An ƙi bayar da gawar wani mutum a asibiti kan zargin 'yan uwansa da dukan likita
Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
Rufewa, Daga Badriyya Tijjani Kalarawi
Asalin hoton, kalarawi84
Ana muka kawo karshen shafin da ke kawo muku bayanai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kasashen makofta har da wasu kasahen duniya.
Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa da wasu labarai da rahotannin, kafin zuwan lokacin za ku iya ziyartar shafinmu na intanet bbchausa.com, domin karanta wasu karin labaran.
Za ku iya zuwa shafukan mu na sada zumunta da muhawara na BBCHausa facebook, da Twitter da Instagram, da shafinmu na Youtube domin kallon bidiyo iri daban-daban.
Amma yanzu, Badriyya Tijjani Kalarawi ke muku fatan alkhairi daga nan sashen Hausa na BBC.
Mu kwana lafiya.
Binciken NDLEA ya gano akwai tabar wiwi a cikin maganin maye na A-kurkura
Asalin hoton, NDLEA
Hukumar hana sha da
fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta tabbatar da cewa ruwan A-Kurkura yana
dauke da sinadarin tabar wiwi a cikinsa daga binciken farko da suka gudanar.
Wannan na zuwa ne bayan da NDLEA din ta kai samfurin A-kurkuran, wani kayan maye
da ke tashe zuwa dakin gwaje-gwajenta don tantance irin illar da yake yiwa masu
ta'ammali da shi a kimiyyance.
Haka kuma hukumar ta ce ta gano gonakin da ake
noma tabar wiwi a jihar Kano tare da lalatasu.
Hukumar ta NDLEA ta kama nau’i
daban-daban na miyagun haramtattun magungunan maye a shekarar da muke bankwana
da ita, har kusan ton tara a jihar Kano ciki har da dubban kwalaben A-kurkura
da karin wasu miyagun kwayoyi da aka yi niyyar safararsu zuwa wasu jihohin
arewacin Najeriya.
Kwamadan NDLEA a Kano, Abubakar Idris Ahmad yace sun bi
sawu har birnin Badun inda suka kama mutumin da ke yin A-Kuraran tare da
gurfanar da shi a gaban kotu a jihar Kano.
Kazalika yace sun kama karin wasu
ababen kayan mayen da mutanen da suke safararsu wadanda suke fuskantar shari’a
a yanzu.
Hukumar ta NDLEA ta ce ta gano
wasu gonakin da ake noma tabar wiwi biyar a kananan hukumomin Dawakin Kudu da
Bichi da Danbatta da Gwarzo da kuma Nasarawa, wadanda tace tuni an lalatasu
sannan aka kama mutanen da suke aikin.
Jihar Kano dai na sahun
gaba-gaba a Najeriya, game da matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi, kuma
hukumar NDLEA tace cikin kusan mutum dubu biyu da ta kama maza da mata, fiye da
mutum dubu daya ana mayar da su cikin hayyacinsu da basu shawarwari.
Sojojin Ivory Coast na gab da sanin makomarsu a shari'ar Mali
Asalin hoton, AFP
Wasu sojojin Ivory Coast 46 na shirin sanin ko za a ba su damar komawa gida, yayin da wata kotu a Mali ke shirin yanke musu hukunci bayan shafe watanni a tsare.
An kama su ne a watan Yuli a lokacin da suka isa filin jirgin saman Bamako kuma gwamnatin sojan Mali ta zarge su da zama sojojin haya.
Hukumomin Ivory Coast sun ce an tura su ne domin bayar da tallafi ga tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Mali.
Shugabannin kasashen yammacin Afirka sun yi kira da a sako sojojin kafin karshen watan Disamba.
Ana dai gudanar da shari'ar ne a bayan fage da kuma sanya ido sosai daga jami'an tsaro.
Tsohon Fafaroma Benedict na samun sauki in ji Fadar Vatican
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Fafaroma Francis lokacin da ya je duba Fafaroma Benedict lokacin rashin lafiyarsa
A ranar Laraba ne Fafaroma Francis ya yi gargadi kan halin rashin lafiyar da tsohon Fafaroma Francis mai shekara 95 ke ciki, tare da neman su taya shi da addu'ar samun sauki.
Sai dai ranar Alhamis, Fadar Vatican ta sanar da cewa Fafaroman ya samu afuwa har da yin bacci a daren jiya Laraba.
A shekarar 2013 ne Fafaroma Bendict ya sauka daga mukamin jagorancin cocin roman Katolika, kuma shi ne na farko da ya taba yin hakan cikin shekaru 600.
A wancan lokacin ya sanar da saukar ne saboda halin rashin lafiya da yawan shekaru. Lokacin da aka zabe shi a matsayin jagoran Vatican ya na da shekara 78 ne kuma ana girmama shi ba kadan ba a wan can lokacin sakmakaon dabbaka darikar da daukaka darajar fadar.
Sunan shi na ainahi Joseph Ratzinger, kuma shi ne Fafaroma Bajamushe na farko cikin shekara 1,000, sai dai cikin shekaru 8 aka sanar da halin tabarbarewar rashin lafiyarshi ba za ta bari ya yi tsahon lokaci kan jagorantar cocin Roman katolika ba.
An yankewa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kisan matar Babansa
Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta yankewa wani matashi mai suna Sagiru Abdullahi mai shekara 29 hukuncin kisa ta hanyar rataya, sakamakon samunsa da kisan matar Babansa.
Solacebase ta rawaito cewa, Sagiru ya kashe Zainab Dan azumi mai shekara 55 ta hanyar sassara ta da adda. Tun da fari kotun ta samu Sagiru mazaunin unguwar Kurmawa da laifin kisan kai.
Mai shari'a Aisha Mahmoud, ta ce dukkan bincike da shaidu sun tabbatar wanda ake zargin ya aikata laifin dan haka aka yanke masa hukuncin kisa.
Mai shigar da kara na gwamnati Tijjani Ibraim, ya shaidawa kotu cewa Abdullahi ya aikata kisan ne tun a watan Yunin 2014, a unguwar Kurmawa da ke tsakiyar birnin Kano.
Mista Tijjani ya ce Abdullahi ya sassara matar babanshi da adda a wurare daban-daban har sai da ya kai ta kasa, kuma a daren da abin ya faru ta rasu a babban asibitin Murtala Muhammad da ke kanon, daga bisani rai ya yi halin sa.
'Yan sanda 10,000 da aka yaye za su yi aiki lokacin zaben Najeriya na 2023
Sufeton 'yan sandan Najeriya ya sanar da cewa, sabbin kwasitabul din 'yan sanda da aka yaye kwanakin nan, da suka kai 10,000 za a ba za u a sassan kasar ldomin tabbatar da doka da oda lokacin zaben shekarar 2023 da ke tafe.
Jaridar intanet ta Solacebase, ta ambato mataimakin sufeton 'yan sandan shiyya ta 8, Ashafa Adekunle, wanda ya wakilci babban sufeton 'yan sandan Najeriyar, IGP Usman Alkali Baba, na bayyana haka a wurin bikin yaye daliban makarantar horon 'yan sandan da ke Ilori.
''Mu na shaida muku bayan faretin kammala horas da sabbin 'yan sanda, za a baza su a sassan Najeriya lokacin zabukan da ke tafe na shekarar 2023. Za su yi aikin tabbatar da tsaro domin a gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da luma,'' in ji Adekunle.
Ya yin da babban zaben Najeriyar ke kara karatowa, ana nuna damuwa kan sha'anin tsaro da ke kara tabarbarewa a wasu sassan kasar musamman arewacin Najeriya da ake fama da barayin daji da masu satar mutane domin kudin fansa.
Jami'an diplomasiyya sun isa yankin Tigray
Asalin hoton, AFP
Masu shiga tsakani da jami'an diplomasiyya
daga akalla ƙasashe 30 sun isa babban birnin yankin Tigray.
Wannan dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙasa
da ƙasa wajen ganin an cimma zaman lafiya mai ɗorewa a yankin, bayan
yarjejeniyar da aka cimma ta kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe shekaru biyu ana
gwabzawa.
Jiya Laraba an ga wasu hotuna na ban sha'awa
da ke nuna yadda jirgin fasinja na farko da ya sauka a babban birnin yankin
Mekelle, cikin shekara ɗaya da rabi.
A ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiyar dai
ana sa ran mayakan na Tigray za su jingine makamansu.
To sai dai masu aiko da rahotanni na cewa
ganin dakarun Eritiriya da 'yan sa-kai daga Amhara a yankin na iya kawo
tasgaro ga yarjejeniyar zaman lafiyar.
Gwamnan Legas ya gana da sifeton 'yan sanda kan kisan lauya
Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya gana da gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu a shelkwatar hukumar 'yan sandan ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar, domin tattauna wasu batutuwa ciki har da batun yin adalci ga lauyar nan da wani jami'an ɗan sanda ya harbe a birnin Legas ranar Kirsimeti.
A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar mai dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar ya ce babban sifeton 'yan sandan, ya jadda cewa za a gudanar da cikakken bincike tare da alƙawarin yin adalci game da batun, yana mai cewa hukumar na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ofishin babban lauyan gwamnatin jihar Legas domin tabbatar da an gurfanar da wanda ke da hannu a gaban kotu.
A nasa ɓangare gwamnan jihar Legas ɗin ya alkawarta taimaka wa rundunar 'yan sandan domin ganin cewa an yi adalci game da binciken kisan lauyar.
Tuni dai babban Sifeton 'yan Sandan ƙasar ya bayar da umarnin dakatar da jami'in ɗan sandan da ya harbe tare da kashe lauyar mai suna Omobolanle Raheem a birnin Legas.
Mutum takwas sun mutu a rikicin ƙabilanci a Sudan
Asalin hoton, AFP
Jami'an agaji a yankin Darfur na ƙasar Sudan
sun ce akalla mutane takwas ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke a cikin dare tsakanin
wasu al'ummomin da ke zaman doya da manja.
Da farko dai an fara harbe-harbe ne a garin
Zalingei, daga bisani 'yan kabilar Rizeigat ta Larabawa, da suka kai hari wani
sansanin 'yan gudun hijira na 'yan kabilar Fur, a kan babura.
Ɓarkewar tashe-tashen hankula sun karu tun
bayan janyewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a
bara.
Har yanzu dai yankin na Darfur bai farfaɗo
ba daga yaƙin da ya sha fama da shi tun kusan shekaru ashirin da suka gabata,
wanda ya raba sama da mutane miliyan biyu da gidajensu.
Ana zargin da sa hannun wasu mayakan sa kai
da ke samun goyon bayan gwamnati a wasu hare-haren da ake kaiwa.
Makami mai linzamin Ukraine ya faɗa cikin ƙasar Belarus
Rahotanni daga ƙasar Belarus na cewa wani
makami mai linzami na ƙasar Ukraine ya faɗa cikin yankin ƙasar.
Ma'aikatar tsaro a Belarus ta ce tana
gudanar da bincike kan ko na'urorin tsaronta ne suka kakkaɓo makamin nau'in
S-300, ko kuma hari ne aka kai kasar.
Kawo yanzu dai hukumomi a Ukraine ba su ce komai game da lamarin.
Tun da farko mai magana da yawun sojojin Ukraine Oleksii Gromov ya ce
harin da Moscow ta kai na yau ya haɗa da makamai masu linzami akalla 64, ciki har da kirar S-300 ɗin.
Ɗaliban jami'o'i a Ghana sun koka kan ƙarin kuɗin makaranta
Ɗaliban jami'o'i a ƙasar Ghana sun yi watsi da ƙarin kuɗin makaranta da wasu jami'o'in ƙasar suka yi.
Ƙungiyar Daliban ƙasar ta umarci masu ruwa da tsaki da su hana jami'o'in ƙasar ƙara kuɗin makarantar.
A baya-bayan nan ne dai Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ƙarin kashi 15 cikin 100 na kuɗin makaranta ga jami'o'in ƙasar.
To sai dai ɗaliban na cewa wasu jami'o'in sun yi ƙarin kusan kashi 40 cikin 100, saɓanin abin da majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi.
Daliban sun bayyana damuwarsu game da lamarin, yayin da ƙasar ke fama da tsadar rayuwa, da ƙaruwar farashin kayyaki da kusan kashi 50 cikin 100.
Ƙungiyoyin ɗaliban ƙasar sun ce ƙarin kuɗin zai jefa dalibai da iyayensu cikin mawuyacin hali.
Rwanda ta ce jiragen yaƙin DR Kongo sun ratsa sararin samaniyarta
Asalin hoton, SCOTT OLSON
Gwamnatin Rwanda ta ce jiragen yaƙin DR Kongo sun ratsa sararin samaniyarta yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar tashin hankali tsakanin maƙwabtan ƙasashen biyu kan ayyukan 'yan tayar da ƙayar baya a gabashin DR Kongo.
A wata sanarwa da gwamnatin Rwanda ta fitar ta ce ''jirgin yaƙin DR Kongo ya saɓa wa sararin samaniyar ƙasarmu inda ya yi shawagi ta ɓangaren tafkin lardin Kivu da ke yammacin ƙasarmu''.
To sai dai daga bi-sani jirgin ya koma DR Kongo kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ko a watan da ya gabata ma dai wani jirgin yakin DR Kongo marar ɗauke da makamai ya sauka a filin jirgin Rwanda a kusa da kan iyakar ƙasar, a wani abu da DR Kongo ta bayyana da cewa hatsari ne.
Rwanda dai ta ce wannan saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ƙulla a ƙasashen Angola da Kenya.
DR Kongo dai na ci gaba da zargin Rwanda da taimaka wa 'yan tawayen M23, zargin da Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka da Fransa da Belgium ke goyon baya.
Zargin da ita kuma Rwandan ta sha musantawa a lokuta da dama.
An ƙi bayar da gawar wani mutum a asibiti kan zargin 'yan uwansa da dukan likita
Asalin hoton, others
Hukumomin asibitin koyarwa da ke Ilorin a jihar Kwara ta tsakiyar Najeriya sun ƙi bayar da gawar wani mutum da ya mutu tare da kama ɗaya daga cikin 'yan uwan mamacin bisa zargin lakaɗa wa wani likitan asibitin duka.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa uku daga cikin 'yan uwan mamacin mai suna Alhaji Saliu ne suka doki wani likita a sashen kula da masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin.
Saboda abin da suka kira 'rashin kula' da lilitocin suka nuna musu lamarin da a cewarsu ya sa ɗan uwan nasu ya mutu.
Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan rasuwar ɗan uwan nasu wanda ke fama da cutar sankarar jini.
Ɗaya daga cikin 'yan uwan mamacin ya ce asibitin ya hana su gawar mamacin saboda faruwar lamarin.
Ya ƙara da cewa sun kai ɗan uwan nasu sashen kula da masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin wajen ƙarfe biyar na asubahin ranar Talata, kuma babu likitan da ya zo kan ɗan uwan nasu duk kuwa da irin roƙon da suka riƙa yi wa likitocin.
Shugabar ƙungiyar likitoci reshen asibitin Mrs Mrs. Elizabeth Ajiboye ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ''gamayyar ƙungiyar likitoci ta ƙasar ne suka umarci hukumomin asibitin da kada su bayar da gawar mamacin har sai an kama tare da gurfanar da mutanen da suka daki likitan a gaban kotu''.
Daga ƙarshe ta shawarci al'umma da su guji ɗabi'ar cin zarafin ma'aikatan lafiya.
Buhari ya miƙa ta'aziyya kan rasuwar shugaban ƙungiyar Ohaneze
Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga iyalan shugaban ƙungiyar al'ummar Ibo ta Ohaneze kan mutuwar jagoran ƙungiyar Farfesa George Obiozor.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar, shugaba Buhari ya ce ya 'kaɗu matuƙa' da jin labarin rasuwar mista Obiozor.
Shugaban ya kuma jajanta wa iyalan marigayin da gwamnati da al'umar jihar Imo tare da ƙungiyar da kuma al'ummar Ibo 'yan Najeriya da mazauna ƙasashen ƙetare.
Buhari ya bayyana mutuwar jagoran ƙungiyar ta Ohaneze da cewa babban rashi ne ga ƙasar, yana mai cewa ƙasar ba za ta taɓa manta irin gudunmowar da ya bai wa ƙasar ba.
Mista Obiozor dai ya taɓa riƙe muƙaman jakadan Najeriya a ƙasashen Amurka da Cyprus da Isr'ila da kuma muƙamin babban darakta a cibiyar kula da al'amuran ƙasashen waje ta Najeriya (NIIA).
Rasha na luguden makamai masu linzami ta sama da ta ruwa zuwa Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da fitar da gargaɗin hare-hare ta sama a faɗin Ukraine a yayin da Rasha ke luguden makamai masu linzami zuwa wasu manyan biranen ƙasar.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara Mykhailo Podolyak ya ce fiye da makamai masu linzami 120 ne Rashar ta harba kan gine-ginen fararen hula.
Magajin garin birnin Kyiv ya ce akalla mutum uku ne ciki har da wata yarinya mai shekara 14 aka kai asibiti bayan wata fashewa a birnin
Haka kuma an ji ƙarar abubuwan fashewa a biranen Kharkiv da Odesa da Lviv da kuma birnin Zhytomyr.
Gwamnan lardin Odesa da ke kudancin ƙasar ya ce an samu ƙaruwar sabbin hare-haren makamai masu linzami a faɗin Ukraine.
Rundunar sojin saman Ukraine ta ce ƙasar Rasha na kai wa Ukraine farmaki da makamai masu linzami daga ɓangarori daban-daban ta sama da ta ruwa.
Haka kuma rahotonni sun ce rasha na amfani da jirage marasa matuƙa masu yawa domin kai hare-haren.
A ranar Alhamis da safe an yi ta jin ƙararrawar gargaɗin hari ta sama a duka yankunan ƙasar.
Mai bai wa shugaban kasar shawara Oleksiy Arestovych ya umarci fararen hula a kasar da su nemi mafaka, yayin da dakarun sojin saman ke bakin ƙoƙarinsu.
Buhari ya amince da sayo motoci masu sulke 400 don kare Abuja da Nasarawa da Niger
Asalin hoton, Shuttestock
Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya amince da sayo motocin yaƙi masu sulki 400 ga dakarun soji, domin kare babban birnin ƙasar Abuja da jihar Nasarawa da wasu yankuna na jihar Niger.
Sabon babban kwamandan rundunar soji mai lura da yankin Manjo Janar Mohammed Usman,ne ya bayyana haka ranar Laraba a cikin jawabin godiya da ya gabatar jim kaɗan bayan shugaba Buhari ya yi masa ƙarin girma.
Manjo Janar Usman ya gode wa shugaban ƙasar saboda jajircewarsa da taimakon da ya ke bai wa rundunar, ciki har da amincewa da sayo motocin sulken 400, waɗanda ya ce sun isa wajen kare yankinsa da ya ƙunshi babban birnin ƙasar, da jihar Nasarawa da kuma wasu yankunan jihar Niger.
Haka kuma ya bayyana jin daɗinsa game da ƙarin girman da aka yi masa, yana mai cewa hakan zai taimaka masa wajen gudanar da aikinsa.
Za a gurfanar da sojojin Ivory Coast da aka tsare a Mali a gaba kotu
Asalin hoton, Reuters
A yau ne za a fara shari'ar sojojin Ivory Coast 46 da aka tsare a ƙasar Mali tun a watan Yuli a gaban kutun ɗaukaka ƙara da ke Bamako babban birnin ƙasar.
Shari'ar sojojin na zuwa ne mako guda bayan ƙasashen biyu sun amince da warware batun ta hanyar masalaha a wani tattaunawa da ƙasar Togo ke shiga tsakani.
An tsare sojojin ne dai bayan da suka isa Mali domin yin aiki da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar.
Mali dai ta zargi sojojin da yunƙurin dagula zaman lafiya da tsaron ƙasar, zargin da Ivory Coast din ta sha musantawa.
A ranar huɗu ga watan Disamba ne kuma ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta umarci shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita da ya saki sojojin kafin ƙarshen shekarar da muke ciki.
'Yan sanda sun kama kwamandan IPOB da ya jagorancin kisan Ahmed Gulak
Asalin hoton, others
Rundunar 'yan sandan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta yi holen wani kwamandan IPOB da ta daɗe tana nema ruwa a jallo mai suna Chinwendu Nwangwu wanda aka fi sani da Onyearmy bayan da ta samu nasarar kama shi.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Michael Abattam, ya ce an kama mista Nwaagwu wanda ya bar aiki a rundunar sojin Najeriya shekara takwas da suka gabata a yankin ƙaramar hukumar Aboh Mbaise da ke jihar.
Mista Abattam ya ce tsohon sojan mai shekara 34 ya aikata laifuka da dama ciki har da kashe-kashen mutane, da kai hare-hare ofisoshin zaɓe a jihar.
Rundunar 'yan sanadn jihar ta ce bayan da ta binciki gidansa ta samu bindigogi biyar, da wasu manyan bindigogin, da ƙananan bindigogi ƙirar gida, da gidan alburusai 50, da gurneti tara ƙirar gida.
Haka kuma mista Nwangwu ya amsa laifin bai wa jami'an ƙungiyar 'yan aware da ESN kusan 1,000 horon makamai da dabarun harin ta'addanci.
Sannan kuma mista Onyearmy ya amince cewa ya jagoranci hare-hare da dama a jihar musamman kan jami'an tsaro da ofisoshin 'yan sanda da na hukumar zaɓe a jihar.
Ya kuma bayyana yadda ya shirya harin da ya yi sanadin mutuwar Ahmed Gulak, mai bai wa tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan kan harkokin siyasa.
Assalamu alaikum
Masu bibiyarmu a wannan shafi Abdullahi Bello Diginza ke muku barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.
Ku kasance tare da mu domin sanin halin da duniya ke ciki, ta hanyar kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta wato BBCHausa Facebook, da Twitter da Instagram, ko shafinmu na Youtube dan kallan bidiyoyi masu ƙayatarwa.