Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yan sanda sun daƙile harin masu garkuwa da mutane a Plateau

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Bankwana

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai-tsaye karshen rahotannin kenan.

    Sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya kaimu.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin mulkin sojin Mali ta yi wa sojojin Ivory Coast 46 afuwa

    Sojojin Ivory Coast 46 da aka tsare a Mali tun daga watan Yuli sun bar ƙasar bayan afuwar da shugaban gwamnatin soja ya yi musu.

    Tsare su ya jawo rikicin difilomasiyya mai zafi, bayan an zarge su da ƙoƙarin yi wa tsaron Mali zagon-ƙasa.

    A watan da ya gabata ne aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara 20 yayin wata shari'ar sirri a birnin Bamako.

    Hukumomin Ivory Coast sun ce dakarun sun shiga Mali ne don taimaka wa Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ta Ecowas ta yi barazanar saka mata takunkumai idan ba a sake su ba.

  3. Dakarun Rasha sun kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi a garin Sevastopol na Ukraine

    Dakarun da ke biyayya ga ƙasar Rasha a Ukraine sun ce sun kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi da aka yi niyyar kai musu hari da shi a sansaninsu da ke garin Sevastopol.

    Zuwa yanzu hukumomin Ukraine ba su tabbatar da kai harin ba, amma hakan na nufin ba a mutunta tsagaita wutar da Shugaba Putin na Rasha ya ayyana ba saboda Kirsimetin 'yan gargajiyar Kiristoci ba.

    An samu rahotannin kai hare-haren atilare tsakanin ɓangarorin biyu a yankin Donetsk.

    Shugaba Putin ya aika saƙon Kirsimetin, yana mai cewa ranar "ta jawo aikata ayyuka na gari da kuma burika".

  4. Mutum shida sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Tunisiya

    Mutum aƙalla biyar ne suka mutu sanna wasu goma suka ɓace bayan jirgin ruwan da ke ɗauke da wasu 'yan ci-rani ya nitse a kusa da ƙasar Tunisiya.

    Hukumomi sun ce jirgin da ke cike maƙil ya yi yunƙurin tsallakawa cikin Italiya a lokacin da ya tsage a kusa da Kogin Sfax - wani wurin lodin 'yan Afirka da Gabas ta Tsakiya da ke son shiga Turai.

    Dakarun gadin iyaka na Tunisiya sun ceto mutum 20.

    A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, mutum fiye da dubu ashirin da biyar ne suka mutu ko suka ɓata yayin da suke ƙoƙarin tsallaka Kogin Bahar Rum ta Arewacin Afirka tun daga shekarar 2014.

  5. Madrid ta ɓarar da damar hawa teburin Laliga bayan shan kashi a hannun Villareal

    Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ɓarar da damar hawa teburin gasar Laliga bayan doke ta da ci 2-1 da Villareal ta yi a wasan mako na 16.

    Villareal ce ta fara cin kwallo ta hannun ɗan wasan ta Yeremy Pino mintuna ƙaɗan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Sai dai Madrid ta samu nasarar farke kwallon ta hannun Karim Benzema a bugun fenariti ana minti 60.

    Daga bisani ne kuma ɗan wasan Villareal Gerard Moreno ya saka su a gaba a bugun daga fenariti bayan da kwallo ta daki hannun dan wasan bayan na Real Madrid, David Alaba.

    Wannan sakamako na nufin har yanzu Madrid na a mataki biyu ne na teburin gasar Laliga maƙi ɗaya da Barcelona wadanda za su fafata da Atletico Madrid a gobe Lahadi.

  6. Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai na jam'iyyar PDP a Kebbi ya rasu

    Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai na jam'iyyar PDP a mazaɓar Birnin Kebbi da Kalgo da Bunza da e jihar Kebbi, Abba Abba Muhammed Bello, ya rasu.

    Bello ya rasu ne a ranar Juma'a bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a cewar Babban Darektan Kwamitin Ƴakin Neman Zaɓen Gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Shehu.

    Marigayi Abba ya kasance ɗa na farko ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dr Bello Halliru.

    Ya samu nasarar wanda zai tsayawa jam'iyyar takarar kujerar ne bayan ka da ɗan Majalisa mai ci, Bello Relisco a zaɓukan fidda gwani da aka gudanar a bara.

  7. Yan sanda sun daƙile harin masu garkuwa da mutane a Plateau

    Rundunar 'yan sandan jihar Plateau sun ce sun yi nasarar daƙile yunkurin garkuwa da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yakubu Sanda da masu garkuwa suka yi niyyar yi jiya Juma'a.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sandan jihar DSP Alfred Alabo ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne lokacin da Kakakin Majalisar ya dawo gidansa da ke anguwar Federal Low-Cost a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa wasu 'yan bindiga guda uku sun yi niyyar shiga gidansa da ƙarfin tuwo amma sai jami'an tsaro da ke aiki suka taka musu burki.

    Ya ƙara da cewa rundunar tana iyaƙar bakin koƙarinta wajen ganin ta nemo masu garkuwa da suka gudu da kuma kama su.

  8. Hotunan yadda tsananin sanyi ya ɗaiɗaita arewacin Indiya

  9. An tsaurara matakan tsaro a Adamawa gabanin ziyarar shugaba Buhari

    Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, ta girke ƙarin jami'an tsaro domin tabbatar da komai ya tafi daidai gabanin ziyarar shugaba Buhari a jihar.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, shi ya tabbatar wa manema labarai hakan a Yola yau Asabar.

    Ya ce sun bukaci jami'an da su nuna ƙwarewa da kuma mutunta 'yancin dan adam yayin gudanar da aiki.

    Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Buhari zai ziyarci jihar ne a ranar Litinin domin kaddamar da ƴakin neman zaɓen 'yar takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC Sanata Aishatu Binani.

    Kakakin 'yan sandan ya ce ƙarin jami'ai da girke sun haɗar da rundunonin jami'an tsaro da jami'an sashin ƴaki da ta'addanci da kuma motocin samame.

  10. Chelsea ta ɗauki matashin ɗan wasan gaba

    Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan wasan gaba na Ivory Coast David Datro Fofana daga ƙungiyar Molde da ke Norway a kan kuɗin fam miliyan takwas zuwa 10.

    Ɗan wasan mai shekara 20 - wanda kuma ya ci kwallo 24 a wasa 65 da ya buga wa Molde - ya saka hannu kan kwantiragin shekara shida da ƙungiyar ta stamford bridge zuwa shekarar 2029, tare da zaɓin tsawaita kwantiragin.

    Shi ne ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta saya cikin wannan wata na Janairu bayan ɗan wasan bayan Faransa Benoit Badiashile da ta saya daga Monaco kan fam miliyan 35.

    "Ina cike da farin cikin zuwa ƙungiyar da na daɗe ina mafarkinta'' in ji Fofana.

    Chelsea ta bayyana ɗan wasan da cewa ''mai hazaƙar zura in ƙwallaye, kuma ɗaya daga cikin matasan 'yan ƙwallon da suke da makoma mai kyau a nan gaba''.

    Haka kuma ƙungiyar na kan tattaunawa da da Benfica kan ɗaukar matashin ɗan wasan tsakiyar Argentina Enzo Fernandez mai shekara 21, wanda ƙa'idar da ke cikin yarjejeniyar cinikinsa ta kai fam miliyan 106.

  11. Za mu ɗauki masu yi wa ƙasa hidima da ke da buƙata ta musamman aikin zaɓe - INEC

    Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima da ke da lalurar buƙata ta musamman cewa hukumar za ta ɗauke su aikin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

    Farfesa Mahmood ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar kwamishinonin hukumar zuwa shalkwatar masu yi wa ƙasa hidima da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    Ya ce ''INEC hukuma ce da ke bayar da daidaito ta fuskar ɗaukar ma'aikata. Muna buƙatar bai wa 'yan ƙasa dama ba kawai ta jefa ƙuri'a ba, har da aikin zaɓe ba tare da la'akari da yanayin da suke ba, kamar wata lalura ta musamman, za mu ba su dama wajen gudanar da aikin zabe''.

    Shugaban na INEC ya kuma yaba wa hukumar yi wa ƙasa hidimar kan taimakon da take bai wa hukumar zaɓen cikin shekaru masu yawa.

    Daga ƙarshe ya alƙwarta ci gaba da aiki da yarjejeniyar da ke tsakanin hukumarsa da hukumar yi wa ƙasa hidimar, tare da alƙawarta kare lafiyar masu yi wa ƙasa hidimar a lokacin gudanar da zaɓukan ƙasar.

  12. Gwamnatin Kogi ta buƙaci Basaraken jihar ya yi bayani kan rashin halartarsa taron Buhari

    Gwamnatin jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta buƙacin sarkin Ebira Dakta Ado Ibrahim da ya yi ƙarin bayani kan zargin da take yi masa na rashin girmama shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Yahaya Bello.

    Rahotonni na cewa gwamnatin jihar na zargin basaraken da rashin zuwa domin tarbar shugaban ƙasar a lokacin da ya kai ziyara jihar cikin watan Disamban da ya gabata.

    A wata wasiƙa mai ɗauke da san hannun daraktan hukumar kula da masarautun gargajiya a jihar, an buƙaci basaraken da ya yi bayani a rubuce cikin kwana biyu''.

    Haka kuma an buƙaci sarkin da ya bayyana a gaban wani kwamiti da gwamnatin jihar za ta kafa domin ya bayar da bahasin da zai gamsar da kwamitin daga ladabtar da shi''.

    A ranar 29 ga watan Nuwamba ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya halarci jihar domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar Yahaya Bello ya gudanar.

  13. Lafiya Zinariya

    Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon ya duba batun cutar Asma tsakanin yara ƙanana.

  14. Ƙungiyoyi a Sudan ta Kudu na kira da a saki 'yan jaridan da aka tsare kan ɓullar bidiyon shugaban ƙasar yana fitsari a wando

    Ƙungiyoyin kare hakkin 'yan jarida sun yi kira ga hukumomin Sudan ta Kudu ta su saki wasu 'yan jarida shida da suka tsare bayan ɓullar wani faifan bidiyo da ya nuna shugaban ƙasar Salva Kiir na yin fitsari a wando yayin wani taro a ƙasar.

    Ana zargin 'yan jaridar da fitar da bidiyon wanda aka ɗauka a wani taro a da shugaban ya halarta a ƙasar.

    Bidiyon wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta a watan Disamba ya nuna shugaban ƙasar Salva Kiir na yin fitsarin a wondonsa a daidai lokacin da ake sauraron taken ƙasa a wani taron da aka gabatar a ƙasar.

    Daga nan ne kuma aka kama 'yan jaridar shida waɗanda ma'aikatan kafar yaɗa labaran ƙasar ne a wani abu da ya yi kama da yunƙurin gano wanda ya saki bidiyon.

    Ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasar ta yi kira da a saki 'yan jaridar shida.

    A baya-bayan nan ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na yawan kiraye-kiraye ga hukumomin ƙasar da su daina muzgunawa tare da yin barazana ga 'yan jarida a ƙasar.

  15. CBN ya umarci bankuna da su saka sabbin kuɗi a na'urorin ATM

    Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan ƙasar da su daina bayar da sabon kuɗi ga kwastomomin da suka shiga cikin banki domin karɓar kuɗi.

    A maimakon haka babban bankin ya buƙaci bankunan da su saka sabbin kuɗin cikin na'urorinsu na cirar kuɗi na ATM.

    Domin tabbatar da cewa kuɗin ya shiga hannun jama'a gabanin ranar wa'adin 31 ga watan da muke ciki da babban bankin ya saka na daina amfani da tsohon kuɗin.

    Rahotonni sun ce babban bankin ya umarci bankunan da su gaggauta aiwatar da wannan umarni.

    A watan Oktoban da ya gabata ne Babban Bankin Najeriya CBN, ya sanar da matakin sauya fasalin kuɗaɗen ƙasar, tare da umartar mutane da su mayar da tsofaffin kudaɗen banki don sauya musu da sababbi.

  16. Muna buƙatar Buhari ya sa baki kan ƙarin kuɗin makaranta - Kungiyar Dalibai

    Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya NANS ta buƙaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi ''gaggawar sa baki'' game da ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'in ƙasar ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin ƙasar''.

    Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa ''duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari'',

    A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu daga cikin jami'o'in ƙasar suka bayyana ƙarin kuɗin makaranta.

    To sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.

    Dalilin ya da sa kenan suka rubuta wasika ga shugaba ƙasa, inda suka buƙace shi a matsayinsa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya.

    Wasu jami'o'in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun nasu.

    To sai dai ƙungiyar ta ce kundin tarin mulki ya wajabta wa gwamnati samar da ingantaccen ilimi ga 'yan ƙasa, don haka dole ta samar da kuɗin gudanar da ɓangaren ilimi.

    Haka kuma Sakataren na NANS ya ce ''matuƙar ba a soke ƙarin kuɗin makarantar da aka yi ba, to kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na ɗaliban ƙasar ba za su koma makaranta ba, saboda ba za su iya biyan wannan kuɗi ba''.

    Abin da kuma a cewarsa zai ƙara yawaitar masu aikata miyagun laifuka a fadin ƙasar saboda rashin makoma da ɗaliban ke da shi.

    Mista Kankia ya kuma yi gargaɗin cewar ''matukar buƙatarmu ba ta biya ba, to za mu gudanar da gagarumar zanga-zangar da za ta shafi abubuwa da dama a faɗin kasar nan''.

  17. Gane Mini Hanya

    Yayin da ya rage saura 'yan makonni a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, 'yan takarar wannan muƙami na ci gaba da ziyartar jihohin ƙasar daban-daban domin yaƙin neman zaɓe.

    Abokin aikinmu Abdulbaki Jari ya tattauna da ɗan takarar muƙamin shugaban ƙasar a jam'iyyar NNPP Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

    Ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.

  18. Mun yaba da yadda aka fito karɓar katin zaɓe - INEC

    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta bayyana gamsuwarta game da yadda mutane ke fitowa domin karɓar katin zaɓe da hukumar ke rabawa a fadin ƙasar.

    Babban kwamishina a hukumar zaɓen kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri'a, Festu Okoye ne ya bayyana haka a wata zantawa da gidan talbijin na Channels TV.

    Mista Okoye ya dangata fitowar jama'a da yadda shugabanni a matakai daban-daban ke wayar da kan jama'a game da fitowa karɓar katin zaɓen.

    “Yawan ƙarbar katin ya bambanta daga wannan jiha zuwa waccan, kuma muna samun bayanai daga kwamishinoninmu da ke jihohin ƙasar daban-daban'', kamar yadda ya bayyana.

    Haka kuma babban kwamishin a hukumar ya ce hukumar na fuskantar matsaloli game da mutanen da ba su san hanyar za su bi domin karɓar katin nasu ba.

    Ya ce INEC ba za ta buga katin ga mutanen da suka yi rajista fiye da sau ɗaya ba, saboda a cewarsa har yanzu tsoffin katinsu yana aiki.

    Amma ga waɗanda suka sauya wurin gudanar da zaɓe, za su iya samun katinan nasu a wuraren da ake karɓar katin.

  19. Biden ya yaba wa mutanen da suka kare ginin majalisar Amurka

    Shugaba Joe Biden ya yaba wa jama'ar da suka kare ginin majalisar dokokin ƙasar daga taɓargazar masu zanga-zanga da suka yi ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

    Yayin da aka cika shekara biyu da faruwar mummunan harin, Mista Biden ya ce tarihi zai ci gaba da tunawa da sunaye da jajircewar mutanen da suka bugi ƙirji wajen kare dimokraɗiyyar Amurka.

    A wani biki da aka yi a Fadar White House, Mista Biden ya karrama mutum 14, wasu a cikinsu sun mutu - waɗanda suka yi fito-na-fito da mutanen da suka afka wa majalisar dokokin ƙasar.

  20. Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu maza biyu

    Iran ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu maza biyu saboda zarginsu da kashe wani jami'in tsaro yayin zanga-zangar gama-garin da aka shafe sama da wata uku ana yi a ƙasar.

    Mahukunta a ɓangaren shari'a sun bayyana sunan mutanen da Mehdi Karami mai shekara 22 da Seyyed Mohd Hosseini, mai shekara 20.

    Dukkansu dai an same su ne da hannu a mutuwar jami'in tsaron sa kan a birnin Karaj kusa da Tehran.