Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mutum goma sun rasu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mutum 15 sun mutu a hatsarin mota a Kogi

    Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗura ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 15, wasu mutum biyar kuma suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya auku a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar (NAN) ya ruwaito cewa hatsarin ya auku ne bayan da wata motar fasinja ƙirar J-5 da wata tankar mai suka yi taho mu gama a garin Koton-Karfe da ke kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja da safiyar ranar Talata.

    Babban kwamandan Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura mai lura da jihar Stephen Dawulung, ya ce tuni aka kai wadanda suka samu raunukan asibiti domin ba su kulawar gaggawa.

    Mista Dawulung ya ce saɓa dokokin hanya da direban motar fasinjan ya yi ne ya haddasa aukuwar hatsarin.

  2. Majalisar wakilan Amurka ta kasa zaɓen shugaba bayan yunƙuri uku

    Majalisar Wakilan Amurka ta ɗage zamanta cikin yamutsi bayan yunƙurin da ta yi har uku na zaɓen Kevin McCarthy na jam'iyyar Republican a matsayin shugaba, ya ci-tura.

    Wannan shi ne karon farko a ƙarni ɗaya da aka kasa zaɓen a ƙuri'ar farko.

    Dan majalisa McCarthy, daga California, ya kasa samun rinjayen yawan kuri'un da ake bukata, 218, bayan da 'yan majalisa 28 na jam'iyyarsa ta Republican suka juya masa baya, inda suka gwammace su zaɓi Jim Jordan a maimakonsa.

    Sai dai duk da haka Mista McCarthy ya ce zai ci gaba da takarar har sai ya yi nasara.

    A baya shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar, saboda haka ake sa ran ya zama kakakin a yanzu bayan da 'yan Republican ɗin suka karɓe rinjaye da majalisar a zaɓen rabin wa'adi na watan Nuwamba.

    Amma kuma idan aka ci gaba da rigima a takarar, to hakan zai tilasta wa 'yan majalisar su nemi wani ɗan takarar daban.

    Tasirin wannan koma bayan shi ne babu wani aiki da majalisar za ta iya gabatarwa har sai ta naɗa kakakinta.

    A majalisar dattawan ƙasar kuma, 'yan jam'iyyar Democrat mai mulkin ƙasar ke da rinjaye, abin da ke nufin ba lalle ne mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta ci gaba da kaɗa kuri'arta ba a duk lokacin da wani batu da ke gaban majalisar ya gamu da cikas.

    Saboda a yanzu 'yan Democrat ɗin na da ƙarin ƙuri'a guda da suka samu a zaɓen watan Nuwamba da aka yi a faɗin ƙasar.

  3. Assalmu alaikum

    Masu bibiyar a wannan shafi,Abdullahi Bello Diginzake muku barka da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Ku kasance da mu a wannan shafi don kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuma kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu