Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda ta kaya a muhawarar 'yan takarar gwamna na jihar Kano

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Noma da kiwo: Sha'aban sharada

    Daukar samfurin kasar kowacce ƙaramar hukuma domin sanin irin noman da ya dace da ita.

    Yin nazari domin noma abubuwan da ba sa nomuwa Kano

    Ƙirƙiro da karoin madatsun ruwa domin noman rani

    Inganta kiwon kifi

    Dawo da harkar kiwo

    Samar da Abbatuwa (mahauta) ta zamani

    Dawo da noma gyada domin samar da dalar gyaɗa

    Dawo da harkar sayen abinci domin tanadar wa talakawa cikin farashin mai rahusa

  2. Tsaro: Mohammed Abacha

    Bibiyar waɗanda ake zargi da aikata muyagun laifuka domin lura da su

  3. Tsaro: Salihu Tanko Yakasai

    Warware matsalar tsaro ba tare da an haifar da wata matsalar ba

    Samar da tsaro tun daga mazaɓu da unguwanni

  4. Manufofin tsaro: Sha'aban sharada

    Tabbatar da an buɗe makarantun kwana da aka rufe a faɗin jihar nan sakamakon rashin tsaro

  5. Manufofin Gawuna kan Tsaro

    Tabbatar da samar da isassun jami'an tsaro domin magance matsalar tsaro a jihar

    Kashi 90 cikin dari na matsalar tsaro ta ragu

  6. Nasiru Yusuf Gawuna

    Yaye matasan da suka koyi sana'a a cibiyoyin koyar da sana'a da ake da su a jihar

    Wayar da kan matasa domin tabbatar da cewa ba su sayar da kaya aikin da aka ba su domin yin sana'o'i ba

    Tabbatar da cewa mata ba su sayar da jarin da aka ba su ba

  7. Mohammed Sani Abacha

    Samar wa matasa wajen da za su koyi sana'a

    Bunkasa sana'o'i noman rani ta hanyar madatsun ruwan da Kano ke da shi

  8. Amsa tambayoyin masu kallo: Abba Kabir Yufuf

    Bunƙasa sana'o'in mata

    Daukar nauyin auren zawarawa

    Tabbatar da ana biyan 'yan fensho kudadensu a kan lokaci

    Farfado da koya wa matasa sana'o'i

  9. Amsa tambayoyi: Salhu Tanko Yakasai

    Samar da wuraren koyon sana'a a kowacce ƙaramar hukuma domin sama wa matasa sana'o'i

    Tun daga sakandire za a rika koya wa matasa sana'o'i daban-daban ciki har da sana'o'in fasaha na zamani

    Samar wa mata jari domin inganta sana'o'insu

  10. Amsa tambayoyin masu sauraro

    Sha'aban Sharaɗa

    Ba za mu taɓa wa 'yan fansho kudaden su ba

    Kafa wata hukumoma da za ta rika kula da shige-da f-ficen mutane a jihar

    Matasa ne za su rika gudanar da gwamnati

  11. Manufofin Nasiru Yusuf Gawuna kan lafiya

    Wayar da kan mata domin su je asibiti su karɓi magani

    Inganta cibiyoyin lafiya a matakin farko a jihar Kano

  12. Manufofin Salihu Tanko Yakasai kan Lafiya

    Samar da cibiyar lafiya a matakin farko

    Daukar likitoci kusan 34,000 a jihar Kano

    Haɗin gwiwwa da jami'o'i domin samar da yawan likitocin da Kano ke bukata

    Inganta walwalar likitocin jihar

  13. Manufofin Sha'aban sharada kan lafiya

    sanya dokar ta-ɓaci kan fannin lafiya

    samara da cibiyar lafiya a matakin fako a kowacce mazaɓa

    Yin dokoki game da shan ƙwayoyi ba tare da izinin likita ba

    Bin matakai kafin maras lafiya ya je babban asibiti

    samar da manyan asibitoci a shiyoyin jihar Uku

  14. Manufofin Mohammed Abacha kan lafiya

    Kara yawan likitoci ga asibi

    Keɓe kashi 25 cikin dari na kasafin kuɗin jihar kan bangaren lafiya

    Gyara asibitoci tare da ɗaukar ma'aikatan jinya ma su yawa

  15. Manufofin Abba Kabir Yusuf kan lafiya

    Samar da magunguna ga asibitoci

    Daukar likitoci da ma'aikatan jinya

    Gyaran asibitocin jihar Kano

    Samar da motocin ɗaukar marasa lafiya

  16. Manufofin Nasiru Yusuf Gawuna kan ilimi

    Wajabta ilimi ga ƙananan yara a jihar Kano

    Samar da ilimin kyauta

    Tabbatar da yara mata sun yi karatu

  17. Manufofin Abba Kabir Yusuf kan ilimi

    Bayar da ilimin kyauta a faɗin jihar kano

    Kyautata wa malaman makaranta domin su samu aiwatar da aikinsu

    Ɗauke wa iyaye nauyin da ke kansu domin ba su damar sanya 'ya'yansu a makaranta

    Ɗaukar sabbin malamai domin maye gurbin waɗanda suka yi ritaya ko suka mutu

  18. Manufofin Momammed Sani Abacha kan ilimi

    Duba cancantar malamai domin inganta harkokin koyo da koyarwa

    Samar wa malaman makaranta kayan aikin da suka buƙata

    Gyara makarantun da suke buƙatar gyarawa

  19. Manufofin sha'aban sharada kan ilimi

    Dan takarar ya ce abubuwan da zai mayar da hankali a kansu a fannin ilimi sun hadar da

    Binciken adadin makarantun kano

    Duba ɓangeren cancantar malaman makarantun furamare

    Sauya wa malaman da ba su dace da koyarwa ba wajen aiki, tare da dauko wasu a wasu ma'aikatun domin su maye gurbinsu

  20. Manufofin Salihu Tanko Yakasai na jam'iyyar PRP kan ilimi

    Salihu Tanko Yakasai ya bayyana manufofinsa kan ɓangaren ilimi kamar haka:

    Mayar da hankali kan ilimi a matakin farko

    Samar da azuzuwa 28,000 a shekara huɗu

    Inganta makarantun Fasaha na Sakandire

    Ƙara kuɗi a fannin bincike a jami'o'i domin haɓaka bincike