Hukumar NDLEA ta kama masu safarar muggan kwayoyi 23,907 cikin watanni 22 a Najeriya
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Aisha Shariff Bappa
Rufewa
Anan muka kawo karshen shafin kai tsaye da ke kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makoftanta har da wasu kasashen duniya.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu, amma kafin zuwan lokacin ku ziyarci shafinmu na Intanet bbchausa.com domin karanta wasu labaran na daban.
Shafukanmu na sada zumunta da muhawara na Facebook da Instagram, akwai labarai da rahotanni da hotuna har da bidiyo masu kayatarwa.
A madadin sauran abokan aiki, Badriyya Tijjani Kalarawi ke mu ku fatan Alkhairi daga nan sashen Hausa na BBC.
Mu kwana Ladiya.
Mjalisa na son Emefiele ya yi mata bayani kan tsarin takaita cire kudi a bankuna
Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, `yan majalisar wakilan kasar sun fusata sakamakon gazawar da
gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele ya yi wajen zuwan gaban su
domin ya yi bayani a kan ka`idar takaita cire kudi daga asussan ajiya da babban
bankin ya gicciya.
Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnan babban bankin yake
kasa amsa gayyatar `yan majalisar. Sai majalisar ta tsayar da ranar Alhamis mai zuwa domin gurfana a
gabanta.
Honarabul Abdullahi Mahmud Gaya dan majalisar ne mai wakiltar mazabar
Gaya da Ajingi da Albasu daga jihar Kano, kuma a tattaunawarsa da Ibrahim Isa ya fada masa dalilin kiran da suka yi wa Emefiele.
Dalilin da ya sa muka kira gwamnan babban bankin Najeriya domin ya yi mana bayani kan batun takaita kudaden da mutum zai cira, yawanci ayyukan da gwamnati ta yi alkawarin yi ba ta yi ba, idan aka kawo batun nan mu za mu cutu.
Maganar gaskiya wasu daga cikin mazabunmu kamar ni da na fito daga Gaya da Ajingi, ba mu da banki ko daya, to ka ga anan akwai matsala kenan.
Idan mutane za su bude asusun ajiyar banki sai sun bar garuruwanmu zuwa cikin gari, saboda babban bankin Najeriya bai wa bankunanan 'yan kasuwa damar bude rassa a irin wuraren ba,'' in ji Honarabul Gaya.
Wannan batu na takaita kudin da masu asusun ajiyar banki za su cira ko su tura, da babban bankin Najeriya CBN ya bulla da shi, na ci gaba da daukar hankali da janyo muhawara da cece-kuce a Najeriya.
Okupe ya ajiye aiki daga Darakta janar na kamfe din Peter Obi na Labour
A wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mr Doyin Okupe ya ce lokaci ya yi da ya kamata ya matsa gefe daga aikin da ya ke yi.
Mista Okupe dai shi ne Darakta Janar na gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Mista Peter Obe.
Ya kuma sanar da cewa har yanzu ya na tare da Mista Obi, da bashi goyon baya akan tafiyar siyasar da ke yi.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan wata Babbar Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja ta yanke wa tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.
A wata sanarwa da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC ta fitar ta ce Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ce ta yanke wa Mista Okupe hukuncin a ranar Litinin bayan samun sa da laifin badaƙalar naira miliyan 702.
Sai dai kuma kotun ta bai wa Okupe zaɓin biyan tarar naira 500,000 kan kowace tuhuma da ake masa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi taro kan zaman lafiya lokacin zaben 2023, Daga Zaharaddin Lawan a Kano
A Najeriya, rundunar ƴan
sandan jihar Kano ta gudanar da wani babban taron wanzar da zaman lafiya ya yin
yakin neman zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe a jihar Kano.
Taron ya sami
halartar shugabannin hukumomin tsaro da hukumar zabe da ƴan takarar gwamna da
shugabannin jam'iyyu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Ya yin taron na Yini daya, na hadin
gwiwa tsakanin rundunar ƴan sandan jihar Kano da kuma gidauniyar Aminu Magashi, an
tattauna dabarun da ya kamata a yi amfani da su don tabbatar da zaman lafiya ya
yin da ake tunkarar babban zaben 2023.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP
Mamman Dauda yace sun tsara dabarun da za su taimaka a yi zaben lafiya.
An gabatar da kasidu
daban-daban game da yadda za a yi zaben lafiya daga manyan bakin da aka gayyata
ciki har da hukumar zabe mai zaman kanta, inda Sulaiman Alkali jami’I a hukumar
a Kano yace sabuwar dokar zaben 2022 ta sake basu kwarin gwiwa yin aiki ba sani ba sabo.
Su ma malamai sun ja kunnen
‘yan siyasa da kada su yi abin da zai haifar da fitina a cikin al’umma.
Akasarin mahalartar taron
zaman lafiyar sun bukaci jami’an tsaro su yi aiki tukuru, sannan shugabanin
hukumimin tsaro da suka gargadi ‘yan takara, su guji takalar junansu da kuma
kaucewa yiwa juna baraza lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin zabe.
Bayanai na cewa nan gaba
rundunar ‘yan sandan zata sake ganawa da ‘yan takarar a Kano don su sanya
hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar ilimi ta Afganistan ta ce za a dakatar da mata daga zuwa jami'o'i har sai abun da hali ya yi.
Wannan dai daya ne daga cikin irin matakan kara uzzurawa 'ya'ya mata musamman ta fuskar hana su samun ilimin boko da Taliban ke dauka.
Wakilin BBC ya ce wata wasika daga ma'aikatar ilimi ta Taliban ta umarci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu, su hana mata shiga take yanke.
Dama dai tuni aka hana mata zuwa makarantun sakandire.
A watan Nuwamba ne hukumomi suka haramtawa mata shiga wuraren shakatawa a Kabul babban birnin kasar, suna masu cewa ba a bin dokokin Musulunci a can.
Tun watan Satumba da aka sake bude makarantu a Afghanistan, aka tilasta wa 'yan mata zaman gida, inda suke kula da 'yan uwansu maza, yayin da sauran mazan ke tafiya makaranta domin daukar karatu.
Kasar ta kasance daya tilo a duniya da 'yan mata tsakanin shekara 12 zuwa 18 ba sa zuwa makaranta.
Hukumar NDLEA ta kama masu safarar mggan kwayoyi 23,907 cikin watanni 22 a Najeriya
Asalin hoton, NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta sanar da kwace sama da kwayar maganin Tramadol miliyan 100, cikin watanni 22 a sassa daban-daban na kasar.
Shugaban hukumar Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ne ya sanar da hakana aranar Talata a wurin taron raba kyautuka da karin girma ga wasu daga cikin ma'aikatan hukumar a Abuja babban birnin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ambato Marwa na cewa ''Cikin watanni 22, hukumarmu ta kama masu safarar mutane 23,907, ciki har da shugabanninsu 29. Mun kuma kama sama da tan 5,500 na muggan kwayoyi, da suka kai darajar naira biliyan 450.
Matakin da muka dauka, na samame gida-gida da ake shuka ganyen tabar wiwi, ya ba mu nasarar lalata eka 772.5 na gonakin wiwi. Mun kuma yi nasara ba 'yar kadan ba wajen rage yaduwar muggan kwayoyi, da sabuntawa wadanda sukai nisa a shaye-shayen tunani,'' in ji Marwa.
Marwa ya ce idan har wadannan muggan kwayoyi suka fada hannun bata gari, Allah ne kadai ya san abin da zai faru idan kwayoyin suka fada hannun jama'a musamman matasa.
Ba wannan ne lokacin farko da NDLEA ke yin irin wannan wawan kamun na miyagun kwayoyi, sai dai har yanzu ana fama da matsalar shaye-shaye ba ga matasa da magidanta ba, har da mata da kananan yara a Najeriya.
Gwamnatin Kenya ta ce a sallami wadanda ake bi bashin kudin asibiti
A Kenya gwamnan babban birnin kasar Nairobi ya umurci dukkan asibitocin da ke rike da marasa lafiyar da ba su kammala biyan kudin aikin da aka musu ba, su kyale su su tafi gida.
Asibitoci a babban birnin dai sun saba rike marasa lafiya har sai sun kammala biyan duk kudin da ake binsu.
Gwamna Johnson Sakaja, ya ce gwamnatin babban birnin za ta biya wa marasa lafiyar kudaden da ake binsu, inda ya bayyana matakin a matsayin goron kirsimeti domin mutane su yi murna da iyalansu.
Al'ummar Kenya na korafin cewa asibitoci masu zaman kansu da na gwamnati na cajar kudaden da suka zarce kima, abun da ke hana mutane da dama zuwa neman magani.
An gano gawa 213 ciki har da sojoji 10 a karanbattarsu da 'yan bindiga a Zamfara
An gano gawawwaki 213 da suka hada da 'yan ta'adda da masu kai musu bayanai, kwanaki kadan da mummunar musayar wutar da aka yi tsakanin sojojin Najeriya da 'yan bindigar a wasu yankunan jihar Zamfara.
Jaridar PRNigeria ta rawaito, sojoji 10 na daga cikin wadanda suka mutu a lokacin da 'yan bindigar suka fantsama garuruwan da ke kusa.
A ranar Litinin ma PRNigeria ta rawaito dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun yi nasara kan 'yan bindigar a kauyen Malele da ke karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara.
Samame ta sama da sojojin sama na Najeriyar suka kai a ranar Asabar ya yi nasarar hallaka gwamman 'yan fashin dajin ciki har da wasu manya daga cikinsu.
An samu karuwar hare-haren 'yan ta'adda a jihar Zamfara, sakamakon yadda sojojin Najeriya ke fatattakarsu daga inda suke buya, samamen da aka kai garuruwan Malele, Maigoge, Yan Sawayu, Ruwan
Tofa, Mai Awaki, and Zama Lafiya, da ke karkashin gundumar Mutunji a karamar hukumar Dansadau
sun kara kai mi.
'Yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar barazana a jihar Zamfara, inda suke haddasa rasa rayuka da dukiya, ko da yake gwamnatin jihar da jami'an tsaro na cewa su na bakin kokarin magance matsalar.
'Yan bindiga sun kashe mutum takwas a Iraqi
Wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar IS ne akan babura sun hallaka farar hula takwas, wasu uku sun jikkata a harin da suka kai wani kauye da ke kasar Iraqi.
Sun kai harin ne kauyen Albu Bali da ke arewacin birnin Bagadaza, kuma nan ne yankin da ba sa tsoron masu tada kayar bayan na IS, yankin da suka ji babu dadi a shekarar 2014 lokacin da suka fafata da dakarun wanzar da zaman lafiya a iyakar Syria da Iraqi.
Wannan harin na zuwa ne, kwana guda bayan wani harin bam da aka dasa a gefen hanya da ya hallaka 'yan sanda tara a birnin Kirkuk mai arzikin mai da ke arewacin Iraqi.
Kungiyar IS dai ta rasa ikon yankuna da dama da ta ke rike da su tun shekarar 2017, a bangare guda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu IS na da karfin iko a Iraqi da Syria inda ta ke da dubban mahara a kasashen.
Jamus ta bai wa Najeriya gumakanta 1,000 da aka sace a ƙarni na 19
Asalin hoton, AFP
Ministar Harkokin Wajen Jamus Annalena Baerbock ta miƙa gumaka da sassaƙe-sassaƙe 20 ga gwamnatin Najeriya, waɗanda aka sace a ƙarni na 19.
Ministar ta miƙa su ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka yi a Abuja, babban birnin ƙasar.
An dawo da waɗannan gumaka na tagulla na Benin ne bayan da aka cimma wata yarjejeniya a farkon shekarar nan ta mayar da muhimman sassaƙe-sassaƙen fiye da 1,000 da mamallakansu na ainihi.
A watan Yuli ne, najeriya ta ce wannan ne karo na farko da wata ƙasar turai ta shiga irin wannan yarjejeniya.
Ms Baerbock ta ce hakan wani ƙoƙari ne na daƙushe "tarihin mulkin mallakar baƙaƙen fata" da aka yi.
Da take magana a wajen bikin a yau Talata, ta ƙara da cewa dama ce ta gyara wasu kura-kurai da aka yi a baya.
Da cikin abubuwan da aka mayar da su sun haɗa da wasu fitattun gumaka da sassaƙe-sassaƙe.
A baya-bayan nan ana samu ƙaruwa kiraye-kiraye kan ƙasashen Turai su mayar da kayayykin Afirka da suke maƙare a gidajen tarihinsu.
An kashe masu ikirarin jihadi da dama a Pakistan
Jami'ai a Pakistan sun ce jami'an tsaro sun kashe wasu masu ikirarin jihadi tare da kubutar da dukkan wadanda suka yi garkuwa da su a wata cibiyar bincike ta yaki da ta'addanci da ke arewa maso yammacin kasar.
Mayakan na Taliban na Pakistan sun yi galaba a kan masu yi musu tambayoyin tare da yin garkuwa da su a yankin Bannu a ranar Lahadi
Kawo yanzu dai ba a bayyana adadin mayakan da aka kashe ba.
Mazauna yankin sun ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa da ke fitowa daga yankin a safiyar yau.
Wakilin BBC ya ce kungiyar Taliban din ta Pakistan wadda ke da dangantaka mai karfi da takwararta ta Afghanistan ta zafafa hare-haren da take kaiwa, tun bayan da suka kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta a watan jiya.
An yafe wa marasa lafiya biyan kudin asibiti a Kenya a matsayin goron kirsimeti
Gwamnan babban birnin kasar Kenya, Nairobi ya umurci dukkan asibitocin da ke rike da marasa lafiyar da ba su kammala biyan kudin aikin da aka musu ba, su kyale su su tafi gida.
Asibitoci a babban birnin dai sun saba rike marasa lafiya har sai sun kammala biyan duk kudin da ake bin su.
Gwamna Johnson Sakaja, ya ce gwamnatin babban birnin za ta biya wa marasa lafiyar kudaden da ake bin su, inda ya bayyana matakin a matsayin goron kirsimeti domin mutane su yi murna da iyalansu.
Al'ummar Kenya na korafin cewa asibitoci masu zaman kansu da na gwamnati na cajar kudaden da suka zarce ƙima, abun da ke hana mutane da dama zuwa neman magani.
Mafarki ya zama gaskiya !
Kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi ya kwana ya tashi tare da kofin duniya da suka lashe a Qatar.
Babban burin Messi ya cika a wannan karon bayan ya gwada sau hudu babu nasara.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Gwamnan Nairobi ya biya wa marasa lafiya kudin asibiti
Asalin hoton, OTHER
Gwamnan Nairobi a kasar Kenya, ya ba wa dukkan asibitocin jihar umarnin sallamar duk wasu marasa lafiya da aka rike saboda rashin kammala biyan kudin asibiti.
Dama dai asibitocin jihar sun saba rike marasa lafiyar da ba su kammala biyan kudadensu ba har sai sun biya.
Gwamna Johnson Sakaja, ya ce gwamnatin jihar ce za ta biya kudaden, sannan ya ce za a biya kudaden ne a matsayin kyauta ta musamman saboda bikin kirsimeti.
Yawancin 'yan kasar Kenya na kokawa a kan yawan kudaden da ake cajar su a asibitocin gwamnati da ma masu zaman kansu, abin da ke hana wasu da dama zuwa asibiti.
An fitar da kudi mai hoton Sarki Charles
Babban bankin Ingila ya fitar da sabbin takardun kudi masu dauke da hoton Sarki Charles.
Hoton Sarkin zai fito ne a takardun kudi na fam biyar da 10 da 20 da kuma 50.
Bankin ya ce kudin za su fara shiga hannun mutane a tsakiyar shekara ta 2024.
Za a ga hoton Sarkin a gaban jikin kudin da kuma idan an daga su ta gefen alamar tsaron jikin kudin.
Bankin ya ce za a ci gaba da karbar tsoffin kudin kasar a shaguna koda an fara amfani da sabbin masu dauke da hoton Sarki Charles.
Sarauniya Elizebeth, ita ce basarakiya ta farko da aka sanya hotonta a jikin takardun kudin Ingila wanda aka fara a 1960.
An yanke wa 'yan kungiyar IS 17 hukuncin kisa a Libya
Wata kotu a Libya ta yanke wa wasu 'yan kungiyar IS 17 hukuncin kisa.
Dukkansu an same su da aikata laifuka a lokacin da masu ikirarin jihadi ke iko da yammacin Sabratha.
Ofishin babban mai shari'a na kasar ya ce mutanen da na hannu a kisan mutane fiye 50 da kuma sace wasu gwammai.
Kungiyar IS ta kwace ikon wasu yankunan Sabratha a 2014, kafin daga bisani ta kwace ikon birnin Sirte, wanda ya zamo matattarar masu ikirarin jihadin a Libya.
Bayan shekaru biyu da kwace ikon, sojojin Libya da ke biyayya ga gwamnatin kasar suka fatattake su daga birnin.
Ma'aikatan jinya na yajin aiki a Ingila da Wales da kuma Ireland ta Arewa
Dubban ma'aikatan jinya ne a Ingila da Wales da kuma Ireland ta Arewa ne suka shiga rana ta biyu da fara yajin aiki.
Ma'aikatan sun shiga yajin aikin ne saboda rashin biyan wasu hakkokinsu.
Yajin aikin shi ne na baya bayan nan da ma'aikata suka dauka a fadin Birtaniya saboda tsadar rayuwa.
Ma'aikatan hukumar kula da lafiya ta Birtaniya ne za su rinka kula da marasa lafiya a asibitoci saboda yajin aikin.
Kungiyar ma'aikatan jinyar ta ce duk da hahhawar farashin kayayyakin da ake samu a kasar, ba a kara musu kudi ba, kuma sun shan wuya wajen gudanar da aikinsu.
Gwamnatin kasar ta conservatin ta ce bukatar da kungiyar ta yi na bata karin kashi 19 cikin 100 ba zai yi wu ba.
Yadda mata mafarauta suka shiga yaki da 'yan bindiga a Taraba
Asalin hoton, OTHER
A jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, mata mafarauta ne suka bi sahun takwarorinsu maza wajen yaki da 'yan bindiga a jihar.
Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa matan sun hadar da masu aure da kuma marasa aure.
Matan sun ce sun shiga a dama da su a yakin ne saboda su taimaka wa mazan wajen murkushe 'yan bindigar da suka addabi jihar.
Matan sun ce, ana kashe mutane maza da mata har da yara a wasu sassan jihar, yayin da ake sace wasu ciki har da matan aure da yammata sannan ayi musu fyade musamman a yankunan Karim-Lamido, da Gassol da kuma karamar hukumar Bali.
Matan sun ce irin wadannan abubuwa da ke faruwa ne ya sa su shiga cikin kungiyar mafarautan da ke yaki da 'yan bindiga a jihar.
Sun ce suna da kwarin gwiwa kuma ba sa tsoro don haka a shirye suke su shiga cikin yakin da ake da 'yan bindiga a jihar ta Taraba don murkushe su.
Sarki Sudan na Wurno Shehu Othman Malami ya rasu
Asalin hoton, OTHER
Sarkin Sudan na Wurno, Ambasada Shehu Othman Malami ya rasu.
Marigayin ya rasu ne a Masar bayan ya sha fama da jinya.
An haifi marigayin a Sokoto a shekarar 1937.
Ya rike mukamai ciki har da jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu a lokacin marigayi Janar Sani Abacha.
Sannan ya kasance shugaban hukumar gudanarwar bankuna da dama a Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana rasuwar basaraken na Sokoto a matsayin babban rashi ba ga iyalansa ba kadai har da gwamnatin Najeriya da kuma daukacin al'ummar jihar Sokoto.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da kuma 'yan uwan marigayin.
Okupe ya biya tarar naira miliyan 13 don gujewa zaman gidan yari
Asalin hoton, OTHER
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon
shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya biya tarar naira miliyan 13 don gujewa
zaman gidan yari.
A ranar Litinin ne wata Babbar Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja ta yanke
wa Doyin Okupe hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari bayan
gabatar da ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa Mista Okupe ya karɓi kuɗaɗe lakadan
na biyan wasu ayyuka a yayin da yake gudanar da aikinsa, kuma bai kai kudin
asusun da ya kamata ba.
Tun a shekarar 2019 ne EFCC ta gurfanar da Mista Okupe a gaban kotu kan
zargin almundahanar.
An zargi Okupe da karɓar kuɗaɗe daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa
shawara an sha’anin tsaro, waɗanda ya gaza yin bayani kansu.
An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyun ne bayan kama shi da laifi 25
daga cikin tuhuma 59 da ake masa.
Tuhume-tuhumen dai sun ta’allaƙa ne a
kan karɓar makuɗan kuɗaɗe kama daga naira miliyan 10, a wasu al’amura
daban-daban daga shekarar 2012 zuwa 2015.
Mr Okupe, ya biya tarar ce, bisa zaɓin
biyan tarar naira 500,000 kan kowace tuhuma da ake masa da kotu ta bashi.
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon
shugaban na Najeriya, ya biya tarar ce tun kafin wa’adin da aka gindaya masa.