Mata za su sami kashi ɗaya bisa uku na kujerun majalisar dokoki a saliyo
Majalisar dokokin Saliyo ta amince da murya ɗaya, wata doka da za ta tabbatar wa mata kashi ɗaya bisa uku na kujerun majalisar dokokin ƙasar, tare kuma da samar wa matan kashi ɗaya bisa uku na kujerun kansiloli a fadin ƙananan hukumomin ƙasar.
A yanzu za a miƙa ƙudurin dokar ga shugaban ƙasar Julius Bio domin ya sanya hannu ya zama doka.
Duk da cewa ƙudurin na daga cikin manyan alƙawuran yaƙin neman zaɓe a 2018. Majalisar ta ɗauki shekara uku kafin ta amince da ita.
A yanzu haka dai mata 19 ne kawai a majalisar dokokin mai mambobi 146.