Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sojin Najeriya sun musanta zargin zubar wa mata ciki a Borno

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi

  1. 'Hankalin ƴan majalisa ya tashi kan sabuwar dokar cire kuɗi ta CBN'

    Majalisar dattijan Najeriya ta ce za ta yi wa shugabannin babban bankin ƙasar (CBN) tambayoyi a kan sabuwar dokar da aka ɓullo da ita ta ƙayyade kuɗaɗen da ake cirewa a kowane mako.

    Dama dai majalisar ta nuna damuwa kan lamarin a zaman da ta yi ranar Laraba, inda ta ce zai yi illa ga masu ƙananan sana’o’i.

    A wata tattaunawa da BBC, sanata Adamu Bukachuwa ya ce "lokacin da muka ji wannan magana hankalinmu ya tashi, masu cin kasuwa irin na ƙauyuka yaushe dubu ɗari zai ishe su a mako."

    Sai dai ƴan majalisar sun ce lamarin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban ƙasa ya tura wa majalisar sunayen mataimakan gwamnan bankin guda biyu domin tantancewa.

    Ya ƙara da cewa za su yi amfani da damar wajen yi wa shugabannin tambayoyi kan sabon tsarin.

  2. Ƴan tawayen Congo sun kashe farar hula sama da 130 - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta samu bayanai kan wani kisan kiyashi da ƴan tawayen M23 suka yi wa fararen hula a ƙarshen watan Nuwamba, a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo.

    Ta ce bincike ya tabbatar da kashe mutUM aƙalla 131 a ƙauyuka biyu, wato Kishishe and Bambo, da ke Rutsuhuru na lardin Kivu.

    MDD ta ce kisan ya kasance tamkar ramuwar-gayya ce a kan hare-haren da dakarun gwamnati ke kai wa ƴan tawayen a baya-bayan nan.

    Ƙungiyar ƴan tawaye ta M23, wadda ta kama garuruwa da dama da ke kan iyakar Rwanda da Uganda ta musanta cewar tana kai hari a kan farar hula.

  3. Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Guatemala hukuncin ɗauri

    Kotu a Guatemala ta yanke wa tsohon shugaban kasar, Otto Perez Molina, da tsohon mataimakinsa Roxana Baldetti, daurin shekara 16 a gidan kaso.

    Kotu ta samu mutanen biyu da laifin cin hanci da rashawa, ta hanyar halasta kuɗaɗen haram, da karbar rashawar miliyoyin daloli a hannun kamfanonin da suke bai wa kwangiloli da kauce wa biyan haraji da kuɗin fito.

    A shekarar 2012 ne aka zaɓi Mr Perez, shugaban Guatemala, amma an tilasta masa murabus a shekarar 2015, lokacin da bayanai suka fito kan wasu gagaruman danbarwar rashawa da aka yi wa laƙabi da "La Linea''.

    Ƴan ƙasar sun kwashe watanni suna zanga-zanga kan danbarwar.

  4. Barka da warhaka

    Masu bibiyar mu a wannan shafi Haruna Ibrahim Kakangi ke maku barka da safiyar Alhamis.

    Za mu rinƙa kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya ta wannan shafi a tsawon wannan yini da yardar Allah.

    Da fatan za ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta domin bayyana ra'ayoyinku kan waɗannan labarai da ma wasu ƙari a facebook, da tuwita, da instagram @bbcnewshausa.

    Za ku iya kallon shirye-shiryenmu na bidiyo a shafinmu na BBC Hausa youtube.