Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

INEC ta roƙi ƴan Najeriya su kare ofisoshinta a faɗin ƙasar

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi

  1. Haɗarin mota ya kashe mutum 33 a Colombia

    A ƙalla mutum 33 ne suka mutu lokacin da wata katuwar motar safa da wasu motoci sukai taho-mu-gama sakamakon zabtarewar kasa a Colombia.

    Manyan duwatsun da suka haifar da haɗarin sun gangaro ne daga tsaunukan da ke yankin yammacin Risaralda.

    An yi gaggawar kwashe mutane daga yankin, inda ministan cikin gida Alfanso Prada, ya jagoranci ma'aikatan ceto domin ci gaba da neman wadanda suka tsira.

    Ruwan saman da aka rinƙa sheƙawa a Colombia ya janyo rashin kyawun yanayi da zabtarewar ƙasa da ambaliyar ruwa.

  2. Iran ta rataye mutum huɗu bisa zargin alaƙa da Isra’ila

    Iran ta rataye mutum huɗu waɗanda ake zargin su da yi wa hukumar leƙen asiri ta Isra’ila aiki.

    Kamfanin dillancin labaru na Mizan ya ruwaito cewar an zartar da hukuncin ne a ranar Lahadi.

    A Larabar makon jiya ne kotun ƙolin ƙasar ta tabbatar da hukuncin kisan a kan mutanen waɗanda aka kama a cikin watan Mayu.

    Haka nan an yanke hukuncin ɗauri na shekara biyar zuwa goma a kan mutane da aka samu da saɓa dokar ƙasa, da garkuwa da mutane da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

    Iran da Isra’ila dai ƙasashe ne biyu waɗanda ba su ga-maciji da juna.

    Wannan hukunci ya zo ne yayin da ƙasar ta Iran ke ci gaba da fama da masu boren adawa da gwamnati.

  3. Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda uku a jihar Sokoto

    Ƴan bindiga sun kutsa kasuwar wani ƙauye da ake kira Yar Bulutu da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto inda suka hallaka ƴan sanda da fararen hula.

    Bayanai sun ce an cikin mutanen da aka kashe akwai ƴansanda uku da kuma fararen hula.

    Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar kudancin Sabon Birni a majalisar dokokin jihar Sokoto ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun isa ƙauyen ne a kan babura kimanin 20.

    Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kuma ƙona mota tare da gawarwakin ƴansandan da suka kashe.

    Sabon Birni na daga cikin yankunan jihar Sokoto da ke fama da hare-haren ƴan bindiga, masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

  4. An kashe ma'aikatan kamfanin mai biyar a Afghanistan

    Ƴan sanda a Afghanistan sun tabbatar da mutuwar mutane biyar a wani hari da aka kai wa ma'akatan wani kamfanin mai da ke cikin motar Bus kan hanyarsu ta zuwa wurin aiki.

    Lamarin dai ya faru ne a yankin arewacin kasar ta Afghanistan.

    Rahotanni sun bayyana cewa wasu ma'aikatan huɗu sun ji mummmunan rauni.

    Mai magana da yawun ƴan sandan yankin Balkh, ya ce hatta motar da harin ya rutsa da ita ta kamfanin mai na Hairatun ne.

    A baya-bayan nan dai ana yawan kai hare-hare a biranen Afghanistan, yawanci kuma kungiyar masu kaifin kishin islama ta IS ke daukar alhakin kai wa.

  5. Indonesia ta amince da dokar tsaurara hukunci kan masu zina

    Ƴan majalisa a Indonesia, sun amince da sabuwar dokar da ta haramta jima'i kafin aure, inda yanzu hakan ya zamo babban laifi, wanda aka samu da lifin ka iya zaman kason sama da shekara guda.

    Dokar dai ta shafi ƴan ƙasa da baki na ƙasashen waje kamar ƴan yawon buɗe ido.

    A ƙarƙashin sabuwar dokar laifi ne jima'i kafin aure, wanda za a iya yankewa mutum hukuncin sama da shekara, kuma an haramta daduro kafin aure.

    Sannan an bai wa iyaye ko ma'aurata damar kai rahoto idan ɗansu ya aikata laifin, ko mata ko miji domin ayi musu hukunci.

  6. Barka da warhaka

    Masu bibiyar mu a wannan shafi Haruna Ibrahim Kakangi ke maku barka da safiyar Talata.

    Za mu rinƙa kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya ta wannan shafi a tsawon wannan yini da yardar Allah.

    Da fatan za ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta domin bayyana ra'ayoyinku kan waɗannan labarai da ma wasu ƙari a facebook, da tuwita, da instagram @bbcnewshausa.

    Za ku iya kallon shirye-shiryenmu na bidiyo a shafinmu na BBC Hausa youtube.