Taliban ta kama matan da ke zanga-zanga kan hana mata zuwa jami'a

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Khalifa Dokaji and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. An yi taron tunawa da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya mai littattafan Tatsuniyoyi da Wasanni, Daga Zahraddeen Lawan a Kano

    Nahalarta taro
    Bayanan hoto, An shirya taron ne domin baje kolin gudummawar da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya ya ba da a bunkasa Harshen Hausa.
    Farfesa Yakubu Magaji Azare a zauren taron tunawa da marigayi Farfesa Ibrahim Yaron Yahaya
    Bayanan hoto, Littafan Tatsuniyoyi da Wasanni na daga cikin wadanda Farfesa Yaro ya rubuta, da ake amfani da su a matakin makarantun Firamare da Sakandare

    Yayin da mashahurin marubucin littattafan hausa nan ya cika shekaru 27 da rasuwa, cibiyar binciken harsunan Najeriya da fassara da hikimomin al'umma ta Jami'ar Bayero Kano, ta gudanar da lakcar tuna wa da gagarumar gudummawar da ya bayar wajen bunkasa harshen Hausa.

    Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya ya rubuta litattafan Hausa masu yawa wadanda suka taimaka wajen bunkasa koyo da koyarwa a makarantu.

    An gabatar da lakca, mai taken “Halaye da Dabi’u A Cikin Tatsuniyoyin Hausa” don tunawa da babban malami kuma jagora Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, wanda ya rasu shekaru 27 da suka gabata.

    Farfesa Yakubu Azare wanda shi ne shugaban cibiyar binciken harsunan Najeriya jami'ar Bayero Kano da ya shirya lakcar.

    Yace ''manufar wannan taron ita ce daga daraja da martaba da kimair marigayi, hakika ya ba da kyakkyawar gudummawa da hidimarsa ta fannin ilimi.

    "Dalilin da ya sanya muka ga ya kamata duniya ta san abubuwan da ya yi, wanda har yanzu al'umma ke ci gaba da mora ta fanno ni da dama musamman bangaren bunkasa ilimi da harshen hausa,'' in ji Farfesa Yakubu Azare.

    Farfesa Lawan Dan Ladi Yalwa na tsangayar koyar da harsuna na daga cikin mahalarta taron, kuma ya gabatar da jawabi game da marifgayi Ibrahim Yaro Yahaya.

    ''An shirya taron lakcar, don ta zamo darasi ga ƴan baya su ji hikimomi da bajintar da babban malamin ya yi wajen bunkasa harshen Hausa, sannan su fadakar tare da koyon darusa.

    "Hakika ya ba da gudummawa wajen bunkasa Adabi da Nahawu da sauransu.''

    Marigayin ya rubuta littatafai har 16 ciki har da bayani kan adabi da al'ada da nahawu, sannan shi ne mutumin da ya fassara littafin dare sha biyu, wadanda suka zama jagora wajen kyautata harshen Hausa da bunkasa ilimi.

    Ya kuma riki mahimman mukamai a Jami'ar Bayero Kano ciki har da mataimakin shugaban jami'ar.

    Manyan malaman Hausa a dakin taron
  2. Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranakun hutun Kirsimati da sabuwar shekara

    Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola

    Asalin hoton, @MINOFINTERIORNG

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 26 ga wata da ranar Talata 27 ga watan Disamba a matsayin ranar hutun bikin Kirsimati a fadin kasar.

    Sanarwar da ma'aikatar cikin gida ta fitar dauke da sa hannun minista Ogbeni Rauf Aregbesola a madadin gwamnatin kasar, ta ce ranar Litinin 2 ga watan Junairun 2023 ne ya kama ranar hutun sabuwar shekara.

    Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya mabiya addinin Kirista a daukacin Najeriya murnar bikin Kirsimati da suke gudanarwa duka shekara, domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa AS.

    Ya bukaci su yi koyi da kyawawan halayaensa da littafin Bibble ya sanar da suka hada da hakuri, da kyautatawa da koyarwa da taimako da sauransu.

    Ogbeni Rauf Aregbesola ya tunatar da daukacin 'yan Najeriya da ke shirin bikin sabuwar shekara, cewa shekarar 2023 ne za a yi babban zaben kasar, don haka su zama cikin shirin kada kuri'a da zaban shugaban da ya cancanci tsamo kasar daga matsin tattalin arziki da inganta da tsaro da ilimi da lafiya.

  3. An kama sojan saman Gambia da hannu a kitsa juyin mulki

    Adama Barrow

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Adama Barrow ya yi nasara a zaben da aka gudanar a shekarar 2016 a Gambia, amma dakyar Yahya Jammeh ya amince da shan kaye

    Gwamnatin Gambia ta sanar da kama wani sojan ruwa da ake zargi da hannu a juyin mulkin da bai yi nasara ba a karshen mako.

    Sanarwar da ta fito daga fadar gwamnati na cewa ana tsare da Lance Corporal Sanna Fadera, tare da wasu jami'an tsaro hudu a wani samame da aka kai ranar Talata.

    Tuni kungiyar Tarayyar Afirka da jam'iyyun adawa a Gambia sukai allawadai da yunkurin juyin mulkin.

    Sai dai wani tsohon jami'in soja ya ce ya na kyautata zaton batun bai wani taka kara ya karya ba. Sanarwar gwamnatin Gambia ta ce amintattun dakaru sun bazama neman wadanda suka taimaka wajen kitsa juyin mulkin, bayan kama jami'an soji da na 'yan sanda da masu gadin fadar shugaban kasa.

    Lamura sun koma daidai a Banjul babban birnin Gambia, tun bayan gwamnati ta baza matakan tsaro domin tabbatar da doka da oda a ranar Laraba.

    A bangare guda kungiyar ECOWAS ta ce ta na tare da shugaba Adama Barrow a wannan lokaci da hankula suke a tashe.

  4. Shugaba Buhari ya yi alkawarin inganta rayuwar 'yan sandan Najeriya

    Shugaba Buhari na Najeriya

    Asalin hoton, STATEHOUSE

    Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta inganta aiki da rayuwar 'yan sandan Najeriya.

    Sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya karbi rahoto kan rundunar 'yan sandan kasar na shekarar 2021, da karbar kudurin kasafin kudin 'yan sanda na badi.

    Sanarwar ta ci ambato shugaba Buhari na cewa: “wannan gwamnatin ta sanya walwala da inganta aikin 'yan sanda a sahun gaba, kuma hakkinta ne ta kawo sauye-sauye masu inganci a aikinsu.

    Ni da kai na na amince muhallin da 'yan sanda ke zaune a ciki ba mai inganci ba ne, dan haka gwamnatinmu ta kuduri aniyar sauya musu ingantacciyar rayuwa, ba su kadai ba har da sojojin Najeriya,'' in ji shugaba Buhari.

    Ya kara da da cewa ya san duk lokutan da aka yi wa jami'an tsaro sauyin wurin aiki, ba za su yi dar ba wajen zuwa aikin, saboda sanin sun bar iyalansu cikin ingantaccen muhalli da tsaro a bariki, yara na zuwa makaranta mai kyau, ga asibitoci masu inganci, wannan zai kara musu kwarin gwiwar gudanar da aikinsu yadda ya dace.

    Batun karawa 'yan sanda albashi da walwala ya dade ana tattaunawa a kai a Najeriya, rashin samun albashi da alawus mai tsoka na daga cikin dalilan da ake cewa ya janyo kananan 'yan sanda karbar na goro.

  5. Imran Khan na barazanar rusa majalisun mazabarsa a Pakistan

    Imran Khan

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Mista Khan shi ne Firaiministan Pakistan na farko da aka kada kuri'ar yanke kauna da mulkinsa

    Tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan, ya yi barazanar wargaza majalisu biyu na wata gunduma a wani mataki na matsawa gwamnati gudanar da zabe nan kurkusa.

    Mataki irin wannan da ya dauka a mazabar shi ta Punjab da Khyber Pakhtunkhwa, ya janyo daukar matakin gaggauta yin zaben da aka shirya gudanarwa a watan Disamba yin shi da gaggawa.

    "Duk matakin da suke dauka na rikitar da siyasarmu da rashin zaman lafiya a Pakistan a dan tsakanin nan, ba a taba ganin hakan ta faru a kasarmu ba,'' in ji Madiha Afzal, wata da ke aiki a cibiyar tink tank mai mazauni a Amirka, kuma mawallafiyar littafin Under Siege: Extremism, Society and the State.

    Wannan barazana ta Mista Khan' ta tada kura a kasar wadda ke fadi tashi kan matsin tattalin arziki, da rikicin siyasa a wani lokaci da ake ganin da kamar wuya daidaituwar lamura nan kusa.

  6. Taliban ta kama matan da ke zanga-zanga kan hana mata zuwa jami'a

    Mata masu zanga-zanga a Afghanistan

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Taliban ta kama mata biyar da suka shiga zanga-zanga a birnin Kabul, kan haramtawa matan kasar karatun jami’a.

    An kuma cafke wasu ‘yan jarida uku a wurin zanga-zangar. Rahotanni sun ce ana ci gaba da zanga-zangar a wasu sassan kasar ciki har da gundumar Takhar.

    A ranar Laraba, masu gadin jami’o’in Afghanistan sun hana dalibai mata shiga harabar, kwana guda bayan gwamnatin Taliban ta sanar da matakin.

    Wanna dai shi ne daya daga cikin tsauraran matakan da Taliban ta dauka a Afghanistan bayan karbe jagorancin kasar a shekarar da ta gabata.

    Tuni daman Taliban ta dauki matakin hana yara mata zuwa makarantun sakandare.

  7. An gano gawar wani mutum a karkashin jirgin sama

    Filin jirgin sama na Gatwick

    Asalin hoton, Gatwick airport

    Bayanan hoto, 'Yan sanda Sussex sun ce ana gudanar da bincike kan lamarin

    An gano gawar wani mutum a karkashin wurin ajiyar kayayyaki da ke jirgin sama a filin jirgin sama da ke Gatwick.

    Jirgin Tui ya taso ne daga kasar Banjul babban birnin kasar Gambia, zuwa filin jirgin da ke yammacin Sussex.

    ‘Yan sanda sun ce tun ranar 7 ga watan da muke ciki aka gano gawar mutumin da misalin karfe 4 na yamma agogon GMT.

    Mai magana da yawun hukumar filin jirgin Gatwick ya bayyana cewa lamarin mai tada hankali ne, su na mika ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwan mutumin.

    ‘Za mu tabbatar an an gudanar da binciken da ya dace, zamu yi aiki tare da kamfanin jirgin sama na Tui da hukumomin Gambia da nan Landan,’’ in ji shi.

  8. Matar da ta nemi tallafin fan biyar ta samu fan 54,000

    Kerela

    Asalin hoton, Girija Harikumar

    Bayanan hoto, Mis Harikumar (dama) ta ce ta fara gangamin taimakawa Subhadra da iyalanta

    Wata ‘yar Indiya da ta nemi taimakon ciyar da ‘ya’yanta, ta samu tallafin miliyoyin rupee na kasar daga mutane daban-daban a shafukan sada zumunta.

    Subhadra mai shekara 46 na zaune a kudancin jihar Kerala, ta roki malamar makarantar da dan ta ke zuwa, ta taimaka mata da rupee 500, domin sayan abinci bayan rasuwar mijinta.

    Tausayin halin da ta ke ciki ya sanya malamar fara gangamin neman taimako a shafukan sada zumunta. Mako guda bayan nan Subadhra da iyalanta suka samu tallafin rupee sama da miliyan 5.

    Matar ta dade ta na shan wuya domin kula da ‘ya’yanta bayan rasuwar mijinta a watan Agusta da ya wuce.

    Ta gagara samun aiki saboda karamin dan ta ya na fama da matsananciyar rashin lafiyar da ke bukatar kulawa a ko da yaushe.

  9. Samar wa Ukraine makamai masu linzami da Amurka ta yi ba zai hana mu cimma buri ba - Rasha

    Putin

    Asalin hoton, EPA

    Gwamnatin Rasha ta ce samar wa Ukraine makaman kariya na makami mai linzami sampurin Patriot da Amura ta yi ba zai hana Rasha cinma burinta na mamaye Ukraine ba.

    A lokacin ziyarar da Shugaba Volodymyr Zelensky ya kai Washington ne aka ba da sanarwar wannan taimako da Amurkar ta bayar.

    Kakakin fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin, Dmirty Peskov ya zargi Amurka da yakar Rasha daga nesa ta hanyar amfani da 'yan Ukraine ko a za su kare.

    Ya ce babu alamun Amurka da Ukraine na da aniyar sauraren bukatun Rasha.

    Kira Rudik wata 'yar majalisar dokin Ukraine ce, ta ce "muna cike da matukar farin ciki da alfahari da abin da ya faru a jiya a Fadar White House da kuma a majalisar wakilai."

    A wani jawabi na nuna ƙin ba da kai da ya gabatar a zauren majalisar wakilan Amurka jiya, Mr Zelensky ya ce Ukraine ba za ta taba ba da kai ba, kuma abubuwan da Amurka ke bayarwa a matsayin gudummawa, jari ne na tabbatar tsaro a duniya.

  10. Bamu san yawan sabon kuɗin da muka buga ba - CBN

    .

    Mataimakiyar gwamnan Bankin Najeriya dake kula da dai-daita al'amuran kuɗi Aisha Ahmad ta ce bata san yawan adadin sabon kuɗin da bankin na CBN ya fitar ba don fara amfani da su a ƙasar ba.

    Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke amsa tambayoyi, a lokacin da ta bayyana a gaban majalisar wakilan ƙasar, don yi musu ƙarin bayani kan tsarin taƙaita cirar kuɗi da bankin ya samar.

    A yayin yi mata tambayoyi ɗaya daga cikin 'yan majalisar Sada Soli, ya nun adamuwar sa dagane da ƙarancin sababin kudin, kwanaki da sakin kudin don al'umma su fara amfani da shi. si dai gashi mmataimakin gwamnan ta ce bata san adadin da aka saka ba na sanon kudin.

    A jiya Laraab ne majalisar wakilan ta Najeriya ta buƙaci mataimakin gwamnan bankin ƙasar a bayyana a gaban ta a yau Alhamsi, biyo bayan tafiyar da gwamnan bankin Godwin Emefeli yayi don a duba lafiyar sa.

  11. Majalisar dattawan Najeriya ta ƙi amincewa da kasafin kuɗin 2023

    .

    Majsalair dattawan Najeirya ta ƙi amince wa da kasafin kudin ƙasar na 2023 da ta shirya amince wa da shi a ya yin zaman majalisar na yau Alhamis.

    Shugaban Majalisar dattijan ƙasar Ahmad Lawan ya ce rashin amincewa da kasfain kuɗin ya biyo bayan kurakurane da kasafin kudin ke kunshe shi, daga banagren gwamanti.

    "Sakamakon wasu ƙalubale, ba za mu iya karbar rahotan kwamitin kula da kasafin kudin ƙasar ba saboda, ya zo majalisa da matsaloli.

    Ahamd Lawan ya ce sai a jiya majalisar dattawan sun kuma karɓar ƙarin wasu buƙatu daga shugaban Najeriya, na kari a kasafin kudin na wasu ayyukan na musamman na naira tirilliyan 23.7.

    Ya ce ranar Larabar 28 ga Disambar da muke ciki, yanzu suka tsayar domin amincewa da kasafin.

  12. APC ta zargi PDP da shirya ta da hargitsi don hana zaben 2023

    .

    Kwamitin yaƙin neman zaben ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya zargi babbar jam'iyyar adawa ta PDP da shirin ta da hargisti don hana gudanar da zaben ƙasar na 2023.

    Daraktan yada labaran kwamitin yakin nema zaben Bola Ahmad Tinubu a APC, Festus Keyamo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da suka wallafa a shafin kwamitin na Twitter, yana mai kira ga hukumomin tsaro a Najeriya da su gaggauta gayyatar shugabanin jam’iyyar PDP don amsa tambayoyi.

    “Mun lura cikin damuwa cewar irin kalaman da ke ƙunshe da sanarwar da PDPn ta fitar , na nuni ƙarara da lama ce ta zasu kawo hargitsin a loakacin zaɓe mai zuwa, kuma mun sami bayanai masu ƙarfi kan wadan ke tayar da hargiutsin a wasu sassan ƙasar, ”a cewar sanarwar.

    Ya ce kiran ya zama wajibi biyo bayan wata sanarwa da PDP suka fitar kan “sahihin zabe” da ke cewar sun zargin wasu daidaiku na kokarin kawo hargitsi a zaben 2023.

    Keyamo ya nanata cewar lallai ne PDP sai ta samar da bayanai dangane da “wajen da aka yi taron da wadan da suka halarci taron; da sunaye wadan da ke taayr da hargitsin ta hanyar kai hare hare oishin hukumar zaben kasar INEC. Wannan bayanai dole ne su hada da bayanann wadan ke daukar nauyin su, idan akwai

    Keyamo ya ce sanarwar da PDP ta fita na zuwa ne sao’i 48 da wata kotu ta yankewa ɗaya daga cikin shugabnin PDPn hukunci, kan laifukan da ke da alaka da zabe, lokacin da ta ke mulki, manuniya ce da ke nuna yadda maratabar PDPN ke zubewa.

  13. Mutum shida sun mutu a wani hadarin mota a Bauchi - FRSC

    .

    Hukumar kiyaye afkuwar haɗura a Najeriya ta ce mutum shida ne suka mutu yayin biyu suka samu rauni a wani haɗarin mota da ya afku a ƙauyen Dinki da ke jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Hukumar ta ce hadrin motar ya faru ne bayan wata mota ƙirar Peugeot ta ƙwace wa direbanta da misalin karfe 10 na safiyar Laraba.

    Shugaban hukumar ta kula da haɗura a Bauchi Yusuf Abdullahi ne ya tabatar da faruwar lamarin yana mai cewar sai da ya dauki jimai'an su sa'a guda kafin su isa inda haɗrin ya afku don miƙasu asibi a basu agajin kulawa, a baban asibitin na Bogoro.

    ya kuma shawarci direbobi da su ringa kiyaye dokokin kan hanya da dokokin tuƙi, a duk lokacin da suka hau abin hawa.

  14. Qatar ta nemi karɓar baƙuncin gasar wasannin motsa jiki na 2036

    .

    Kwamitin kula da harkokin gasar motsa jiki ta Olympics na Qatar ya sanar da aniyar gwamantin ƙasar na karɓar baƙuncin gasar wasannin motsa jiki na 2036.

    Kwamitin ya tabbar da cewar Qatar ta miƙa bukatar karɓar baƙuncin karon farko don amincewa, ga kwamitin shirya gasar wasanni motsa jikin ta duniya, wanda hakan ba zai hana a bincika tare da duba yiwuwar ko tana da damar da zata karɓi irin wannan gasa.

    Sanarwar dai na ƙunshe a wata sako da kwmaitin ya wallafa a shafinsu na Twitter.

    Suma kasashen Indonesia da Inidiya sun nuna sha’awarsu na karbar baƙuncin gasar ta Olympics.

    Qatar ta yi hasashen samun kuɗin shiga da ya kai dala biliyan 20 a gasar cin kofin duniya na 2022 da aka kammala a baya-bayan nan. Wanda hakan ya sa ƙasar, take son karbar bakuncin gasar, saboda irin tsarin filiayen da take

    A baya a shekarun 2016, da 2020 da 2032 an ki amincewa da buƙatar Qatar na karɓar baƙuncin gasar wasannin motsa jiki.

  15. Gwamnatin Buhari ta ce ba za ta iya kammala aikin layin doga daga Ribas zuwa Borno ba

    ..

    Asalin hoton, Bashir Ahmad

    Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta iya kammala aikin shimfida layin dogo na jirgin ƙasa da ta ce za ta yi da zai hada gabashin ƙasar da kudancin ƙasar ba, kafin ƙarewar wa'adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

    Gwamnatin ta ce kammala aikin shimfada layin dogon ba abu ne mai yiwuwa ba saboda ƙarancin kudaden da za a yi aikin.

    Ministan harkokin sufurin ƙasar, Mu'azu Jaji Sambo, ne ya sanar da hakan bayan kammala zaman majalisar zartarwar ƙasar da ya gudana a ranar Laraba.

    A cewar sa gwamnatin tarayyar, ba ta sami damar karbar kudin hadin guiwar da za a gudanar da aikin ba, wanda hakan ya sa suka gaza samar da kudaden da suka kamata a yi aikin.

    Jihohin da za su ci gajiyar aikin sun haɗa da jihohin Ribas, Abia, Anambra, Imo, Ebonyi da Enugu, da Nasarawa, Benue, Plateau, Kaduna, Yobe, Borno, Bauchi da kuma Gombe.

    Shekara biyu da suka gabata ne, tsohon ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce za a kammala aikin shimfida layin dogon na Fatakwal zuwa Maiduguri kafin karewar mulkin Shugaba Buhari.

    A lokacin kaddamar da shirin, an kiyasta cewa za a kashe kusan dala biliyan biyu wajen gina layin dogon, wanda suke cewar zai bunƙasa tattalin arzikin jihohin 14 da aikin zai shafa.

  16. INEC ta ɗebe kayan zabe masu muhimmacin daga ofishinta na Imo

    .

    Hukumar Zaben mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ta kwashe kayan zabe masu muhimmanci daga ofishinta na jihar Imo sakamakon hari tare da lalata kayan da ke ciki, a yankin ƙaramar hukumar Isu.

    Shugaban sashen wayar da kan masu zabe da yada labarai na hukumar ta INEC Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a ranar Larabar a Abuja.

    “Saboda haka ne muka ɗauki matakan bai wa kayan zaben kariya, inda muka canza wa kayan zabe mazauni," in ji shi.

    Ya kara da cewa: "Haka zalika dukkan katin zaben da ba a karɓa ba, muna adanawa, sannan za a ƙaro jami'an tsaron don tabbbatar da an ci gaba da aikin rarraba katin ga masu shi, a harabar ofishin."

    Festus Okoye ya ce wannan shi ne karo na huɗu da aka kai hari ofishin INEC a jihar Imo da ke kudancin Najeriya, a ƙasa da makonni uku, bayan da aka kai makamancin wannan hari a ƙaramar hukumar Orlu da Oru dukkan su a jihar ta Imo.

  17. 2022: Waƙoƙin Burna Boy aka fi sauraro a Boom player, Apple, Spotify

    .

    Asalin hoton, Burna Boy

    Manhajojin sauraron waƙoƙi na Boom Player, da Apple, da Spotify sun ce waƙoƙin fitaccen mawaƙin Najeriya Burna Boy aka fi saurara a shekarar 2022.

    Burna Boy, wanda ya saki kundin waƙoƙinsa na shida “Love, Damini,” a 2022, shi aka fi saurara a manhajar Najeriya ta Boomplay da Spotify da Apple Music.

    Waƙarsa ta “Last Last” da ya yi ta baya bayan nan ta yi matuƙar karɓuwa a wajen al’umma, wannan hakan ya ƙara taimakawa wajen fito da shaharar mawaƙin, lamarin da ya sa ya kere wa takwarorinsa mawaƙa.

    Burna Boy ya taɓa lashe kyautar GRAMMY a shekarar 2021.

  18. Yau za a fara shari'ar Sam Bankman-Fried mai kamfanin kirifto a Amurka

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Sam Bankman-Fried, tsohon shugaban kamfanin kirifto da ya karye wato FTX, ya isa birinin New York daga Bahamas don fuskantar tuhume-tuhumen da ake masa.

    Mahukunta a Amurka sun ce an kai matashin mai shekaru 30 Amurka ne bisa zargin aikata almundahana mafi girma da aka taba yin irinta a tarihin kasar.

    Duk da musanta zargin da ake tuhumar sa da aikatawa, ana sa ran Mr Banjman Fried zai bayyana a kotu yau Alhamis.

    Biyu daga cikin abokan harkar sa sun musanta zargin.

    Ɗaya daga cikin lauyoyin matashin, Mr Wang, wanda ya ke karewa a gaban shari'a ya amince a nauyin da ke kansa, yana matukar bayar da handin kai a matsayinsa na shaida.

  19. Kotu ta ba da umarnin kwace $899,900 daga wurin Ahmed Idris

    Ana zargin Ahmed Idris da wawure miliyoyin dala

    Wata babbar kotun a Najeraya ta bayar da umarnin kwace dala 899, 900 da naira miliyan 304, 490, 160. 95 da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC ta karbo daga hannun tsohon Akanta Janar din Najeirya Ahmed Idris.

    Mai shari’a M. A Haasan ne ya bayar da umarnin a zaman kotun a ranar 13 ga Disambar da muke ciki, yayin da yake yanke hukunci kan ƙarar da hukumar EFCC a Najeriya ta shigar gabanta.

    Haka kuma kotun ta umarci da a karbe kadarori 15 mallakinsa da ke Kano da Abuja.

    Kadarorin da aka bayar da umarnin a kwace sun haɗa da babban kantin sayar da kaya na Al-Iklas, da wasu shaguna a Ladanai, da gidan gidan alfarma na unguwar Daneji dukkan su da ke Kano.

    Haka sai gidansa da ke Karsana a Abuja, da wani plotin, dake rukunin gidaje na Blue Fauntain shima a baban birnin Najeriyar Abuja.

    Hukumar EFCC ta gurfanar da Ahmed Idris da ƙarin wasu mutane, gaban kotun ne kan zargin aikata wasu laifuka 14 da ke da alaƙa da sata da halarat kuɗin haram da kiyasin su ya kai naira bilyan109.

  20. Barkanmu da safiyar Alhamis

    Masu bibiyar a wannan shafin barkanmu da safiyar Alhmis, ni ne Khalifa Shehu Dokaji da fatan mun wayi gari lafiya.

    Ku kasance da ni tsawon wannan rana domin karanta labaran da suka shafi rayuwarku.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a bbc hausa.