Bankwana
Da haka Umaymah Sani Abdulmumin ke bankwana da ku a wannan shafi sai kuma gobe Juma'a da yardar Allah. A huta lafiya
Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.
Haruna Kakangi
Da haka Umaymah Sani Abdulmumin ke bankwana da ku a wannan shafi sai kuma gobe Juma'a da yardar Allah. A huta lafiya
Wani ƙudiri da ke neman kare auren jinsi a Amurka ya samu amincewa ta ƙarshe daga Majalisar wakilai.
Wannan wani gagarumin ci gaba ne ganin shekarun da aka ɗauka ana ta fafutukar yaƙin neman daidaito.
Ƙudirin a yanzu kawai yana jiran sa hannun Shugaba Joe Biden ne domin ya zama doka.
Shugabar majalisar wakilan Amurka mai barin gado, Nancy Pelosy ke cewa mutum ɗari biyu da hamsin da takwas ne suka goyi bayan wannan ƙudirin, waɗanda suka ƙi amincewa da shi kuwa ɗari da sittin da tara ne a don haka an amince da shi.
Akwai fargabar da aka yi ta nunawa cewa Kotun Kolin ƙasar na iya daƙile yunƙurin tabbatar da dokar kamar yadda ta yi ga dokar zub da ciki.
A watan da ya gabata ne, majalisar dokokin Amurkar ta amince da ƙudirin.

Asalin hoton, DSS
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bai wa kamfanin man NNPC da kungiyar dalilan man fetur ta IPMAN wa'adin sa'o'i 48 su tabbatar da wadatuwar fetur a fadin kasar.
Kakakin DSS, Peter Afunanya, ne ya fitar da sanarwar a Abuja bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkokin fetur.
Sanarwar ta ce NNPC ta tabbatar da cewa tana da wadataccen fetur jibge da zai wadatar da 'yan kasar har bayan bukukuwa karshen shekara.
Ya ce an baza jami'an DSS a kowanne kusurwa na kasar domin hukunta duk maso boye mai ko yiwa harkar samar da mai zagon-kasa.
Sanarwar ta ce irin wannan matsala na fetur da ake haifarwa a kasar na taka rawa wajen sake asasa matsalolin tsaro.
Shugaba Biden ya yi maraba da wani shirin musayar fursunoni da Rasha inda aka yi musayar wata fitacciyar ƴar wasan ƙwallon kwando ƴar Amurka, Brittney Grinerda ɗan Rashar nan, dillalin makamai, Viktor Bout.
Shugaba Biden ya ce ya yi magana da Griner, wadda aka mayar da ita Amurka, inda ya ce tana cikin ƙoshin lafiya.
Wakiliyar BBC ta ce cikin watan Yuli ne, Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi wata sanarwa da ba a saba ji ba cewa sun miƙa shawararsu ga Rasha, wadda yanzu muke sanin kan batun musayar mutanen ce.
Griner, wadda ta lashe lambar zinare sau biyu a gasar Olympics, an tsare ta ne a Rasha cikin watan Fabrairu lokacin da aka gano tabar wiwi a cikin jakunkunanta.
An tisa ƙeyar Viktor Bout zuwa Amurka bayan wani samame da aka kai Thailand a shekarar 2008.

Asalin hoton, LP
Jam'iyyar Labour Party ta Peter Obi ta ce ɗan takararta zai mayar da mafi karancin albashi naira dubu 80 zuwa 100, idan ya yi nasara a zaɓen 2023.
Mataimakin shugaban jam'iyyar, Ayo Olorunfemi, ne ya shaida hakan a lokacin wani tataunawa da tashar Channels.
Olurunfemi ya ce tuni sun soma nazarin tabbatuwar hakan da zaran sun yi nasara domin sauya tsarin dubu 30 da yake gaggara duk da cewa baya biyan bukatun 'yan kasa.
Batun karin albashi na daga cikin alkaura ko bukatu da Peter Obi ke amfani da shi a gangamin yakin neman zabe.
An soma shari'ar da ta shafi wata badaƙala mafi girma a tarihin Jamus wadda ta shafi tsohon shugaban kamfanin hada-hadar kuɗi na Wirecard.
Shari'ar ta Markus Braun da wasu tsaffin jami'an kamfanin na gudana ne cikin wata kotu da aka samar wa cikakken tsaro a harabar wani gidan yari.
Kamfanin na Wirecard ya ruguje shekaru biyu da suka gabata bayan da ya amince cewa babu dala biliyan biyu a asusunsa.
Masu gabatar da ƙara na zargin kamfanin da ƙirƙiro wasu hanyoyin samun kudin shiga domin yaudarar masu zuba jari da masu karɓar rance.
Mista Braun dai ya musanta aikata ba dai-dai ba.

Asalin hoton, BAT
Uwargidan ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a Najeriya, Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa nan gaba kaɗan za a samu ɗan karar shugaban kasa Kirista da mataimakin ɗan takarar shugaban kasa Kirista a shugabancin ƙasar.
Ta bayyana haka a lokacin yaƙin neman zaɓen da mata magoya bayan ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC suka kira wani dandazon mata don tallata cif Bola Ahmad Tinubu.
To sai dai takarar Musulmi da Musulmi a yanzu na ci gaba da tayar da kura a cikin siyasar ƙasar.
Sanata Oluremi Tinubu wadda Kirista ce kuma fasto ta ce wannan tsari da ake kai zai sauya fasalin makomar siyasar Najeriya da manufa mai kyau.
"Allah, Allah ne, Yana saka-wa masu aiki a boye, haka Yana saka mu su a fili. Abin da ke faruwa da Shattima da abin da ke faruwa da mu, Allah shine mai yin Yadda ya ga dama.
"Game da tikitin ɗan takarar shugaban kasa Musulmi da ɗan takarar mataimakin shugaban kasa Musulmi, wannan zai sauya fasalin siyasar kasar nan Najeriya anan gaba."
Ta bayyana hakan dai a lokacin yakin neman zabe na shugaban kasar na jam’iyyar APC a legas sakamakon korafe-korafe da wasu mabiya addinin Kirista da wasu 'yan kasar ke adawa da tsarin uwar jam’iyyar APC da a yanzu ta tsayar da dan takarar shugaban kasa da kuma mataimakinsa Kassim Shattima dukkaninsu Musulmi.
Najeriya mai al'umma sama da mutum miliyan dari biyu dai tana kuma da mabiya manyan addinan nan biyu wato addinin Musulunci da kuma addinin Kiristanci- wanda kusan duk wasu lamura kan harkokin kasar kan ta'allaka su da su.
A shekara ta 1993, Najeriya ta taba gwada tsarin ɗan takarar shugaban kasa da ya samu gagarumin karɓuwa da rinjaye inda marigayi cif MKO Abiola da ga kudu maso yammacin kasar Musulmi da kuma Babagana Kingibe, mataimakin ɗan takarar shugaban kasa wanda shima Musulmi suka tsaya takara a zaɓen da aka dakatar a dab da suna kan hanyar lashe zaɓen kasa.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi mayaƙan M23 da ke Gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kashe fiye da farar hula ɗari da talatin yayin wasu hare-hare da ta kai a makon da ya gabata.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, mayaƙan M23 sun kai hari kan ƙauyuka biyu da ke Gundumar Rutshuru da ke kusa da iyakar Rwanda da Uganda.
A cewar tawagar Majalisar Ɗinkin Duniyar ta MONUSCO, kimanin mata da ƴan mata 27 ne aka yi wa fyaɗe. Sai dai ƴan tawayen sun musanta kashe farar hula.
A farkon makon nan ne, ƙungiyar ta ce a shirye take ta janye daga yankunan da ke ƙarƙashin ikonta bayan ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla.

Asalin hoton, CBN
Majalisar wakilan Najeriya ta soki sabon tsarin Babban Bankin Najeriya wato CBN, na taikata kudin da za a iya cirewa a banki a rana.
Bisa wannan dalili, majalisar ta gayyaci gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ya zo ya mata karin haske da amsa tambayoyi.
A ranar Alhamis din nan ne ya je gaban majalisar kuma ya shaida cewa wannan tsari ba zai yiwu a janye ba, dole a aiwatar kamar yada aka tsara.
Wanan sabon tsari na CBN dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman tsakanin 'yan kasuwa da sauran al'umma da ke ganin za a kware su.
Sai dai masana na ganin wannan wani kokari ne na takaita yawan mu'amala da takardun kudi a hannu da jan hankali mutane su rungumi tsari hada-hadar kudade ta intanet.

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa uku yayin lokacin wani samame da suka kai kan Jenin, da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce sojoji sun shiga birnin domin kama mutanen da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.
Ƙungiyar da ke iƙirarin Jihadi ta Falasɗinawa ta ce mayaƙanta sun yi arangama da sojojin na Isra’ila.
Sojojin Isra’ilar dai na kai samame kusan kullum a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan sakamakon munanan hare-haren da aka kai a ƙasar.
Kusan Falasɗinawa ɗari da hamsin da ƴan Isra’ila ashirin da shida ne suka mutu tun bayan fara yamutsin a wannan shekarar.

Asalin hoton, DAVIDO
An tabbatar da cewa fitaccen mawaki dan Najeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido ko OBO zai yi wasa a bikin kammala wasannin cin Kofin Duniya a Qatar.
Mawakin mai shekara 30 shi ya jagoranci watar taken wasannin na bana da hadin-gwiwar Trinidad Cardona da Aisha, a ranar 18 ga watan Disamba za a rufe gasar.
A lokacin buɗe taron an shirya mawakin zai nishadantar, sai dai hakan bai samu ba sakamakon mutuwar ɗan sa, Ifeanyi Adeleke.
Wannan shi ne taro na farko da Davido zai yi wasa tun bayan mutuwar ɗan sa mai shekara uku, sakamakon nitse a ruwan ninkaya wato suwimin ful.

Asalin hoton, OTHER
Uganda ta karɓi rigakafin cutar Ebola guda 1,200 wadda za a yi amfani da ita domin kariya daga nau'in cutar wadda ta samo asali daga Sudan.
Ya zuwa yanzu dai babu rigakafin da aka tabbatar tana aiki kan irin wannan nau'in cutar.
An samu mutum 142 da suka kamu da cutar, yayin da 55 suka mutu tun bayan ɓallewar cutar a watan Satumba.
Za a bayar da rigakafin ne ga mutane waɗanda suka yi mu'amala da waɗanda suka kamu da cutar.
Masu binciken na sa ran mutum 3,000 ne za su shiga gwajin.
Akwai ƙorafin cewa an kawo rigakafin ne a ƙurarren lokaci.

Asalin hoton, TWITTER/DEFENCEINFONG
Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta mayar da martani kan rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters wanda ya zargi sojojin ƙasar da aiwatar da wani shirin zubar wa matan da mayaƙan Bpoko Haram suka yi wa fyaɗe ciki.
Shalkwatar tsaron ta bayyana rahoton na Reuters a matsayin labarin kanzon kurege.
Tare da cewa wani shiri ne na shafa wa sojojin Najeriyar kashin kaji.
Shugaban sashen yaɗa labaru na shalkwatar tsaron Manjo Janaral Jimmy Akpor ya ce tun daga watan Yulin 2021 har zuwa watan Nuwamban bana mayaƙan Boko Haram sama da dubu 82 tare da iyalansu ne suka yi saranda ga dakarun ƙasar kuma fiye da dubu arba'in daga ciki yara ne.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar Borno ta samar wa tsoffin mayaƙan Boko Haram da iyalan nasu matsugunai domin ba ta son ta raba yaran da iyayensu.
Shalkwatar tsaron ta kuma ƙara da cewa an haifi jarirai 262 a cikin wannan sansani, cikin watanni huɗu.
Rahoton na kamfanin dillancin labaru na Reuters ya yi zargin cewa an tilasta wa mata da yara mata dubu 12 zubar da ciki tun daga 2013 karkashin wani shiri da aka aiwatar cikin sirri.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yawan mace-mace da ake samu sanadiyyar cutar zazzɓin cizon sauro ya ragu a bara, bayan ƙarin da aka samu a shekarar farko na ɓullar korona.
Sai dai a cikin rahoton da ta fitar jiya Alhamis, WHO ta yi gargaɗin cewa akwai ƙalubalen samun sauro waɗanda ke bijire wa maganin kashe ƙwari, da kuma ƙwayar cutar wadda ke bijire wa magani.
Ana samun kashi 95% na masu fama da malariya ne a nahiyar Afirka, inda yara suka fi zama cikin haɗari.
Duk da mayar da hankali da duniya ta yi a kan korona a shekarun nan, yawan waɗanda maleriya ta kashe sun ragu da mutum 6,000.
Sai dai yawan waɗanda suka kamu da cutar ya ƙara yawa kaɗan, inda aka samu mutum miliyan 247 waɗanda suka kamu da ita a shekarar ta 2021.

Asalin hoton, OTHER
Iran ta zartar da hukuncin kisa na farko a kan ɗaya daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnati, wadda ta zamo ƙarfen-ƙafa ga hukumomin ƙasar tun cikin watan Satumba.
An kama Mohsen Shekari da laifin raunata jami'in tsaro na sa-kai da kuma datse hanya a babban birnin ƙasar, Tehran.
Saboda haka ne aka gurfanar da shi bisa zargin yin fito-na-fito da dokokin Allah, wanda hukuncinsa shi ne kisa.
An kai Mr Shekari wani wurin da aka tsare shi kwana biyu gabanin rataye shi.
Aƙalla mutum 11 ne aka yanke wa hukuncin kisa tun bayan zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar sanadiyyar mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini.
Akwai wasu mutum 20 da ke cikin haɗarin fuskantar hukuncin kisa a ƙasar yanzu haka.

Asalin hoton, Getty Images
Jihar Indiana da ke Amurka ta shigar da ƙara a kotu tana tuhumar kamfanin ByteDance wanda ya mallaki manhajar TikTok da nuna wa yara abubuwan da ba su dace ba.
An shigar da ƙarar ce a ranar Laraba ana zargin kamfanin da saɓa dokokin kare masu mu’amala da shi.
Babban mai shari’a na jihar Todd Rokita ya kuma zargi TikTok da ƙin bayyana yiwuwar cewa ƙasar China za ta iya tatsar bayanai ta manhajar.
Inda ya bayyana manhajar a matsayin ‘kura a cikin fatar akuya.’
Ƙarar ta ce tsarin na TikTok na tura wa yara bidiyon da ya ƙunshi shan kayan maye, da ƙwaya, da tsiraici, da lalata da kuma munanan kalamai.
Hauhawan farashin kayan masarufi a Kamaru na sanya mutane zullumi yayin da ake tunkarar ƙarshen shekarar 2022.
A irin wannann lokaci mutane kan tanadi kayan abinci da sutura ga yara kananan domin murnar karshen shekara.
Abincin da aka fi bukata a irin wannan lokaci shi ne shinkafa da kaza da wasu kayan wasan yara.
Sai dai yanzu haka ba kowa ne ke iya samar da waɗannan abubuwan buƙatu ga iyalansa ba.
Kamar sauran ƙasashe, kamaru na daga cikin wuraren da ake fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi saboda matsin tattalin arziƙi na duniya.

Asalin hoton, AFP
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ba zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa ba kasancewar tsayawar za ta zubar masa da ƙima.
A wata tattaunawa da aka yi da shi lokacin bukin ƙaddamar da wani littafi kan rayuwa tsohon limamin cocin fadar shugaban ƙasa, a ranar Talata, Jonathan ya ce ƙaddara ce kawai za ta sanya ya sake zama shugaban Najeriya.
Ya ce amma shi da kansa ba zai taɓa tunanin sake zuwa ya sayi fom sannan ya bi mutane yana roƙon su su zaɓe shi ba.
A baya dai an yi ta raɗe-raɗin cewar tsohon shugaban ƙasar zai sake tsayawa takara a zaɓen 2023.

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan da aka samu daga ƴan’uwa sun ce an sako Oba Clement Omoola Jimoh ne jiya Laraba, inda aka kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.
A makon da ya gabata ne aka sace basaraken, inda ya kwashe mako guda a hannun masu garkuwa da mutane.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ƴan bindigan suka kutsa fadarsa da ke ƙaramar hukuma Akoko ta Yamma a ranar Alhamis ɗin makon jiya, inda suka ɗauke shi zuwa wani wuri na daban.
Daga baya ƴan bindigan sun buƙaci a biya maƙudan kuɗaɗe domin sako shi, sai dai an sulhunta a kan ƙasa da abin da suka buƙata, amma duk da haka ba a fayyace ko sai da aka biya kuɗin fansar kafin sako basaraken ba.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar ta Ondo SP Funmilayo Danlami ta tabbatar da lamarin a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels..

Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon bincike ya nuna cewa jaririn da ke cikin mahaifiyarsa na iya faɗawa haɗari idan mai ciki ta yi aiki a wuri mai zafi sosai.
Binciken ya yi nazari kan mata manoma sama da 90, waɗanda ke aiki a gonakin shinkafa a ƙasar Gambia - mafi yawan lokaci a cikin tsananin zafin rana.
Masu bincike na kwalejin lafiya ta London School of Hygiene sun ce zuciyar ƴan-tayin irin waɗannan mata ta rinƙa bugawa da sauri, wani abu da ya sanya su cikin haɗari.
Kuma sun gane cewa kwararar jini zuwa jikin ɗan-tayin ya ragu saboda matsin da mahaifa ta shiga sanadiyyar yanayin na zafi.
Masana kimiyya sun buƙaci da a ƙara zurfafa binciken a wasu yankunan masu yanayin zafi domin samun ƙarin haske.