Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An gano cibiyar haɗa bama-bamai ta 'IPOB' a Ebonyi

Wannan shafin yana kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge

  1. EFCC ta kwato naira biliyan 30 daga hannun Ahmed Idris

    Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati EFCC) ta ce ta kwato naira biliyan 30 daga wurin dakataccen Akanta-Janar na kasar, Ahmed Idris.

    Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

    EFCC tana tuhumar Idris da wasu mutane bisa zargin sace N109.

    Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.

    EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.

    An kama Idris bayan ya ƙi karɓar gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa.

  2. Barkanmu da safiyar Juma'a

    Buhari Muhammad Fagge ne yake muku barka da safiyar Juma'a - Haji babbar rana.

    Ku kasance da ni tsawon wannan rana domin karanta labaran da suka shafi rayuwarku.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a bbchausa.