Jami'an tsaro sun kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan Edo 12

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Yan bindiga sun kai hari coci tare da yin garkuwa da mutum tara a Katsina

    Katsina

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun sace masu bauta tara a wani coci a ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Rahotonni sun ce 'yan bindigar sun je cocin ne da ke unguwar Gidan Haruna a kan babura da safiyar ranar Lahadi a lokacin da masu bautar ke gudanar da addu'o'insu.

    Reveran Yusuf Haruna shugaban ƙungiyar CAN reshen ƙaramar hukumar Kankara ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun sace mutum tara ciki har da mata bakwai da yara biyu.

    Ya ƙara da cewa maharan sun daki wani magidanci tare da karya shi a lokacin da suka kai harin.

    Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin arewacin ƙasar da 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

    A watan Disamban 2020 'yan bindiga sun kai wani hari makarantar sakandiren Kankara tare da yin garkuwa da ɗalibai 300, waɗanda daga baya a ka sako su.

  2. Hikayata: Labarin 'Jarumar Mace'

    A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alalan gasar Hikayata ta 2022, suka ce sun cancanci yabo, a yau mun kawo muku labarin 'Jarumar Mace'.

    Wanda Maryam Muhammad Sani da ke birnin Gombe ta rubuta, Nabeela Muktar Uba kuma ta karanta

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraron labarin
  3. Mutum bakwai sun mutu a harin bom a Somaliya

    Harin Bom

    Asalin hoton, AFP

    'Yan sandan Somaliya sun ce mutum takwas ne aka kashe a wani harin bom da ƙungiyar al-Shabab ta yi iƙirarin kai wa.

    Lamarin ya faru ne a tsakiyar yankin Hiran na ƙasar inda dakarun gwamnatin ƙasar da mayaƙan sa-kai ke ƙwace garuruwa daga hannun ƙungiyar ta al-Shabab mai alaƙa da Al-Qaeda.

    A farkon wannan watan ne aka kashe mutum 19 a wasu tagawayen hare-haren bom a yankin na Hiran.

    Babban jami'in Baturen 'yan sanda na yankin ya ce wani ɗan ƙunar baƙin wake ne ya tayar da bom a cikin motar da yake ciki a garin Buloburde da ke yankin.

    Hotunan da aka yaɗa sun nuna yadda gine-gine tare da wani masallaci suka lalace bayan harin.

    Wannan hari dai wata alama ce da ke nuna cewa har yanzu ƙungiyar al-Shabab na da sauran ƙarfi a yankin duk kuwa da ƙwace garuruwan da ke hannunta da dakarun gwamnati ke yi.

    A 'yan watannin baya-bayan nan mayaƙan sa-kai a yankin sun nuna sha'awarsu ta taimaka wa sojojin gwamnati wajen yaƙar 'yan tawayen.

    Ƙungiyar ta al-Shabab na tilasta wa mazauna yankunan da ke ƙarƙashinta biyan haraji a daidai lokacin mummunan fari ke haddasa arasar dabbobi da amfanin gona a ƙasar.

  4. Jami'an tsaro sun kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan Edo 12

    Edo

    Asalin hoton, others

    Hukumomin jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ce an kuɓutar da fasinjoji 12 na jirgin ƙasa, da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a tashar jiragen ƙasa da ke jihar a makon da ya gabata.

    An kama wasu daga cikin 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su, to sai dai wasu daga cikinsu sun tsere tare da wasu fasinjojin biyu a lokacin da jami'an tsaro ke ƙoƙarin kuɓutar da su.

    Hukumomin jihar sun ce an kuɓutar da mutanen 12 a lokacin da jami'an tsaro suka yi wa masu garkuwa da mutanen kwanton ɓauta.

    Tuni aka kai mutanen da aka kuɓutar ɗin asibiti domin duba lafiyarsu.

    Gwamnatin jihar ta alƙawarta ci gaba da nemo sauran fasinjojin biyu da ke hannun 'yan bindigar.

    Gwamnan jihar ya soki hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar kan gaza samar da tsaro kan tasoshin jiragen ƙasan duk da faruwar makamancin wannan hari a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar a shekarar da ta gabata.

    Tun da farko dai hukumomin sun ce mutum 32 ne 'yan bindigar suka yi garkuwa da su a harin da suka kai tashar jirgin ƙasa ta Igueben a makon da ya gabata, to sai dai daga baya hukumomin sun ce adadin mutanen 20 ne.

    An saki mutum shida a farkon makon nan a wani samame da jami'an tsaro suka kai wa 'yan bindigar.

    Kama mutane domin neman kuɗin fansa ba sabon abu ba ne a Najeriya, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tsaro a ƙasar a 'yan shekarun baya-bayan nan.

  5. Amsoshin Takardunku

    Shin wane ne Dakta Zakir Naik fitaccen malamin addinin musuluncin na ɗan ƙasar Indiya?

    Shirin namu na wannan mako wanda Haruna Shehu Tangaza ya gabatar ya yi duba kan tarihin rayuwar shahararren malamin addinin.

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  6. Zan kawo ƙarshen sace-sace da ƙwacen wayoyi a Kano - Salihu Tanko Yakasai

    Salihu

    “Sace-sace da kwacen waya su ne manyan kalubalen tsaro da ake fuskanta a Kano kuma za mu yi maganinsu''. A cewar ɗan takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jam'iyyar PRP Salihu Tanko Yakasai

    Ya ce ya rasa aikinsa sabo da matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta, a yayin da yake magana a zauren taron muhawar 'yan takarar gwamnan jihar Kano da BBC ta gudanar ranar Asabar.

    Ya ƙara da cewa ''maganar sace-sacen waya wannan babbar matsala ce'', kuma gwamnati mai ci ta ɗauki matakin dakatar da matsalar ta hanyar hana 'yan adaidaita fita tun daga ƙarfe goman dare, sai dai hakan na haifar da wata matsalar a cewarsa.

    Sai dai ya ce zai ɗauki matakin da ya dace domin dakatar da sace-sace da ƙwacen wayoyin ba tare da haifar da wata matsalar ba.

    Sannan ya ce zai ɗauki matakin inganta tsaro tun daga unguwanni zuwa mazaɓu, domin inganta tsaro a faɗin jihar.

  7. Buhari ya halarci bikin tunawa da 'yan mazan jiya karo na ƙarshe

    Buhari

    Asalin hoton, Twitter/Bashir Ahmad

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci bikin taron tunawa da 'yan mazan jiya, wanda kuma shi ne na ƙarshe da shugaban ƙasar zai halarta a matsayinsa na shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin tsaro na ƙasar.

    A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce wannan ne karo na takwas kuma na ƙarshe da Buhari ke halartar wannan biki a matsayinsa na shugaban ƙasa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Daga cikin waɗanda suka halarci bikin wanda aka gudanar a Abuja babban birnin ƙasar sun haɗar da mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da babban alƙalin alƙalan ƙasar, Mai shari'a Olukayode Ariwoola, da sauran manyan jami'an gwamnati.

    Ana dai gudanar da wannan biki ne a duk shekara domin tunawa da irin gagarumar gudunmowar da tsoffin dakarun ƙasar suka bayar wajen zaman lafiya da ci gaban ƙasar.

    A wajen bikin Shugaban ƙasar da sauran jami'an gwamnati kan ajiye furanni domin nuna jinjina ga 'yan mazan jiyan, tare da yin faretin girmama wa ga shugaban ƙasa, sannan kuma shugaban ya saki fararen tattabaru suka tashi sama duk domin nuna tunawa da irin ƙwazon da 'yan mazan jiyan suna nuna ga ƙasar.

  8. Zan gayyato masu zuba jari daga ƙasar waje zuwa Kano - Sha'aban

    Sha'aban sharada

    Dan takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jam'iyyar ADP sha'aban Ibrahim Sharada ya faɗa Aa taron muhawarar 'yan takarar gwamna da BBC ta gabatar cewa zai gayyato manyan-manyan 'yan kasuwa don su zo su zuba jari a jihar Kano domin bunƙasa harkokin kasuwancin jihar.

    Ya kuma ƙara da cewa zai baiwa karananna hukumomin gashin kansu, tare da inganta masana'antun jihar da ke Bomfai da Chalawa.

    ''Za mu janyo manyan 'yan kasuwa na ƙasashen wajen domin su zo Kano su haɗu da 'yan kasuwarmu tare da haɓaka kasuwanci a jihar'' in ji Sha'aban

    Da aka tambaye shi cewa baya ganin matsalar tsaron da ƙasar ke fusknata zai kawo cikas ga zuwamn masu zuba jarin daga ƙasashen waje?

    Sai Sha'aban ya ce zai gina kyakkayawar alaƙa da ƙasashen waje domin ba su damar zuwa ƙasar.

    Ya kuma sha alwashin habaka kuɗin shigar jihar daga biliyan 2.5 zuwa biliyan goma a kowanne wata

  9. NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi na kusan naira biliyan biyar

    kwayoyi

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeroiya NDLEA ta ce ta kama wasu miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya kai naira biliyan biyar a wani gidan ajiye kayyaki.

    A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ta gano tan bakwai na tabar wiwi a jihohin Legas da Borno da Edo da Enugu da Katsina da kuma birnin tarayya Abuja.

    Hukumar ta ce daga cikin miyagun ƙwayoyin da ta gano sun haɗar da ƙwayar tramadol da yawanta ya kai 3,264,630, da kwalaben kodin 3,490 da wasu ƙwayoyin.

    Yayin da yake yaba wa jami'an na NDLEA bisa wannan namijin ƙoƙari, shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi kira a gare su da su ƙara tsage dantse domin kawo raguwar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Zan kawo wa Kano sabon fasalin kasuwanci na zamani - Mohammed Abacha

    Ɗan takarar gwamnan jihar ƙano ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP Mohammed Abacha ya ce jihar na buƙatar sabon fasalin kasuwanci na zamani, kuma ya sha alwashin kawo hakan.

    Mohammed Abacha ya yi wannan iƙirari ne a lokacin muhawar 'yan takarar gwamnan jihar da BBC ta gabatar a Jihar ranar Asabar.

    Ya kuma sha alwashin tallafa wa ƙananan 'yan kasuwa domin su bunƙasa jarinsu.

  11. 'Yan bindiga sun ƙona limamin coci a jihar Niger

    Niger

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan bindiga a jihar Niger da ke tsakiyar Najeriya sun kai hari gari Kafin Koro a yankin ƙaramar hukumar Paikoro tare da ƙona wani limamin coci

    Rahotonni sun ce 'yan bindigar sun kai hari garin ne da asubahin ranar Lahadi inda suka fara harbin kan-mai-uwa-da-wabi kafin su nufi gidan limamin.

    A wani sako da rundunar 'yan sandan jihar ta fitar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ambaci faston da suna Rev. Father Isaac Achi na cocin St. Peters da cocin Paul Catholic da ke ƙaramar hukumar Paikoro.

    Sanarwar ta ce “'Yan bindigar sun yi yunƙurin shiga gidan limamin cocin, amma da suka kasa sai suka cinna wa gidansa wuta inda limamin cocin ya mutu sakamakon wutar da suka cinna wa gidansa''.

    Haka kuma 'yan sandan sun ce 'yan bindigar sun harbe wani abokin aikin limamin a lokacin da ya yi yunƙurin guduwa daga inda lamarin ke faruwa.

    Rundunar 'yan sandan ta ce nan take ta tura jami'anta zuwa inda lamarin ke faruwa, sai dai a cewarta kafin zuwan jami'an nata 'yan bindigar sun tsere.

  12. Zan daƙile cin hanci da rashawa domin bayar da ilimi kyauta a Kano - Abba Kabir Yusuf

    Abba kabir Yusuf

    Ɗan takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP Abba Kabkir Yusuf ya ce babban abin da gwamnatinsa za ta sanya a gaba shi ne bayar da ilimi kyauta ga 'yan asalin jihar.

    Abba kabir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron muhawar 'yan takarar gwamna da BBC ta shirya a jihar ranar Asabar.

    A lokacin da mai gabatar da muhawar ya tambaye shi cewa ta ina zai samo kuɗin da zai bayar da ilimi kyauta a jihar a daidai lokacin da jihohi da dama ke kokawa kan matsin tattalin arziki?

    Sai Abba Kabir ya ce ''Idan ka dakile cin hanci da rashawa a Kano to ka yi maganin matsalar''.

    Sannan ya ce zai bunƙasa hanyoyin samun kuɗin shiga ta hanyar nemo taimako a wajen ƙungiyoyin bayar da tallafi domin tallafa wa ilimi a jihar.

    Abba Kabir ya kuma ce zai mayar da hankali wajen ɗaukar isassun malaman makaranta domin wadata jihar da malaman da take buƙata.

  13. Ko wa Allah ya bai wa mulkin Kano za mu bi shi - Gawuna

    Gawuna

    Asalin hoton, Kano govt

    Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ko wa Allah ya bai wa mulkin jihar za su bi shi su kuma ba shi shawara, domin ciyar da jihar gaba.

    Ɗan takarar ya yi wannan maganar ne a lokacin wata muhawara tsakanin 'yan takarar gwaman jihar Kano da BBC Hausa ta gabatar ranar Asabar.

    Gawuna ya ce ''idan Allah ya so ya ba mu muna addu'ar ya yi riƙo da hannunmu za mu hidimta wa al'umma; idan kuma Allah bai ba mu ba, ko wa Allah ya bai wa za mu bi shi, kuma za mu ba shi shawara ta gaske, domin a samu ci gaban al'ummar jihar Kano''.

    Ɗan takarar ya kuma sake nanata kiran al'ummar jihar da cewa a zaɓi cancanta a lokacin zaɓen gwamnan da ke tafe ''a duba mutumin da ya cancanta a zaɓa''.

    Ya kuma ce a yi siyasa cikin lumana, domin kuwa ''Mu 'yan takarar duka da muka zo nan BBC Hausa ta sauke mu a ɗaki ɗaya kuma duka muka gaisa tare da mutunta junanmu'',.

    ''Dan haka ina kira ga magoya bayanmu da su zauna lafiya'' in ji Gawuna

  14. Mutum 12 sun mutu a harin da Rasha ta kai Dnipro

    Dnipro

    Asalin hoton, STR/EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

    Akalla mutum 20 ne suka mutu sanadin wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan wani rukunin gidaje a birnin Dnipro.

    Wasu da dama ne kuma suka jikkata a lokacin da ginin mai hawa tara ra ruguje.

    Masu agaji na ci gaba da neman waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ginin.

    Mataimakin magajin garin ya ce ana tunanin akwai mutane da dama da suka maƙale cikin ɓaraguzan ginin.

  15. Barka da hantsi

    Masu bin mu a wannan shafi Abdullahi Bello Diginza ke muku barkanmu da hutun ƙarshen mako, fatan an karya kumallo lafiya.

    Ku kasance tare da mu domin sanin irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya bin mu a shafukanmu na sada zumunta, domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Ku biyo mu.....

    Dumame

    Asalin hoton, Sayyadi

    Bayanan hoto, Ɗumame