Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Za a rataye mutum biyar da suka yi wa dalibar jami'a fyade da kashe ta a Ilorin

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa

  1. Yarinyar da ta yi fada da kada don tsira da ranta a Mozambique

    Wata yarinya 'yar kimanin shekara tara da haihuwa ta tsallake rijiya da baya bayan ta kaucewa harin wata kada a lardin Chibuto da ke kudancin Mozambique.

    Yarinyar na yin ninkaya ne a wani kogi da ke Limpopo a lokacin da kadar ta far mata.

    Ta shaida wa manema labari cewa a lokacin da ta fuskanci kadar ta kawo mata hari sai ta yi kokari ta karci hancinta wanda a yayin hakan ne ta samu mummunan rauni a daya daga kafafunta.

    Ta ce," Sai da kadar ta ja ni da karfi ta rike ni, ni kuma sai na yi kokari na kai mata duka sannan na karci hancinta,a nan ne da ta ji zafin duka ta sake ni ta wullar dani gefe."

    A yanzu yarinyar na asibiti inda ake kula da ita kuma tana samun sauki.

    Wani likita a asibitin da aka kai yarinyar ya ce wannan ne karo na biyu a cikin shekara guda da aka kai musu marar lafiyar da kada ta jiwa rauni.

    Harin kada a Mozambique ba wani sabon abu bane.

    • ‘Yan-tara na farko a duniya sun koma gida Mali

      Jariran nan ‘yan-tara na farko a duniya da aka haifa lokaci guda sun koma kasarsu Mali lami lafiya.

      Iyayen jariran da ‘ya’yansu sun isa filin jirgin saman Bamako a safiyar ranar Talata inda ministan lafiyar kasar ya tarbe su.

      Tun bayan haihuwar jariran a wani asibiti da ke birnin Casablanca na Morocco, iyayen jariran tare da ‘ya’yansu suka koma wani gida da zama a can.

      A ranar 4 ga watan Mayun 2021 aka haifi jariran.

      Sun shiga cikin kundin tarihi na duniya wato Guinness World Record, saboda kasancewarsu ‘yan tara da aka haifa a lokaci guda da suka rayu.

      Jariran sun kasance mata biyar maza hudu, kuma an same su ne ta hantar dashe, sannan kuma tiyata aka yi wa mahaifiyarsu wajen ciresu.

    • Barkanmu da wannan safiya

      Masu bibiyar wannan shafin ni ce Aisha Shariff Baffa nake muku barka da safiyar Talata.

      Ku kasance da ni tsawon wannan rana domin karanta labaran da suka shafi rayuwarku.

      Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a bbchausa