Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ba za mu ƙara kuɗin man fetur ba a yanzu - Gwamnatin Najeriya

Wannan shafi na kawo maku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Babu wanda zai kada kuri’a sai ya na da PVC - INEC

    Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta jaddada cewa babu wanda za a bari ya jefa kuri’a a babban zaben kasar mai zuwa sai ya nuna katin zabe na dindindin.

    Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da taron sabbin kwamishinonin zabe na hukumar, wanda aka yi ranar Laraba a Legas.

    Mahmud ya bukaci al’ummar kasar da su yi watsi da jita-jitar da ke cewa mutum na iya kada kuri’a a ranar zabe ba tare da katin na PVC ba.

    Ya ce sashe na 47(1) na dokar zabe ta 2022 ta ce duk wanda zai kada kuri’a zai gabatar da katin zabensa ga jami’in zabe domin tantancewa a runfar zaben da ya yi rajista.

    Saboda haka ya ce dokar ba ta sauya ba, wajibi bin e duk wanda zai kada kuri’a ya gabatar da katin zaben sa ga jami’an zabe.

  2. An mika bayanin harajin da Trump ke biya ga majalisa

    Baitul-malin Amurka ya mika wa wani kwamitin majalisar dokokin kasar takardun da ke kunshe da bayanan harajin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ke biya.

    Hakan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yanke ne a makon da ya gabata, inda ta bayar da umarnin bai wa kwamitin da 'yan jam'iyyar Democrat ke jagoranta takardun, na tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2020.

    Wani kakakin Baitun-malin ya ce hukumar ta bi umurnin kotun amma kuma ya ki ya ce uffan game da cewar ko takardun sun kai ga hannun 'yan kwamitin zuwa yanzu.

    Mista Trump ne shugaban Amurka na farko a cikin shekara arba'in da ya yi kememe ya ki bayar da takardun harajinsa.

    Ya kafe cewa kwamitin na neman yi masa bita-dakullin siyasa ne kawai.

  3. Bata-gari sun kashe mutum 12 a Haiti

    Wasu da ake zargin 'yan wata kungiya ne ta bata-gari a Haiti sun kashe akalla mutum 12 a wani kauye da ke arewa da babban birnin kasar Port-au-Prince, suka kuma cinna wa gawarwakin wuta.

    Wasu rahotanni sun ce miyagun sun kai hari ne kan mutanen a kauyen Source Matelas, bayan da mutanen suka fara hada kungiyar 'yan sintiri domin kare kansu.

    Magajin garin ya bukaci kasashen duniya da su taimaka wa kasarsa yakar kungiyoyin 'yan daba da sauran miyagu.

    Daman tuni ita ma gwamnatin kasar ta mika irin wannan roko ga kasashe da hukumomin duniya kan su taimaka mata.

    Sai dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza cimma matsaya kan tura jami'an tsaro kasar ta yankin Karebiya ( Caribbean).

  4. Barka da warhaka

    Masu bibiyan mu barka da shigowa wannan shafi namu na kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.

    Ni Haruna Ibrahim Kakangi zan rika kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma fadin duniya.

    Ku je shafukanmu na sada zumunta a facebook, da tuwita da kuma instagram domin tofa albarkacin baki kan labaran da muka kawo maku.