'Sojojin Sudan za su miƙa mulki da zarar ƴan siyasa suka cimma matsaya'
Shugaban mulkin soji na Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ce sojoji za su miƙa mulki da zarar ƙungiyoyin farar hula suka cimma matsaya kan kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya.
Burhan ya ce ɓangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar ranar biyar ga watan Disamba, wadda ta ƙunshi batun kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ƙarƙashin farar hula za su kafa kwamitocin samar da kundin tsarin mulkin ƙasar.
Ya ce miƙa mulki ga farar hula ya danganta ne ga lokacin da ƙungiyoyin farar hula za su kwashe wajen samar da matsaya.
Ya kuma jaddada cewa sojoji sun ceci ƙasar ne a lokacin da suka yi juyin mulki na ranar 25 ga watan Oktoban 2021.