Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mahaifiyar Ummita ta ba da shaida a gaban kotu kan zargin Ɗan China da kisan ƴarta

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Limaman Kaduna za su gana da ƴan takaran gwamnan jihar

    Majalisar malamai da limaman addinin musulunci a jihar Kaduna ta ce za ta gana da ƴan takarar gwamnan jihar domin fahimtar manufar kowane daga cikin su.

    Mataimakin shugaban majalisar, Imam Musa Tanimu ne ya bayyana haka ranar Laraba, lokacin da ya gana da manema labaru a jihar ta Kaduna.

    Ya ce tattaunawar za ta samar wa al’ummar musulmin jihar alƙibla domin ganin sun zaɓi shugabanni masu gaskiya.

    A tattaunawarsa da BBC, Imam Tanimu ya ce sun aika da saƙon gayyata ga ƴan takaran gwamna na jam’iyyu biyar domin halartar tattaunawar, wadda za a yi a ranar Asabar 19 ga watan Nuwamba.

    Sai dai ya bayyana cewa malaman ba su da aniyar bayyana goyon baya ga kowane ɗan takara.

    Ya buƙaci ƴan takaran da su halarci tattaunawar domin fayyace manufofinsu ga al’umma.

  2. Tinubu ya gana da ƙungiyar kiristoci ta CAN

    Ɗan takaran shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressive Congress, Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da zargin cewar ba ya martaba addinin kirista.

    Zaɓen da Bola Tinubu ya yi wa tsohon gwamnan jihar Borno sanata Kashim Shettima ya janyo muhawara mai zafi a Najeriyar, kasancewar dukkaninsu mabiyan addinin musulunci ne.

    Wasu na ganin hakan tamkar rashin adalci ne ga sauran mabiya addinai a ƙasar mai mutane masu addinai da yare daban-daban.

    A wata ganawa da ya yi da shugabannin ƙungiyar ta CAN ranar Laraba, ya ce zaɓen da ya yi wa Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ba ya da alaƙa da addini.

    Ya ce “na zaɓi Shettima ne saboda ina tunanin wanda zai taimaka min wajen tafiyar da mulki.”

    Ya ƙara da cewa “ban ce babu mutumin kirki mabiyin addinin kirista da zan iya ɗauka a matsayin mataimaki ba, amma abin da muke buƙata a yanzu shi ne samun mafita ga matsalolinmu.”

    Ya kuma soki waɗanda ke yi masa kallon mai tsattsauran ra’ayin addini.

  3. Wani ƙaramin soja 'da ya sha giya' ya kaɗe babban janar da mota har lahira a Lagos

    Wani ƙaramin soji ya hallaka wani babban janar na sojojin Najeriya da mota.

    Lamarin ya faru ne a barikin sojojin Najeriya da ke unguwar Oshodi a birnin Lagos.

    Lamarin dai ya faru ne a kusa da barikin sojojin a lokacin da babban sojin ya fito daga wurin motsa jiki.

    Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ruwaito wata majiya da ta ce karamin sojin a buge yake da giya a lokacin da ya kade babban sojan.

    Tuni dai aka tsare ƙaramin sojan a barikin domin gudanar da bincike.

  4. Gini mai hawa bakwai ya kashe mutum uku a Kenya

    Aƙalla mutum uku ne suka mutu bayan da wani gini ya rufta kansu a Nairobi, babban birnin Kenya.

    Haka nan kuma ana ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo mutum 10 waɗanda ake kyautata zaton cewar leburori ne waɗanda ginin ya danne.

    Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu an ceto mutum shida, daga ginin mai hawa bakwai, wanda ake cikin aikin ginawa.

    Wata jaridar cikin gida ta ƙasar ta ce sau biyu mai kula da aikin ginin yana ƙin bin shawarar dakatar da ginin, bayan da aka nuna damuwa game da rashin tsayawar ginin yadda ya kamata.

    Ba a cika samun yawaitar rushewar gine-gine ba a birnin na Nairobi.

  5. Sojoji sun kashe riƙaƙƙen ɗan bindiga Kachalla a Kaduna

    Gwamnatin jihar Kaduna ta ce dakarun Najeriya sun hallaka riƙaƙƙen ɗan bindiga Kachalla Gudau.

    Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook.

    Sanarwar ta ce Kachalla Gudau na daga cikin ƴan bindiga da suka addabi yankunan ƙananan hukumomin Chikun, da Kachia.

    Ta ƙara da cewa an samu nasarar kashe ɗan bindigan ne ranar Lahadi, sakamakon samamen da sojoji suka kai a wasu dazuka na jihar.

    Aruwan ya ce an gano gawar Kachalla ne a dajin Kankomi inda ya mutu sanadiyyar zubar jini bayan raunukan da ya samu.

  6. Mahaifiyar Ummita ta bayar da shaida a gaban kotu kan zargin Ɗan China da kisan ƴarta

    An fara gabatar da shaidu a shari'ar dan kasar China nan wanda ake zargi da kashe matashiyar nan Ummita a gaban wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

    Masu gabatar da kara su suka fara shiga da shaidun su inda a yau aka saurari mutum biyu, ciki har da mahaifiyar marigayiyar.

    A zaman babbar kotun na yau, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ne ya ci gaba da sauraren tuhumar da ake yi wa Mista Geng Quangrong da kashe tsohuwar budurwarsa Ummulkhulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.

    Hajiya Fatima Zubairu mahaifiyar Ummulkhuksum da kuma Asiya Sani, su ne shaidun, kuma sun yi wa kotu bayanin abin da suka sani game da zargin da ake yi wa Mista Geng.

    Hajiya Fatima, ta faɗa wa kotun cewa a ranar 16 ga watan Satumbar 2022 Mista Geng Quangrong ya je gidansu inda ya yi ta buga kofa, bayan da suka bude kofar a cewarta, sai ya shiga dakin Ummita ya kulle kofar, da kuma ta leka ta taga sai ta ganta cikin jini, al’amarin da yasa ta fita waje neman a kawo musu dauki.

    Barista Muhammad Balarabe Dan Azumi shi ne lauyan Mista Geng, ya kuma yi wa Hajiya Fatima da Asiya Sani tambayoyi a gaban kotun.

    Lauya mai gabatar da kara kuma kwamishinan Shari'a na jihar Kano Musa Abdullahi-Lawan shi ya jagoranci lauyoyin gwamnati a zaman kotun.

    An shafe sa’o’i ana zaman saboda musayar bayanai da tambayoyi da aka riƙa yi wadanda suka dauki hankali sosai, abin da yasa har hutu aka ta fi har sau biyu.

    Alkalin babbar kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage zaman zuwa gobe da kuma jibi juma’a inda ake fatan ci gaba da sauraren shaidu.

  7. Ba za mu sauya matsayinmu ba kan ASUU - Ministan Ilimi

    Yayin da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami'o'in ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.

    Ministan ilimin ƙasar Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami'ar ma'aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.

    “An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi'', in ji Adamu Adamu.

  8. Saurari labaran minti ɗaya na rana

    Labaran minti ɗaya na rana tare da Sadiqa Bekeke da Abdullahi Bello

  9. An kashe mutum 11 a wani hari da aka kai jihar Plateau

    Akalla mutum 11 ne suka mutu a ƙauyen Maikatako a gundumar Butura da ke yankin ƙaramar hukumar Bokkos da ke jihar, sakamakon harin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai a jihar.

    Rahotonni sun ce maharan sun je ƙauyen ne cikin dare inda suka riƙa harbi tare da cinnawa gidaje wuta,, lamarin da ya jikkata mutane da dama..

    Kwamishinan yaɗa labaran jihar ya shaida wa BBC cewa rikicin ba na addini ko ƙabilanci ba ne, to amma ya ce rikicin ya yi kama da na manoma da makiyaya

    Jihar Plateau na daga cikin jihohin da ake yawan samun tashe-tashen hankula masu alaƙa da ƙabilanci da addini a Najeriya

  10. 'Yan Afirka ta Kudu na bayar da karnukansu bayan kashe yaro

    Kusan mutum 50 ne suka bayar da karnukansu bisa raɗin kansu bayan da wani karen ya kashe wani yaro mai shekara 8 a ƙarshen makon da ya gabata, kamar yadda ƙungiyar da ke kare mutane daga hatsarin dabbobi ta Afirka ta Kudu ta (SPCA) ta bayyana.

    A baya-bayan nan dai ana ta samun ƙarin kiraye-kirayen haramta kiwon karnukan Turawa a ƙasar, inda kusan mutum 90,000 suka saka hannu kan takardar ƙorafin da ke goyon bayan haramta kiwon karnukan.

    Ƙasar Afika ta Kudu na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake samun mace-macen da ke da alaƙa da farmakin karnuka.

  11. Majalisar dattawan Najeriya ta goyi bayan sake fasalin kuɗin ƙasar

    Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudurin babban bankin ƙasar na sake fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar.

    Majalisar ta amince da ƙudurin bayan zazzafar muhawara kan ƙudurin da Sanata Uba sani ya gabatar a zauren kan ƙudurin babban bankin na sake fasalin wasu takardun kudin ƙasar.

    Mafiya wayan 'yan majalisar sun amince da ƙudurin, to sai dai wasu daga ciki sun bayyana damuwarsu game da ranar da babban bankin ya saka na daina karɓar tsoffin kuɗin a faɗin bankunan ƙasar.

    Sannan kuma sun ɗiga ayar tambaya kan da alfanun yin hakan game da tattalin arziki, da yadda yin hakan zai sauƙaƙa hauhawar farashin kayyaki da farfaɗo da darajar naira.

    Suna masu buƙatar gwamnan babban bankin Godwin Emefiele da ya yi musu ƙarin haske kan waɗannan batutuwa.

    'Yan majalisun sun kuma ce suna fargaba game da illar da hakan za ta haifar ga mazauna karkara da wauraren da ba su da bankuna.

    A sanarwar da babban bankin ya fitar game da sake fasalin kuɗin ya ce sabbin kuɗin za su fara yawo daga ranar 15 ga watan Disamban 2022, a yayin da za a daina karɓar tsoffin kuɗin ranar 31 ga watan Janairun 2023.

  12. Ba gudu ba ja da baya kan samar da kamfanin Nigerian Air - Gwamnatin Najeriya

    Gwamnatin tarayya ta bakin ministan zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa Hadi Sirika ya ce babu wata doka a Najeriya da za ta hana gwamnatin Najeriya kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Nigerian Air

    Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Legas ce ta hana gwamnatin tarayya aiwatar da ƙudurin samar da kamfanin jiragen sama na Nigerian Air

    Hukuncin na zuwa ne bayan da wasu kamfannonin jiragen sama na cikin gida suka shigar da ƙara suna kalubalantar kafuwar kamfanin Nigeria Air, ta hanyar haɗin gwiwwa da Ethiopian Airlines.

    A umarnin da kotun ta bayar ranar Talata ta ce gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da wannan yarjejeniya har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron karar domin yanke hukunci.

  13. Kuwait ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutum bakwai

    Kuwait ta zartar da hukuncin kisa karon farko cikin shekara biyar, inda ta rataye mutum bakwai ciki har da mata biyu, duk kuwa da kiraye-kirayen dakatar da hukuncin daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama.

    Hukumar shigar da ƙara ta ƙasar ta ce waɗanda aka zartar wa hukuncin kisan sun haɗar da mata biyu ɗaya 'yar ƙasar, ɗaya kuma 'yar Habasha da kuma maza biyar uku 'yan ƙasar sauran biyun kuma 'yan ƙasashen Pakistan da Siriya ne.

    Kusan mutum 80 aka zartar wa da hukuncin kisa a Kuwait tun shekarun 1960, mafi yawa a kan laifukan da suka shafi kisan kai da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

    Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi kira ga ƙasar da ta jingine zartar da hukuncin kisan.

  14. Saura kwana 100 a buɗe rumfunan zaɓe a Najeriya - INEC

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ce yau saura kwana 100 a buɗe rumfunan zaɓe a fadin ƙasar

    A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Tuwita, mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar Farfesa Mahmod Yakubu, ya ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, sannan mako biyu baya a yi na gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi.

    Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa ba gudu ba ja da baya game da amfani da na'urar tattara sakamakon zaɓe da ta tantance masu kaɗa ƙuri'a a lokacin babban zaɓen da ke tafe.

  15. ‘Yan Mexico na makokin mutuwar karya

    Al'ummar Mexico na jimamin mutuwar wata karya - wadda ta zama fitacciya wajen aikin ceton mutanen da girgizar ƙasar 2017 ya rutsa da su.

    Rundunar sojin ruwan ƙasar ta ce karyar ta mutu ne sakamakon tsufa da ta yi.

    Sanye da tubarau da takalman sau-ciki, karyar mai suna Frida ta yi aiki tuƙuru wajen kuɓutar da mutanen da gini ya rufta kansu a birnin Puebla a shekarar 2017.

    A lokacin da take aiki da rundunar sojin ruwan ƙasar an kai Frida aikin ceto a ƙasashen Haiti da Ecuador.

    A wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin ruwan ƙasar ta yaba da kyawawan halaye da biyayyar da karyar ta nuna a lokacin aikinta.

  16. Za mu cire tallafin man fetur a 2023 – Gwamnatin tarayya

    Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta Najeriya Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur a watan Yunin 2023.

    Hajiya Zainab ta bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai da ta gudanar a Abuja babban birnin ƙasar bayan kammala taron tattalin arziki na ƙasa karo na 28.

    Kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito cewa biyan tallafin kudin man fetur ya laƙume naira tiriliyan 2.565 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022.

    Haka kuma a cikin kasafin kudinta, gwamnatin tarayya ta ƙiyasta kashe naira tiriliyan 3.3 wajen biyan tallafin man tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2023.

    Ta ci gaba da cewa kuɗin tallafin man na kawo wa kasafin kudin giɓin da dole sai an ciwo bashi kafin cike shi.

    “Ba kuɗi ne da muke da su a hannu ba, kudi ne da muke karɓo bashinsu domin biyan tallafin'', in ji ministar.

    “Wasu ƙasashe sun fara biyan tallafi saboda annobar Korona, da batun yaƙin Ukraine, to amma suna amfani da kuɗaɗensu wajen biyan tallafin, to amma mu bashi muke karɓowa domin biyan tallafin, to kun ga duka biyu kenan, dan haka dole mu dakatar da shi'', in ji ministar

  17. Buhari ya bai wa jami'an tsaro umarnin binciko waɗanda suka kashe Basarake a Imo

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga jami'an tsaron kasar da su gudanar da bincike domin gano wadanda suka kashe sarki Obudi Agwa Eze Ignitus Asor da ke jihar Imo.

    A ranar Litinin ne dai wasu 'yan bindiga suka kutsa fadar sarkin inda suka halakashi tare da wasu fadawansa hudu ta hanya bude musu wuta da bingigogi.

    A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba shehu ya fitar, shugaban ya umarci jam'ian tsaro da su gaggauta zaƙulo waɗanda suka aikata wannan mummanan laifi domin su fuskanci hukunci

  18. Gini ya rufta kan wasu mutane a Kenya

    Masu aikin ceto na neman akalla mutum goma, mafi yawansu masu aikin gini, waɗanda ake fargabar sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan wani gini da ya faɗi a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

    Ana cikin aikin ginin - mai hawa bakwai - a lokacin da ya faɗi ranar Talata da rana a yankin Kasarani da ke wajen birnin.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa sau biyu hukumomin na gargaɗi ga mai kula da ginin da ya dakatar da ginin saboda rashin tsari da ingancin ginin.

    Faɗuwar gine-ginen da ba a kammala ba abu ne da ya zama ruwan dare a ƙasar.

    Masu aikin ceto na ci gaba da aiki domin zaƙulo mutanen da suka akale a cikin ɓaraguzan ginin.

  19. Rukuni na biyu na sojojin Kenya na kan hanyarsu ta zuwa DR Kongo

    Rukuni na biyu na dakarun Kenya na dab da isa asar jamhuriya Dimokradiyyar Kongo a yau Laraba.

    Sojojin na daga cikin dakarun kawancen wanzar da zaman lafiya a gabshin asar.

    A watannin baya-bayan nan ungiyar tayar da ayar baya na zafafa kai hare-hare, abin da ke ƙara haddasa fargaba a gabashin ƙasar.

    Fiye da dakarun Kenya 900 ne za su kafa sansanin a kusa da birnin Goma da ke fama da rikice-rikice.

    Tun cikin watan Agusta ne dai sojojin Burundi ke aikin wanzar da zaman lafiya a lardin Kivu.

    Dakaraun na Kenya za su kasance a arewacin lardin Kivu, inda 'yan tayar da ƙayar baya na M23 ta kwace garuruwa da dama cikin watannin baya-bayan nan, tare da raba dubban mutane da muhallansu.

    Nan gaba cikin wannan watan ne gwamnatin Kongo za ta koma teburin tattaunawa da wakilan ƙungiyoyin tayar da ƙayar bayan a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

  20. Mutum 412 ne suka mutu a hatsarin ababen hawa cikin wata 10 a Legas - FRSC

    Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta Najeriya ta ce mutum 412 ne suka mutu yayin da mutum 522 suka samu munanan raunuka a haɗuran ababen hawa da suka auku a hanyoyin Legas tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba.

    Babban jami'in hukumar mai lura da shiyyar Legas Olusegun Ogungbemide -wanda ya wakilci babban shugaban hukumar - a taron ranar tunawa da waɗanda hatsarin kan tituna ya rutsa da su ne ya bayyana haka a birnin na Legas.

    Ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa gudun wuce kima, da rashin gyaran ababen hawa, da tuƙin ganganci a matsayin abubuwan da suke haddasa aukuwar mafi yawan haduran da ake gamuwa da su.

    Ya ci gaba da cewa sauya wa direbobi ɗabi'a game da waɗancan abubuwa da na da matuƙar muhimmanci, wajen rage aukuwar hasuran.