Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An zargi sojojin Najeriya da zubar da cikin matan da Boko Haram ta yi wa Fyaɗe

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi

  1. Bankwana

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake sallama da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  2. An saki wanda ya kashe jarumin da ya yaƙi wariyar launin fata a Afrika ta Kudu

    Ma'aikatar shari’a ta Afirka ta Kudu ta tabbatar cewa an saki mutumin da ya kashe Chris Hani, jarumin da ya yi yaƙi da wariyar launin fata a ƙasar.

    Matakin da Kotun Tsarin Mulkin ta ɗauka a watan da ya gabata na sakin Janusz Walus ya janyo cece-kuce da suka a Afirka ta Kudu.

    Matar Mista Hani ta yi kakkausar suka kan matakin. A dai shekarar 1993 ne aka harbe Mista Hani.

    Kisan na shi wani yunƙuri ne da bai yi nasara ba na miƙa mulki hannun farar hula daga mulkin tsirarun farar fata.

    A makon da ya gabata ne, Mista Walus ya samu kulawar likitoci a gidan yari bayan da wani fursuna ya daɓa masa wuƙa.

  3. Yadda 'yan sanda suka kama wasu da ake zargi da shirin hambarar da gwamnati a Jamus

    Ƴan sanda a Jamus sun kai samame sassan ƙasar inda suka kama mutum ashirin da biyar da ake zargi da shirin hamɓarar da gwamnati.

    Kungiyar ta’addancin da ta ƙunshi maza da mata kimanin hamsin, a cewar masu bincike, tana ƙoƙarin kutsawa majalisar dokokin ƙasar don tsige gwamnati.

    Sun yi yunƙurin kafa tasu gwamnatin da kuma majalisar ministoci wadda tuni aka zaɓa daga cikin mabiyansu.

    Wannan ya haɗa da wani likita wanda shi aka tsara zai zama ministan lafiya da wani lauya da zai shugabanci ɓangaren shari’a.

    Bayanai na cewa tsaffi da kuma wasu jami’an rundunar sojin Jamus na daga cikin waɗanda aka ɗauka aiki a ƙungiyar.

  4. Kotu ta yanke hukuncin daurin shekara 12 kan ɗan tsohon shugaban ƙasar Mozambique

    Wata kotu a Mozambique ta yanke wa ɗan tsohon shugaban ƙasar, Armando Guebza da wasu tsaffin jami’an leƙen asiri biyu hukuncin shekara 12 a gidan yari saboda hannu a badaƙalar cin hanci mafi girma da ta taɓa faruwa a ƙasar.

    Alƙalin ya samu Ndambi Guebuza da laifin halalta kuɗin haram da almubazzaranci.

    A ƙarƙashin badaƙalar ce dai aka samar da wasu sabbin kamfanoni da suka karɓi rancen dala biliyan biyu tsakanin 2013 da 2014 ba bisa ƙa’ida ba inda kuma aka yi amfani da kuɗaɗen wajen sayen jiragen ruwan kamun kifi da wasu jiragen sintiri na soji.

    Badaƙalar dai ta sa masu ba da tallafi rage kuɗaɗen da suke bai wa Mozambique abin da kuma ya jefa ƙasar cikin matsalar tattalin arziki.

  5. An shirya taro a Hisba kan kare mata daga cin zarafi

    Wata cibiyar bincike da bunkasa al'amuran jama'a da haɗin gwiwar kungiyar mata musulmai ta Najeriya FOMWAN sun shirya wani gaggarumin taron horas da kwamandojin Hisba a Kano game da rawar da za su taka wajen kare mata da 'yan mata daga cin zarafi.

    Taron na yini uku an gayyaci kwararru kan harkokin shari'a da zamantakewa inda za a koyar da jami'an na Hisba sabbin hanyoyin da su bi don dakile matsalar cin zarafin mata har ma da kananan yara a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

    Cibiyar wadda ke nazari da binciken kan al'amuran da suka jiɓanci ci gaban al'umma da walwala ta ce, al'amarin cin zarafin mata da na kananan yara yana ci gaba da karuwa a tsakanin al'umma.

    Alhaji Ubale Ibrahim Rano babban jami'i a cibiyar bincike, ya ce kasancewar Hisba na gudanar da ayyukan kyautata rayuwar mata da sauran al'umma, yasa suka bijiro da wannan bita.

    Hajiya Aisha Ahmad Hassan shugabar FOMWAN shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, ta ce yanzu babban abin tashin hankali shi ne yadda ake daukar mata da ‘yan mata, da sunan aiki zuwa wasu kasashe amma sai a bige da cin zarafinsu.

    Kwamandojin HIsba daga jihohin Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina da Kebbi da Zamfara da kuma Sokoto ne suka halarci wannan taro.

    Matsalar cin zarafin mata da 'yan mata ta jima tana ciwa al'umma tuwo a kwarya musamman a Najeriya, inda al'amarin ke ci gaba da sauya salo, kwararru na ganin tilas a hada hannu a sauya salon yadda ake tunkarar matsalar.

  6. An zargi sojojin Najeriya da zubar da cikin matan da Boko Haram ta yi wa Fyaɗe

    Kamfanin dilancin labaran Reuters ya ce ya samu shaidu da ke tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun rinka ɓarar da juna-biyu ga mata na tsawon shekara 9, musaman mata da Boko Haram ke yi wa ciki.

    Galibin waɗannan matan Boko Haram ne suka yi garkuwa da su da kuma yi musu Fyaɗe a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

    Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta wannan zargi.

    Rahoto na Reuters na cewa shirin na ɓarar da cikin mata - akalla mata dubu 10 aka ɓararwa ciki ba tare da amincewarsu ba.

    Reuters ya tattauna da mata 33 da 'yan mata da suka shaida yada aka tilasta cire musu cikin da suke ɗauke da shi, a lokacin da suke riƙe a hannun sojoji.

    Matan sun ce ana yi musu allurai da ɗura musu magunguna ɓarar da ciki.

    Kafar labaran ta kuma tattauna da wasu jami'an kiwon lafiya biyar da na tsaro 9 da ake gudanar da wannan aikin da su.

    An dai ɓarar da galibin wannan ciki ne a cikin watan Nuwamban bara.

    Sai dai kamfanin labaran bai iya tantace ko tabbatar da sojojin ko gwamnatin da ta kirkiri wannan shiri na ɓarar da cikin matan ba.

    A makon da ya gabata, kafin fitar da wannan rahoton, ma'aikatar tsaron Najeriya tayi fatali da binciken Reuters tana mai cewa babu gaskiya a ciki, kuma cin mutunci ne ga al'ummar Najeriya da al'adunsu.

  7. Saudiyya ta tarbi Shugaban China Xi Jinping

    Saudiyya ta tarbi Shugaban China, Xi Jinping inda aka dasa tutar Sin a titunan Riyadh gabanin isowar babban baƙon.

    Wannan ce ziyara irinta ta farko da Mista Xi zai kai Saudiyya cikin shekara shida.

    Shugaba Xi zai gana da Sarki Salman na Saudiyya da Yarima mai jiran gado, Muhd Bn Salman.

    Ana kuma sa ran za a ƙulla yarjejeniyoyi da dama kan fasaha da wataƙila kan makamai.

    China dai tuni ta zama babbar abokiyar kasuwancin Saudiyya kuma ƙasashen biyu na son sake ƙarfafa alaƙarsu ta tattalin arziki.

    Tun asali Saudiyya na da alaƙa ta ƙut da ƙut da babbar abokiyar hamayyar China wato Amurka.

    A watan Yuli ne Shugaba Biden ya kai ziyara Saudiyyan domin neman Yarima Muhd Bn Salman ya ƙara yawan man da suke samarwa – buƙatar da yaƙi amincewa da ita.

  8. EFCC ta yi gwanjon motoci sama da 400

    Hukumar EFCC da ke yaƙi da rashawa ta soma gwanjon motoci 435 na kwanaki biyu da tace za ta aiwatar bisa tsari da dokokinta.

    EFCC ta ce zata yi gwanjon motoci ne da ke ofisoshinta da manyan cibiyoyi. Galibin wadannan motoci a Legas suke, kuma sun hada da manya da kananan motoci.

    Ma su sha'war motoci na da damar kwada sa'arsu a inda za a ji gwanjon.

  9. Masu gidan burodi sun fara yajin aiki a Tunisiya

    Dubban masu gidajen burodi sun fara yajin aiki a Tunisiya saboda gazawar gwamnati na biyan kuɗin tallafi cikin sama da shekara guda.

    Masu gidajen burodin sun ce suna bin gwamnati bashin kusan dala miliyan 80.

    Wannan matakin na zuwa ne bayan irin sa da masu sana'ar suka ɗauka a watan Oktoba, inda suka janye yajin aikin bayan cimma wata yarjejeniya, wadda suka ce gwamnatin ta gaza cikawa.

    Ƙarancin burodi al'amari ne da kan iya tayar da hatsaniya a Tunisia, ƙasar da ta fuskanci jerin zanga-zanga a baya saboda ƙarancin abinci da rashin kayan more rayuwa.

  10. Hukumar NCC ta gargaɗi 'yan Najeriya kan ɗaura bidiyo a TikTok

    Hukumar kula da kofofin sadarwa ta Najeriya, NCC ta garagdi 'yan Najeriya kan shiga gasar naɗar wani bidiyo da ake ɗaurawa a shafin TikTok, suna cewa ana iya satar bayanan mutanen.

    TikTok ya kasance shafi da ke samun gagarumin karɓuwa da haɓɓaka a Najeriya, musamman tsakanin matasa.

    Gasar naɗar bidiyon da ake kira 'Invisible Challange' a turance ya kunshi naɗar bidiyon tsiraici sannan a jirkita a shafin ta yada ba za a iya gane mutum ba.

    A wata sanarwa, hukumar NCC ta ce ɓata-gari na hawa shafin inda suke ɗaura ire-iren waɗannan bidiyoyi dauke da adireshin da za a latsa domin kwaikwayo ko jirkita hoto ya koma irin nasu.

    Sai dai da zaran mutum ya latsa wannan adireshi hakan zai bai wa masu kutse damar tattara bayanan wayoyin mutane, ta hanyar aike sako biros da ake kira WASP ko W4SP mai haɗari.

    Hukumar ta ce ta irin wannan hanya ake yiwa duk waɗanda suka shiga wannan gasa kutse da tattare duk wasu bayanansu na sirri da imel.

    Sannan wannan biros ɗin a cewar NCC na tattare har da bayanan hotuna da bidiyo da duk wani abu da ke cikin waya.

    Da haka ake yi wa 'yan Najeriya gargaɗi kan gujewa irin waɗannan adireshi da kuma yawaita duba wayoyi ko kamfutocinsu da tsaftace manhajarsu a kai-a kai.

  11. Taliban ta fara zartar da hukuncin kisa a Afghanistan

    Ƙungiyar Taliban ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa karon farko tun bayan da ta ƙwace mulki a Afghanistan a shekarar da ta gabata.

    A cikin wata sanarwa, Taliban ta ce an kashe wani mutum mai suna Dajmir, saboda ya amsa laifin yin kisa.

    Kakakin ƙungiyar ya ce an aiwatar da hukuncin ne a wani filin ƙwallon ƙafa da ke Lardin Farah a Kudu Maso Yammacin ƙasar.

    Wasu manyan jami’an gwamnati sun halarci wajen ciki har da ministan harkokin cikin gida da ministan harkokin waje.

  12. An saki mutumin da ya kashe mai yaƙi da wariyar launin fata a Afirka ta kudu

    Ma’aikatar shari’a ta Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa an saki mutumin da ya kashe Chris Hani, jarumin da ya yi yaƙi da wariyar launin fata a ƙasar.

    Matakin da Kotun Tsarin Mulkin ta ɗauka a watan da ya gabata na sakin Janusz Walus ya janyo cece-kuce da suka a Afirka ta Kudu.

    Matar Mista Hani ta yi kakkausar suka kan matakin.

    A dai shekarar 1993 ne aka harbe Mista Hani.

    Kisan na shi wani yunƙuri ne da bai yi nasara ba na miƙa mulki hannun farar hula daga mulkin tsirarun farar fata.

    A makon da ya gabata ne, Mista Walus ya samu kulawar likitoci a gidan yari bayan da wani fursuna ya daɓa masa wuƙa.

  13. Majalisar dattijai ta buƙaci CBN ya yi taka-tsantsan kan ƙayyade cire kuɗi

    Wasu ƴan majalisar dattijan Najeriya sun nuna fargaba game da matakin babban bankin ƙasar na taƙaita kuɗin da al'umma za su iya cirewa daga asusun ajiya.

    Shugaban marasa rinjaye na majalisar Phillip Aduda ya janyo hankalin wakilan majalisar kan cewa matakin na CBN zai yi illa ga al'umma musamman ma masu ƙananan sana'o'i.

    A nasa tsokacin, shugaban majalisar sanata Ahmed Lawan ya ja hankalin bankin na CBN da ya yi nazari kan lamarin kafin yanke hukunci kai-tsaye, kasancewar matakin zai shafi mutane da dama.

    Ya kuma ce akwai buƙatar a tattauna da bankin domin samun cikakken bayani kan tsarin, sannan ya buƙaci kwamitin kula da harkar bankuna na majalisar ya tattauna kan batun a lokacin zaman tantance mataimakan shugaban bankin, wanda ake sa ran yi a mako mai zuwa.

    A ƙarƙashin sabon tsarin na CBN, ɗaiɗaikun mutane na da damar cire naira 100,000 ne kacal a mako, yayin da kamfanoni za su iya cire naira 500,000 a mako.

  14. ICPC ta kama mawaƙin Najeriya D’Banj kan badaƙalar N-Power

    Hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC a Najeriya ta ce ta kama mawaƙin nan mai suna Oladipo Daniel Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’Banj kan wani bincike da take yi wanda ya shafi kuɗaɗen shirin N-Power.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ta kama D’Banj ne saboda ya ƙi martaba gayyatar da hukumar ta yi masa game da batun.

    Sanarwar ta ce ta gayyaci kimanin mutum 10 a cikin watannin da suka gabata a kan binciken da take yi game da badaƙala ta kuɗin N-Power, kuma tuni ta sake su, sai dai ta riƙe D’Banj bayan da ya kai kansa babban ofishin hukumar da ke Abuja a ranar Litinin saboda ƙin martaba gayyatar da ta yi masa a baya.

    ICPC ta ce yanzu haka mawaƙin na tsare a ofishinta kuma yana taimakawa a wajen binciken da ake yi.

    Ta kuma ce za ta tabbatar an hukunta duk mutane ko bankuna da suka taimaka wajen badaƙalar.

  15. Kotu ta ɗaure ɗan tsohon shugaban Mozambique shekara 12, Jose Tembe

    Wata kotu a Mozambique ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 12 a kan ɗan tsohon shugaban ƙasar da wasu mutanen saboda samun su da hannu a harkar rashawa.

    Ndambi Guebuza, wanda ɗa ne ga tsohon shugaban ƙasa Amando Guebuza, an yanke masa hukuncin ne tare da tsoffin shugabannin tattara bayanan sirri na ƙasar guda biyu, Gregorio Leao da Antonio do Rosario.

    Haka nan sauran mutum takwas waɗanda ke da hannu kan badaƙalar sun samu hukuncin ɗauri na tsakanin shekara takwas zuwa 12.

    Tun farko an gurafanar da mutane 19 ne a gaban kotu bisa zargin su da hannu a wata gagarumar badaƙala da ake wa taken 'tuna bonds', wadda ita ce badaƙalar kuɗi mafi girma da aka taɓa samu a ƙasar.

    Badaƙalar ta ƙunshi batun ciyo bashin kuɗi sama da dala biliyan biyu daga bankuna na duniya, kuma an ciyo yawancin bashin ne ba tare da izinin majalisar ƙasar ba, wani abu da ya sanya tattalin arziƙin ƙasar cikin ƙaƙa-ni-ka-yi.

    An wanke takwas daga cikin waɗanda aka gurfanar ɗin bisa rashin isassun hujjoji.

  16. Gobara ta ƙona tankokin dakon mai biyar a Kano

    Wata gobara da ta tashi ranar Talata a Kano ta ƙone tankokin dakon mai biyar waɗanda ke ɗauke da mai, mai yawan lita 20,400.

    Bayanai daga hukumar kashe gobara ta jihar sun ce lamarin ya faru ne a wani gini da ake amfani da shi a matsayin rumbun adana mai a Farawa Kwanar Yashi da ke babban birnin jihar.

    Mai magana da yawun hukumar ya ce ba a samu rasa rai ba a lokacin gobarar, sai dai wasu mutum uku na samun kulawa a asibiti.

    Bayanan sun nuna cewa gobarar ta tashi ne daga wani ƙaramin janareto da ake amfani da shi wurin samar da wutar lantarki a ginin.

  17. Ghana za ta fara tura wa Birtaniya malaman jinya

    Gwamnatocin Ghana da Birtaniya za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar tura malaman jinya daga Ghana zuwa Birtaniya, wani abu da zai sanya Ghana ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga da suka kai fan 1,000 a kan kowace malamar jinya ɗaya.

    Ministan lafiya na ƙasar, Kweku-Agyeman-Manu ya shaida wa majalisar dokokin Ghana cewar "muna gab da sanya hannu kan yarjejeniyar, ciki har da waɗanda karatunsu ya tsaya a (ƙaramin) satifiket, za su je su samu horo sannan su dawo gida bayan shekara uku."

    A 2020 ma Ghana ta tura malaman jinya 100 zuwa tsibirin Barbados domin tallafa wa ƙasar wadda ke fama da ƙarancin malaman lafiya.

    A baya dai shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya ce ƙasar na da wadatattun malaman jinya, har ma da rara, amma tura su asibitocin gwamnati na da wahala.

    Sai dai shugabar ƙungiyar malaman jinya da ungo-zoma ta Ghana, Perpetual Ofori-Ampofo ta shaida wa BBC cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin malaman jinya da za su yi aiki a asibitocin ƙasar.

    Ghana na da malaman jinya masu rajista kimanin 120,000, amma kashi 46% ba su da babbar takardar karatu.

  18. Ƴan bindiga sun sace mai yi wa ƙasa hidima a Abuja

    Ƴan bindiga sun kashe wata mata tare da yi awon-gaba da wata mai yi waƙasa hidima, da kuma wasu mutunen a unguwar Kubwa da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

    Lamarin ya faru ne a ranar Talata sa’ilin da ƴan bindigan suka kai hari tare da kwashe matasan takwas.

    Bayanai sun ƙara da cewa mutane da dama sun tarwatse a lokacin da aka kai harin.

    Wani shaida ya faɗa wa jaridar Punch cewa da farko mutum goma ne ƴan bindigan suka kwasa, sai dai biyu daga cikinsu sun tsere a lokacin da ake tafiya da su cikin daji.

    Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun rinƙa yin harbi a daidai lokacin da suka isa domin tsorata mazauna yankin.

  19. An mayar da lantarki a Tigray bayan fiye da shekara ɗaya cikin duhu

    An mayar da wutar lantarki a Mekelle, babban birnin yankin Tigray bayan sama da shekara ɗaya a cikin duhu.

    Wasu majiyoyi a yankin sun shaida wa BBC cewa yanzu haka lantarkin ta dawo a faɗin birnin.

    Wani mazaunin birnin ya ce "akwai wuta a duk faɗin garin tun daga jiya."

    Ranar Talata kafar yaɗa labaru ta Fana Broadcast mai alaƙa da gwamnati ta ce wannan ne karon farko da aka dawo da ƙarfin wutar lantarki a birnin bayan shekara guda.

    Kafar ta tuwaito mai magana da yawun kamfanin lantarki na Habasha, Moges Mekonnen na cewa an dawo da wutar ne bayan aikin da aka yi a kan wani layin wuta mai ƙarfin 230kv.

    Haka nan rahotannin sun ce an dawo da harkar sadarwa a yankin Shire da wurare masu maƙwaftaka.

    Hanyoyin sadarwa da na wutar lantarki sun katse ne a yankin bayan da yaƙi ya ƙazance a watan Nuwamban 2020.

  20. NCC ta gargaɗi masu TikTok kan shiga gasar bidiyo

    Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa a Najeriya - NCC ta yi gargaɗin cewa mutane za su iya shiga cikin haɗari idan suna shiga cgasar bidiyo na TikTok, inda ta ce za su iya faɗawa tarkon masu satar bayanan jama'a ta intanet.

    Hakan na kunshe ne a cikin shawarar da NCC ta bayar inda ta ƙara da cewa masu kutse a intanet za su iya amfani da gasar ta TikTok wanda ake kira ‘Invisible Challenge’ wajen yaɗa manhajar satar bayanai ta intanet da ake kira WASP ko W4SP.

    Ta ƙara da cewa za a iya satar sunan mutum da lambobinsa na sirri da harkokinsa na kuɗi ta hanyar amfani da dabaru na zamba a intanet.

    TikTok na da matukar farin jini a Najeriya musamman a tsakanin matasa.

    Shafin TikTok shi ne na tara a farin jini a tsakanin shafukan soshiyal midiya a Najeriya kuma hukumomin ƙasar ba su sanya wa shafin ido ba.