Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An karrama ɗan sandan da ya ƙi karbar rashawar $200,000 a Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa

  1. Mutum fiye da 120 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

    Mahukunta a Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo sun ce mutane fiye da 120 ne suka rasa ransu sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da aka jima ba a fuskanci irinta ba a babban birnin kasar Kinshasa.

    Yawancin wadanda suka rasa ran na su na zaune ne a yankunan da tsaunuka suke inda aka samu zabtarewar kasa.

    Rahotanni sun ce akwai iyalan gida guda su tara da suka mutu bayan gidansu ya rufta.

    Tuni aka ayyana zaman makokin kwana uku a kasar wanda za a fara daga yau Laraba.

    Mutane dai na yawan kaura su koma Kinshasa a shekarun baya bayannan kuma birnin na fama da rashin magudanan ruwa.

  2. Barkanmu da safiyar Laraba

    Masu bibiyar wannan shafin ni ce Aisha Shariff Baffa na ke muku barka da safiya.

    Ku kasance da ni tsawon wannan rana domin karanta labaran da suka shafi rayuwarku.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a bbchausa.