Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan takarar jam'iyyun adawa ba su san hanya ba balle su nuna wa wani - Tinubu

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. MDD ta yi ƙiyasin cewa yawan al'ummar duniya ya kai biliyan takwas

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa a yau yawan al'ummar duniya zai cika miliyan dubu takwas.

    Shekara goma sha ɗaya da ta gabata ne duniyar ta zarta yawan mutum miliyan dubu na ƙarshe da ta kai, amma kuma kiyasin na Majalisar ya nuna cewa duniyar ba za ta sake cimma wata miliyan dubu ɗin ba nan gaba sai a ƙarshen shekarun 2030.

    Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma yi ƙiyasin cewa rabin hayayyafar da za a yi a nan gaba a duniyar baki ɗaya, ana ganin za a yi ta ne a ƙasashe takwas, biyar daga cikinsu na Afirka ne.

    A shekara mai zuwa ne kuma ake sa ran Indiya za ta zarta China yawan al'umma a duniya baki ɗaya.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ne zai kasance tare da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhara kan labaran da muke wallafawa.