebbi saboda matsalar sauyin kuɗi

    'Yan kasuwa a Birnin Kebbi da ke arewacin Najeriya sun yanke shawarar rufe harkokin kasuwancinsu saboda ƙarancin sabbin kuɗi, wanda hakan ya sa harkokin kasuwancin fuskantar koma baya.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa a Jihar Kebbi Alhaji Umar Dangura Gwadangwaji, ne ya bayyana hakan, yana cewa 'yan kasuwa na ta ƙoƙarin samun sabbin kuɗin daga bankuna amma hakan ya ci tura.

    "In muka ci gaba da karɓar kuɗi daga hannun kwastoma, to wanne banki ne zai karɓi kuɗaɗen kafin a daina amfani da su," in ji shi.

    A cewar jaridar masu hayar mota da masu sayar da kayayyaki a gefen tituna a ranar Talata sun daina karɓar tsofaffin kudi daga kwastoma, saboda bankuna da masu POS basu da sabbin kuɗin suma.

  4. Ana tuhumar Google da amfani da haramtacciyar hanya don hana takwarorinsa ja da shi

    Gwamnatin Amurka ta yanko wa kamfanin fasaha na Google sammaci, inda ta ke zarginsa da coge , da hakan ya ba shi damar yin babakere a tallace tallacen internet.

    Dama gwamnatin da ta wuce ta taba gabatar da irin wannan korafi kan take taken goggle na hana kamfanoni motsi ta fannin tallace tallace.

    Masu shigar da kara na kuma zargin Google da amfani da haramtacciyar hanya don hana takwarorinsa ja da shi.

    Sai dai a martanin kamfanin ya musanta zargin da ake masa na hana kamfanoni motsi a internet, inda ya buga misali da Amazon da Meta da Microsoft, da ya ce suna gogayya da shi.

  5. Ƙiris ya hana India da Pakistan su harbawa juna makamin nukiliya - Amurka

    Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya rubuta a sabon littafinsa cewa kadan ya rage kasashen Indiya da Pakistan su harba wa juna makamin nukiliya a 2019, ba don Amurka ta shiga tsakani ba.

    A Littafin nasa mai suna ''Never Give an Inch'', Mr Pompeo ya ce yana yankin Hanoi wurin halartar taro kan Amurka da Koriya ta Arewa ne ya samu labarin cewa rikici tsakanin kasashen biyu ya dauki sabon salo, kuma tuni Pakistan ta fara hada makaminta na nukiliya don harba shi Indiya.

    Kuma hakan ya biyo bayan wani hari da Indiya ta yi ikirarin kai wa yan tawaye a yankin Kashmir, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Pakistan 40.

    Sai dai kawo yanzu daga Indiya har Pakistan ba bu wanda ya ce komai game da littafin na Pompeo.

  6. Barka da hantsi

    Masu bibiyarmu barkanmu da safiya da fatan an tashi lafiya.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya domin kawo muku labarai da rahotanni daga ko wanne sassa na duniya.

    Sai ku kasance da mu.