Hukumar hana sha da
fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta tabbatar da cewa ruwan A-Kurkura yana
dauke da sinadarin tabar wiwi a cikinsa daga binciken farko da suka gudanar.
Wannan na zuwa ne bayan da NDLEA din ta kai samfurin A-kurkuran, wani kayan maye
da ke tashe zuwa dakin gwaje-gwajenta don tantance irin illar da yake yiwa masu
ta'ammali da shi a kimiyyance.
Haka kuma hukumar ta ce ta gano gonakin da ake
noma tabar wiwi a jihar Kano tare da lalatasu.
Hukumar ta NDLEA ta kama nau’i
daban-daban na miyagun haramtattun magungunan maye a shekarar da muke bankwana
da ita, har kusan ton tara a jihar Kano ciki har da dubban kwalaben A-kurkura
da karin wasu miyagun kwayoyi da aka yi niyyar safararsu zuwa wasu jihohin
arewacin Najeriya.
Kwamadan NDLEA a Kano, Abubakar Idris Ahmad yace sun bi
sawu har birnin Badun inda suka kama mutumin da ke yin A-Kuraran tare da
gurfanar da shi a gaban kotu a jihar Kano.
Kazalika yace sun kama karin wasu
ababen kayan mayen da mutanen da suke safararsu wadanda suke fuskantar shari’a
a yanzu.
Hukumar ta NDLEA ta ce ta gano
wasu gonakin da ake noma tabar wiwi biyar a kananan hukumomin Dawakin Kudu da
Bichi da Danbatta da Gwarzo da kuma Nasarawa, wadanda tace tuni an lalatasu
sannan aka kama mutanen da suke aikin.
Jihar Kano dai na sahun
gaba-gaba a Najeriya, game da matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi, kuma
hukumar NDLEA tace cikin kusan mutum dubu biyu da ta kama maza da mata, fiye da
mutum dubu daya ana mayar da su cikin hayyacinsu da basu shawarwari.