Za a rataye mutum biyar da suka yi wa dalibar jami'a fyade da kashe ta a Ilorin

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa

  1. Bankwana

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake bankwana da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  2. Kotun Faransa ta samu wasu 'yan kasar da taimakawa harin ta'addancin Nice

    Wata kotu a Faransa ta samu dukkanin mutum takwas da laifi wadanda aka zarga da taimakawa wani ɗan Tunisia kai wani mummunan hari a Nice shekaru shida da suka gabata.

    Mutum 86 aka kashe yayin da daruruwa suka ji rauni a harin, lokacin da wata mota a guje ta abka wa gangamin jama'a da ke bikin ranar Bestille.

    Harin ya kasance daya daga cikin hare-hare manufi muni a Turai.

    Kotun da ke Paris ta zartar wa mutanen hukuncin ɗaurin tsakanin shekara biyu zuwa takwas, kan laifuka da suka shafi mallakar bindiga da alaƙa da ta'addanci.

    Yan sanda ne suka harbe maharin a lokacin da ya kai harin.

  3. Kungiyoyi na nuna damuwa kan hukuncin kisa da aka yankewa ɗan kwallon kafa a Iran

    FIFPRO

    Asalin hoton, FIFPRO

    Kungiyar kwararrun 'yan wasan ƙwallon ƙafa ta bayyana kaɗuwa da damuwa kan wani ɗan wasan ƙwallon Iran Amir Nasr da ke fuskantar hukuncin kisa Iran.

    Nasr - wanda ya wakilaci kasar a gasar yan kasa da shekara 16 - ana zarginsa da wasu mutum biyu da laifin kashe jami'an tsaron Iran .

    Magoya bayansa sun ce dan wasan bai shiga zanga-zangar kin jinin gwamnati ba kuma ba shi da alaka da kisan.

    An dai rataye wasu Iraniya biyu a makon da ya gabata, kuma akwai wasu 11 da aka ruwaito an yankewa hukuncin kisa kan shiga zanga-zagar.

  4. Lai Mohammed ya ce wa Atiku ya daina zargin Buhari kan batun Boko Haram

    Lai Mohammed

    Asalin hoton, FG

    Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed, ya nemi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar, da ya daina ɗora alhakin ruruwar wutar rashin tsaro da ake fama da ita a kan Shugaba Muhammadu Buhari.

    Atiku Abubakar ya bayyana mamakinsa kan yadda har yanzu ƙungiyar Boko Haram tana nan, a wajen wani yaƙin neman zaɓe da ya fita a Abuja a ƙarshen makon da ya wuce.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito a yau cewa Minista Lai ya ce kamata ya yi Atiku ya karkata akalar zarginsa kan jam'iyyar PDP.

  5. An kashe 'yan tawaye 11 a Uganda

    Rundunar sojin Uganda ta ce ta kashe ƴan tawaye 11 da suka tsallako daga gabashin Congo da ke bakwabtaka.

    Kakakin rundunaer sojin kasar ya ce mayaƙa sama da ashirin ne daga ƴan tawayen ADF suka tsallako yankin Ntoroko a daren Litinin.

    Ya ce an kama takwas daga cikinsu, amma an kashe daya daga cikin sojojin Uganda a musayar wuta.

    Yan tawayen dai ba su cika tsallakawa Uganda ba.

    Bayan jerin hare-haren bama-bamai a bara - ciki har da uku da aka kai a Kampla babban birnin kasar - ɗaruruwan sojojin Uganda ne aka baza a gabashin jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo a wani aikin hadin giwa da sojojin Congo domin yakar ƴan tawaye.

    Amma ƴan tawayen sun ci gaba da kai hare-hare.

  6. Majalisa ta bai wa NNPC wa'adin mako guda su kawo karshen wahalar fetur a Najeriya

    Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci kamfanin mai na kasa NNPC ya kawo karshen karancin fetur da ake fama da shi a cikin cikin mako guda.

    A cewar majalisa tsawon watanni 'yan Najeriya na wahalar fetur wanda ke tasiri ga tattali arzikin kasa da jefa al'umma cikin wahala.

    Sannan kamfanin na bijiro da wasu dalilai a matsayin hujjar wahalhalun mai a fadin Najeriya, don haka wanna gargadi ne ga NNPC.

    Umarnin majalisa na zuwa ne bayan a karshen mako hukumar DSS ta bai wa NNPC da kungiyar IPMAN wa'adin sa'o'i 48 su wadatar da mai a fadin Najeriya.

    Tun farkon shekara ta 2022 kusan baa shafe wani lokaci mai tsawo ba tare da 'yan Najeriya sun shiga wahalar fetur ba.

    Ana danganta wannan dalili da nayin farashin dala da kuma rikicin Rasha da Ukraine.

  7. Kotu ta yanke hukuncin rataya kan mutane biyar da suka kashe daliba a Ilorin

    o

    Asalin hoton, others

    Wata babbar kotu a Ilorin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu mutane biyar da aka samu da laifin fyaɗe da kisa kan wata matashiya da ke aji na uku a jami'ar Ilorin na Kwara.

    Alkali Yusuf Adebayo ya kuma wanke mutum uku cikin takwas da aka shigar da kara a kansu kan kisan dalibar.

    Wannan batu ya fito fili ne lokacin da yayar marigayiya Olajide Blessing Omowumi, ta tsincI gawar kanwarta tsirara an ɗaure mata hannu da baki a gidansu bayan ta dawo da ga aiki.

    'Yansanda da ke tabbatar da waɗannan bayanai sun ce nan take aka sanar da su kuma suka ɗau mataki.

    Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya ce irin waɗannan ɗabi'a ba abin lamunta ba ne tsakanin al'ummar jihar kuma dole su cigaba da daukan matakai masu tsauri.

    k

    'Yan sanda sun ce mutanen da suka aikata fyaden da kisan sun bar wasika a kan gawar da ke cewa "Jami'ar Ilorin ba ta yafewa".

    Iyayen marigayiyar dai sun yi mamai lokacin da suka gano cewa cikin mazan da suka aikata wannan danye aiki akwai fuskar sani.

  8. Masarautar Birnin Gwari ta bai wa Tinubu sarauta

    BOLATINUBU

    Asalin hoton, BOLATINUBU

    Sarkin Birnin Gwari da ke Kaduna, Malam Zubair Jibril Maigwari II, ya nada dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin "Dakaren Birnin Gwari".

    Tinubu tare da tawagarsa sun ziyarci Birnin Gwari a daren jiya Litinin domin neman kuri'a a zaben shugabanci kasa da ke tafe a badi.

    A lokacin ziyarar, Sarki ya bai wa Tinubu wannan sarauta.

    An kuma nada gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin Sadaukin Birnin-Gwari

    BOLATINUBU

    Asalin hoton, BOLATINUBU

    BOLATINUBU

    Asalin hoton, BOLATINUBU

    BOLATINUBU

    Asalin hoton, BOLATINUBU

  9. An tsaurara matakan tsaro a Abuja saboda bukukuwan karshen shekara

    NPA

    Asalin hoton, NPA

    Rundunar 'yan sanda Najeriya a Abuja ta tsaurara matakan tsaro da tura karin jami'anta sassa daban-daban na birnin domin tabbatar da tsaro yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan karshen shekara.

    Rundunar ta ce ta tura dakaru na musamman duk yankunan da ke bukatar sa ido domin dakile duk wani yunkurin tada zaune tsaye ko bata-gari, kamar yada kakakin 'yan sanda Josephine Adeh ya tabbatar a sanarwarsu.

    Sannan an garagadi jami'an da su gudanar da aikinsu cikin kwarewa da kaucewa duk wasu halaye da zai bata sunansu ko zubar da mutuncinsu a idon al'umma.

    Sannan su fitar da wasu lambobin kar-ta-kwana da mutane ke iya kira idan sun tsinci kansu cikin wani yanayi.

  10. Asusun lamuni na duniya zai bai wa Ghana taimakon dala biliyan uku

    Kungiyar IMF ta samu yarjejeniya da Ghana a kan Shirin taimako na dala biliyan uku.

    Sabuwar kungiyar da a ka kafa a cikin yarjejeniyar mai suna Extended credit facility za ta yi aiki na shekara uku. An sanar da haka bayan wakilcin IMF sun gama ziyara.

    An kafa kungiyar domin ta gyara tattalin arzikin ghana da kuma biyan bashin Ghana

    Kudun da IMF ta bada da kuma kudin gwamnatin zasu tsaranta bashin kasar .

    A satin baya, kudin ghana mai suna cedi ta fadi gaba da dala bayan kuma ta rasa rabin mahimmancin ta a cikin wannan shekaran.

    A watannin baya, hauwar farashin kaya ta karu da 40% domin haka, kasar na matukar bukatar kudi domin gyara tattalin arzikinta.

  11. Shugabannin Afirka na halartar taron yaukaka dangantaka da Amurka a Washington

    Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Shugabanin kasashen Afrika da na gwamnatoci sama da 40 da manyan ‘yan kasuwa da dama ke halartar wani taro a birnin Washington na yaukaka dangantaka tsakanin Amurka da kasashen Afrika.

    Taron na kwanaki uku da shugaban Joe Biden zai jagorenta, zai mayar da hankali ne kan dagantakar Amurka da kasashen nahiyar Afirka ta bangarori da dama.

    A game da wannan taron mai tarihi, babban sakataran Amurka Antony Blinken, ya jaddada cewa wannan taro zai duba kabali da ba’adin huldodin da ke tsakanin Amurka da nahiyar Afirka.

    Amurka dai ta dage haikan kai da kafa domin ta yi babban tasiri a Afirka ganin yadda China da Rasha da ma sauren kasashen duniya ke ci gaba da yunkurowa a nahiyar.

    Amurka na sa ran taimaka wa kungiyar tarrayar Afirka da ta kasance mamba ta dundundun a cikin kungiyar G-20.

  12. Ukraine na bukatar agajin sama da dala 100

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce kasarsa na bukatar sama da dala miliyan dari takwas na agaji, domin tunkarar matsalar karancin makamashin da hare-haren bama-baman Rasha ya haddasa.

    Galibin yankunan kasar sun kasance babu lantarki, yayin da ake gudanar da wani taron kasashen duniya a birnin Paris, domin tattauna irin taimakon da za a iya bai wa Ukraine.

    Shugaba Zelensky ya shaida wa wakilan taron cewa asibitoci da sauran wurare ba su da karfin ci gaba da amfani da janareto domin samun wutar lantarki.

  13. An tsige mataimakiyar shugabar Majalisar Tarayyar Turai

    Eva Kaili

    Asalin hoton, Reuters

    An tsige mataimakiyar shugabar Majalisar Tarayyar Turai bayan an zarginta da karbar cin hanci da halatta kudin haram, a wata kuri'a da aka kada a majalisar ta turai.

    Eva Kayiili, yar majalisa daga Girka ta musanta karbar cin hanci daga Qatar, domin yin tasiri da kuma kare martabar gwamnatin Doha.

    'Yan sandan Belgium sun gurfanar da ita da wasu mutane uku da ake zargi, bayan wani samame a Brussels inda aka gano makudan kudade.

    Nan gaba a yau ne Majalisar Tarayyar Turai za ta gudanar da muhawarar gaggawa game da badakalar, inda za a yi nazari kan ra'ayoyi da kuma yadda za a kara sa ido tare da tabbatar da gaskiya game da kudaden Tarayyar.

    Qatar dai ta musanta zargin bayar da cin hancin.

  14. Somalia ta kaucewa fadawa cikin bala'in yunwa

    Mata da 'ya'yanta

    Asalin hoton, AFP

    Kididdigar baya-bayan nan game da matsalar karancin abinci a Somalia, ta ce kasar ta kaucewa fadawa cikin bala'in yunwa a bana.

    Sai dai hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji na gargadin cewa har yanzu dubban mutane za su ci gaba da rayuwa cikin kunci da yunwa, kuma galibinsu suna fuskantar mutuwa.

    Masana sun yaba da matakan da aka dauka musamman daga kungiyoyi na cikin gida da na kasa da kasa game da fari mafi muni a Somalia cikin shekaru arba'in.

    Sai dai sun ce matukar ba a samu isassun kayan agaji ba, kasar za ta sake tsunduma cikin matsananciyar yunwa nan da watan Afrilu mai zuwa.

    Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi kira ga masu bayar da tallafi da su gaggauta amsa kiran Majalisar Dinkin Duniya da ta nemi agajin sama da dala biliyan biyu.

  15. WHO ta aika rigakafin cutar kwalara Haiti

    Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce Haiti ta karbi allurar rigakafin cutar amai da gudawa wato kwalara da dama domin shawo kan annobar cutar data barke.

    Akalla mutane fiye da 300 sun rasa ransu tun bayan barkewar cutar a watan Oktoban da ya wuce.

    WHO ta ce nan da wasu makonni masu zuwa za a sake tura wasu karin alluran rigakafin zuwa kasar.

    Za dai a fi mayar da hankali wajen yi wa yara rigakafin musamman a yankunan da cutar tafi kamari a kasar.

    Kasar dai fama da matsaloli da dama ciki har da karancin ayyukan jin kai inda kusan rabin al'ummar kasar ke fama da matsananciyar yunwa.

    Kungiyoyin 'yan daba ne dai ke rike da bangarori da dama na kasar abin da ke shafar kai kayyakin amfani zuwa asibitocin kasar kamar man fetur.

  16. Najeriya ta kawo karshen gwajin cutar korona ga matafiya

    Matafiya

    Asalin hoton, OTHER

    Mahukunta a Najeriya sun ce daga yanzu matafiya sun dai na nuna sakamakon basa dauke da cutar korona idan sun isa ko kuma za su yi tafiya zuwa wata kasa.

    Hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta kasar ta ce an dauki matakin hakan ne bayan tabbatar da cewa a yanzu ba kasafai ake samun wadanda suka kamu da cutar ba a kasar dama sauran kasashen duniya.

    Hukumar ta ce daga yanzu duk wani matafiyi daga gida Najeriya da ma wadanda suka dawo daga wata kasar ba za a bukaci sakamakon gwajin cutar da ya nuna basa dauke da ita ba.

    A baya dai wajibi ne ga duk matafiya suyi gwajin cutar kafin tafiya, haka ma wadanda suka dawo dole su nuna sakamakon gwajin da ya nuna basa dauke da ita.

  17. An gargadi asibitocin Ukraine su tsaya cikin shirin ko-ta-kwana

    Ministan lafiya a Ukraine, ya ce ya gargadi asibitocin kasar da su yi shirin ko-ta-kwana, a yayin da Rasha ke zafafa hare-hare kan ababan more rayuwa da tashoshin makamashin kasar.

    Viktor Lianshko, ya ce yakamata asibitoci su takaita yawan marasa lafiyar da za su rinka kula da su.

    Ya ce daukewar hasken lantarki a wasu sassan kasar sakamakon hare haren Rasha, na nufin ba bu abubuwan dumama daki da ruwan sha da makamantansu.

    Mr Liashko, ya ce tuni suka bukaci abokan huldarsu da su taimakawa asibitocin kasarsu da kayayyakin aiki kamar janareto da abubuwan dumama daki don ci gaba da kula da marasa lafiya ko da kuwa a cikin duhu ne.

  18. Maroko ta baiwa magoya bayanta tikiti dubu 13 domin kallon wasanta da Faransa

    Maroc

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar da ke kula da kwallon Maroko ta siya wa magoya bayanta tikiti dubu goma sha uku kyauta domin kallon wasansu da Faransa a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

    A gobe Laraba za a buga wasan kusa da karshe a tsakanin kasashen biyu bayan Maroko ta kafa tarihi a matsayin kasar Afrika ta farko da ta kai wannan matakin.

    Haka kuma kamfanin jirgin sama na kasar watau Royal Air Maroc ya saka jirage 30 a farashin mai rahusa ga 'yan kallo domin su yi balaguro zuwa Qatar.

    An yi shagulgula sosai a Maroko tun bayan da kasar ta samu galaba a kan manyan kasashen Turai a gasar da Qatar ke daukar bakunci.

    A daya wasan kusa da kashe Argentina ce za ta kara da Croatia a yau Talata.

  19. Mozambique ta kona mayukan da ke haddasa cutar daji

    Mace na shafa mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukunta a Mozambique sun kona kayayyaki da mayukan shafawa dubu 10 da ke da hadari ga lafiyar al'umma bayan ankararwar da Kungiyar Tarayyar Turai ta yi a kansu.

    Mayukan sun hadar da na wanka da wadanda ake wanke kai da kuma na fesawa.

    Mahukuntan sun ce mayukan na dauke da sinaran da ke haddasa cutar daji a cikinsu wanda kuma babban hadari ne ga rayuwar al'umma.

    A watan Satumba ne Kungiyar Tarayyar Turai ta yi gargadi a kan amfani da irin wadannan mayuka.

    Mahukuntan sun ce a yanzu sun tabbatar cewa babu irin wadannan mayuka wadanda ke da hadari a kasuwanni.

    Tuni masu samar da irin wadannan mayuka suka fitar da wasu nau'ukan inda suka turasu hukumar da ke kula da inganci kayyaki ta kasar don tantancesu.

    A Turai dai tuni aka cire duk wasu sinadarai da ke da hadari a cikin mayukan da ake amfani da su.

  20. Ba zan taba tsayawa takarar Sanata ba - El-Rufai

    El-Rufai

    Asalin hoton, OTHER

    Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya ce ba zai taba neman takarar kujerar dan majalisa ba bayan ya bar mulki.

    Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a wani taro da aka yi game da harkokin 'yan majalisa a Abuja.

    Ya ce baya tunanin cewa idan har ya zama Sanata zai iya tabuka wani abin azo a gani saboda yanayin majalisar.

    A shekarar 2015 aka zabi El-Rufai a matsayin gwamna a Kaduna, inda a yanzu yake cikin wa'adinsa na biyu a kan kujerar.

    Ba sabon abu bane tsayawar gwamnonin da suka yi wa'adi biyu a kan mulki tsaya takarar sanata a Najeriya.

    A yanzu haka akwai irin wadannan tsoffin gwamnoni a majalisar Dattawan kasar kamar, Seriake Dickson na Bayelsa da Orji Kalu na Abia da Kashim Shettima na Borno da Tanko Almakura na Nasarawa da Ibrahim Geidam na Yobe da Rochas Okorocha na Imo da Ibrahim Geidam na Yobe da Ibikunle Amosun na Ogun da kuma Abdulaziz Yari na Zamfara.