Bankwana
Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake sallama da ku a wannan Juma'ar. A kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin yana kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma sassan duniya.
Buhari Muhammad Fagge
Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake sallama da ku a wannan Juma'ar. A kwana lafiya.
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da wata kungiyar kare hakkin yada labarai sun bi sahun masu sukar hamshakin attajirin nan mamallakin shafin Twitter, Elon Musk, bayan ya rufe shafukan wasu 'yan jarida da ke yada labaransa.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya ce majalisar ta damu matuka, ganin cewa dama 'yan jarida na fuskantar barzana iri iri.
Kungiyar yan jarida ta Reporters Without Borders ta yi Allah-wadai da abin da ta kira abun mamakin da Mista Musk ya yi.
Shi dai Elon Musk ya ce 'yan jarida ba su da 'yancin samun wata kulawa ta musamman.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Joe Biden na Amurka tare da wasu shugabannin Afirka a wajen tarn kasashen Afirka da Amurka da ake gudanarwa a birnin Washington DC.
Mambobin jam'iyyar ANC da ke mulki a Afrika ta Kudu na hallara a birnin Johannesburg domin wani taro da shugaba Cyril Ramaphosa ke fatan a sake zabarsa a matsayin shugaban jam'iyyar, duk kuwa da wata badakala a baya-bayan nan.
Mista Ramaphosa ya kaucewa binciken tsige shi a farkon makon nan, lokacin da akasarin 'yan majalisar wakilan jam'iyyarsa suka kada kuri'ar kin amincewa da wani rahoto da ya gano cewa watakila ya karya dokar yaki da cin hanci da rashawa bayan sace wasu makudan kudade a gonarsa.
Babban abokin hamayyarsa a neman shugabancin shi ne tsohon ministan lafiya, Zweli Mkhize, wanda shi ma ake zarginsa da cin hanci da rashawa.
Wani wakilin BBC a Johannesburg ya ce akwai yiwuwar Mr Ramaphosa zai ci gaba da rike mukaminsa, duk da koma bayan da aka samu a baya-bayan nan.
A gobe Asabar shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai cika shekara 80 da haihuwa.
An haifi shugaba Buhari ne a ranar 17 ga watan Disamba a garin Daura da ke Katsina.
Tuni manyan mutane da 'yan siyasa suka soma tura sakon taya murna ga shugaban kasar.
Cikin wadanda suka soma aike sakon murnarsu ga shugaban akwai dan takarar shugabanci kasa a inuwar Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila.
Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta ce ta samu nasarar gano wata cibiyar harhaɗa bama-bamai, mallakar kungiyar IPOB ta 'yan aware mafi girma a kudu maso gabashin Naijeriya.
Wannan dai ya zo bayan jami'an tsaro na rundunar hadin-guiwa ta samu sahihan bayanai game da cibiyar da ake hada bama-bamai domin tayar da zaune tsaye cikin al’umma.
Ta kashe da kuma kama wasu mambobin IPOB, yayin da wasu suka tsere da munanan raunuka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi Chris Anyanwu wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce binciken ya biyo bayan wani samame da ‘yan sandan suka kai inda suka yi artabu da ‘yan kungiyar IPOB/ESN
Mutum biyu sun hallaka daga cikin 'yan kungiyar ta aware ta IPOB tare da kama daya daga cikin kwamandojin a cibiyar haɗa bama-baman.
Tawagar hadin guiwa ta Sojoji da jami’an tsaro na farin kaya da 'yan sanda, sun dira inda Kwamandan da ake zargi yake kitsa barna tare da gano manyan abubuwa na tashin hankali.
Abubuwan da aka gano sun haɗa da "Ababan fashewa 30 da na'urorin haɗawa da kwance bama-bamai da sauran na'urori da sinadaran hada bama-baman daban-daban da ake hada nakiyoyin.
Anyanwu ya ce an gano cibiyar hada bama-bamai ce a wani sansani da ke Obegu da ke kan iyaka tsakanin kananan hukumomin Onicha-Isu da Ishielu na Jihar Ebonyi.
Jami'in ya kuma ce wasu ‘yan sanda biyu sun samu kananan raunuka yayin da aka kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar da raunata wasu daga cikin mambobinsu da suka tsere yayin musayar wuta da ta gudana.
An shiga wata na hudu, a zanga-zangar da ake yi a Iran sakamakon kisan da ake zargin 'yan sanda sun yi wa wata mata mai suna Mahsa Amini mai shekaru ashirin da biyu.
Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Zahedan da ke kudu maso gabashin kasar suna yin Allah wadai da jami'an tsaron Iran saboda murkushe masu zanga-zanga.
A cikin jawabinsa na baya-bayan nan, shugaban Iran Ibrahim Raisi, ya sake yin ikirarin cewa zanga-zangar wata manakisa ce ta kasashen yamma.
A wannan juma'ar limamai a masallatan juma'a sun rika caccakar majalisar dinkin duniya kan cire Iran daga kwamitin kare hakkin dan adam na majalisar.
Wani babban malamin Shi'a Ahmad Khatami, ya gaya wa masallata cewa addinin musulunci ne ya yi wa kowa riga da wando ta fuskar ba shi 'yanci.
Gwamatin tarayya ta bayar da umarnin bude gadar Neja ta biyu domin matafiya da ababan hawa su yi amfani da ita, domin saukaka zirga-zirga a yankin kudu maso gabas a lokutan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar Shekara.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta gina gadar bayan shafe gomman shekaru tana cikin yanayi na lalacewa da kuma Ababan hawa kan kwashe tsawon kwananki cunkushe saboda rashin kyawunta.
Babbar gadar dai ta kasance wacce take hada kudu maso gabashin kasar da sauran jihohi dake makwabtaka.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, wanda ya ba da wannan umarni a ranar Laraba a wajen kaddamar da gadar, ya ce za a bude gadar domin amfani da ita na tsawon wata daya a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara mai kamawa.
Minista Fashola ya ce manufar Shugaba Muhammadu Buhari na kammala gadar ita ce ceton rayuka da kuma rage radadin talauci da lokaci mai tsawo da ake bata-wa kan tsohuwar gadar Neja ta farko.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da cewa tunda an gama gadar ya kamata a samar da hanyar shiga ta yadda a lokacin hutu zasu ci gajiyar wannan muhinmin gyara da aka yi kan gadar.
Hukumomin sufuri a kasar sun kayyade gudun kan hanyoyin Najeriya shine kilomita 100 a cikin sa’a guda.
Saboda haka gwamnati za ta ji dadi idan masu amfani hanyoyi na tuka motocinsu cikin natsuwa da kiyayewa a lokacin amfani da wannan hanya musamman a lokutan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Gwamnatin kasar ta bayar da tsawon kwanaki talatin ana cin gajiyar ko yiwa mutane alakoro kafin a sake rufe babbar gadar a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2023, domin ci gaba da aiwatar ayyukanta da suka dan rage.
Shugaban lura da cibiyar al'adun Rasha a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya jikkata a wani harin bam.
Ofishin jakadancin Rasha ya ce ya ji rauni ne a kansa, amma yana karbar magani a wani asibiti da ke Bagui babban birnin kasar.
Sojojin haya na Wagner sun zargi Faransa da faruwar lamarin, suna cewa ita take daukar nauyin ta'addanci.
Wanger na aiki a wasu daga cikin kasashen Afrika da suka hada da Mali da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya ce babu rayuwar da aka rasa ta yan ci rani da suka yi aikin gina filayen wasa a Qatar, da duniya ba ta yi bakin ciki ba.
Da yake martani game da tambayar da aka masa kan batun, Infantino ya ce mutuwar tasu a bakin aiki rashi ne ga iyalansu da kuma kowa da kowa.
Sai dai ya ce wasu kafafen yada labarai na zuzuta batun don bata sunan wasu.
''Mutum 400 zuwa 500 ne suka mutu yayin aikin gina filaye daga 2014 zuwa yanzu. Idan muna magana kan alkaluma, yakamata mu rika tabbatar da cewa mun fadi ainihin gaskiyar.''
''Yakamata mu yi hattara kar mu fadi abunda ba shi ba da zai iya haifar da wani abu daban ga idon al'umma'', in ji Shugaban na FIFA.
Ukraine ta ce tara daga cikin cibiyoyin samar da wutar lantarkin ta sun lalace a wasu manyan sabbin hare-haren makamai masu linzami na Rasha, kuma yawan makamashin da ake amfani da shi a kasar ya ragu da fiye da rabi.
An bayar da rahoton cewa, hare-haren da aka ce sun kai akalla sittin, sun kashe akalla fararen hula uku a tsakiya da kuma kudancin Ukraine. A birni na biyu mafi girma a kasar wato Kharkiv, babu wutar lantarki.
Rahotanni sun ce yanayi ne mai wahala ake ciki a Kyiv, ana ta kankara, mutane a nan da sauran garuruwa na cikin mawuyacin hali.
Ana fargabar baraguzai sun danne wasu, yayin da wani makami mai linzami ya dira a wata majalaisa da mutane ke hutawa a birnin Kryvyi Rih da ke tsakiyar kasar.
Shugaban hukumar zaben Najeriya - INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya ce tun daga shekara ta 2019 zuwa yanzu an kai hari kan ofisoshin hukumar sau 50 a jihohi 15 na kasar.
Ya bayyana haka ne a yau Juma'a lokacin da yake bayani ga kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke bincike a kan barnar da aka yi wa INEC.
A cewar Farfesa Yakubu an kai hari sau takwas a shekara ta 2019 a ofisoshin INEC, sau 22 a 2020, sau 12 a 2021 sannan kuma a 2022 an kai hari sau takwas.
Shugaban INEC din ya ce an fi kai hare-hare kan ofisoshin hukumar a jihar Imo inda aka kai sau 11 sannan kuma sai jihar Osun inda aka kai hari sau bakwai.
Galibin hare-haren an kaddamar da su ne a jihohin da ke kudancin Najeriya.
Farfesa Yakubu ya ce duk da irin wadannan matsalolin, suna ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da suka kamata domin tsara zabe mai inganci a Najeriya.
Hukumar lafiya a matakin farko ta ce kimanin 'yan Najeriya miliyan 54 ne aka yi musu allurar korona cikakkiya, yayin da miliyan 60 aka yi musu ta farko.
Shugaban hukumar Faisal Shu'aib ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin nazari kan nasarar da hukumar ta samu.
Ya ce hukumar na kokarin yi wa kashi 70 cikin 100 na mutanen da suka cancanta a Disambar 2022, kuma an kara tsammanin da ake yi na yi wa 'yan kasar cikakkiyar allura da suka kai kashi 53 na yawan 'yan kasar, yayin da kashi 63 za a yi wa matakin farko.
Ya kuma ya bai wa gwamnonin jihohin Nasarawa da Jigawa da Kwara da Kaduna da kuma Borno saboda samar da yanayi mai kyau ga hukumar lafiyar.
Hukumar yada labarai ta Taliban ta zane mutum 12 a garin Firoz Koh, babban birnin Lardin Ghor.
Shugaban yada labarai na Taliban Sakhir Rahman Fayez, kuma shugaban kotun daukaka kara na lardin ya ce, "kotun nan ta tuhumi mutum 12 ciki har da mace da aikata abin da bai dace ba, rashin da'a, sata, da kuma wadanda suka sha kayan maye, duka an zane su a filin wasan kwallon kafa na garin.
Ya ce "an zargi mutum 6 daga cikinsu da yin sata, wasu 4 kuma daga cikinsu an zarge su da shan giya, an zargi mutum daya kuma da yin rashin da'a, mutum daya kuma an zarge shi da guduwa daga gida, kuma duka na zane su."
A watan jiya, Taliban ta zane maza da mata a bainar jama'a, kuma shi ne hukuncin farko da aka yi a bainar jama'a a Farah.
A kalla mutum 1,700 ne suka tsere wa rikicin da ke faruwa tsakanin bangaren sojoji a arewacin Sudan Ta Kudu kusa da Nile wanda ya gangaro cikin Sudan, kamar yadda gidan jaridar Sudan din Suna ya rawaito.
Hukumar Unicef ta MDD ta ce rikici tsakanin sojojin da ya fara a watan Agusta ya tilastwa dubban maza da mata tserewa daga muhallansu, saboda ci gaba da samun kashe fararen hula da ake yi, ana sace wasu wasu kuma a raunata su.
Tun daga nan rikicin ya watsu zuwa yankin Jonglei dana Unity.
A ranar Laraba, MDD ta ce rikicin ya yi sanadin mutuwar mutum 166 ya zuwa yanzu.
Ana ta kiraye-kiraye ga kungiyoyin ba da agaji su kai agajin gaggawa ga wadanda suke neman tsira.
Majalisar Mozambique ta amince da kudurin amfani da 'yan kato da gora a yakin da take da masu ikirarin jihadi a arewacin lardin Cabo Delgado.
'Yan kato da gora suna taimakon sojoji da kawayensu daga Rwanda da kuma yankin kudancin Afrika a yakin da suke da masu jihadi a lardin.
Ministan tsaro Cristovao Chume, wanda ya gabatar da wannan kuduri gaban majalisar, ya bayyana cewa sojojin Muzambique ba su da karfin da za su yaki wadan nan mutane da ake fama da su, su kudai.
Ya ce akwai bukatar gaggawa ta fara amfani da 'yan bindiga domin karfafa sojoji, da kuma kokarin karkade sauran mayakan.
Yace za su rika kare unguwanni da kuma dukiyoyin al'umma, irin dai hanyoyin da aka yi amfani da su a wasu yankunan a baya.
Gwamnatin India ta ce hudu daga cikin magungunan tarin da suka kashe wasu yara a Gambiya an yi gwaji an gano ba su da matsala.
Hukumar Lafiya Ta Duniya a watan Oktoba ta ce hudu daga cikin magungunan tari da kamfanin Maiden da ke da alaka da mutuwar yara 66 a Gambiya.
Daga baya hukumar kula da magunguna ta Indiya ta ce WHO ba ta da wata hujja ta wannan ikirari da ta yi. Indiya dai ita ce kasar da ta fi kai maguguna nahiyar Afrika.
Har yanzu dai ana ci gaba da bincike domin gano matsalolin da ke tattare da wadannan magunguna da suka janyo illa a Gambiya.
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da shirin sake bude makarantun firaimare da sakandire da aka rufi a kananan hukumomin Rafi da Shiroro da kuma Munya saboda hare-haren 'yan bindiga.
Gwamna Abubakar Sani Bello yabbaya hakan yayin bude wasu dakunan kwanan dalibai da gidajen ma'aikata da dakunan karatu da cibiyar kashe gobara a Jami'ar Badamasi Bababngida da ke Lapai.
Ya ce za a bude makarantun ne bayan gagarumin ci gaban ta fuskar tsaron da ya shafi wadannan kananan hukumomi, ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da karfafa tsaro domin kiyaye yara 'yan makarantar da ke yankunan.
Ya ce dakunan kwanan daliban da sauran wuraren za su rage kalubalen da dalibai ke fuskanta a jami'ar.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce makobciyar kasarsa Burkina Faso ta gayyaci sojojin haya daga kamfanin Wagner na Rasha.
Ya bayyana hakan ne ya yin wata tattaunawa da Sakataren Gwamnatin Amurka Antony Blinken inda ya bayyana hakan a matsayin abin tsoro.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke nuna damuwa kan karuwa fantsamar masu ikirarin jihadi a yankin kasasshen kudu da hamadar sahara.
Shugaban kasar Ghanan Akufor-Addo ya ce sojojin hayar Rashan na kan iyakar arewacin kasarsa.
Ya ce ya gano cewa an bai wa sojoji wani wajen hakar ma'adanani ne a matsayin ladan aikinsu - domin yaki da masu ikirarin jihadi.
Rahotanni daga Malaysia na cewa kimanin mutum takwas ne suka mutu sakamakon wata zaizayar ƙasa da ta faru a wajen Kuala Lumpur, babban birnin ƙasar.
Lamarin ya faru a wata gona da ke jihar Selangor da sanyin safiyar yau.
Hotunan bidiyo sun nuna masu aikin agaji suna tono laaka mai kauri tare da tumɓuke bishiyoyi domin lalubo sama da mutane hamsin da suka yi ɓatan dabo.
Zuwa yanzu dai ba a san abin da ya haifar da zaizayar ƙasar ba amma jihar ta sha fuskantar wannan ibtila'i a baya.