Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan takarar jam'iyyun adawa ba su san hanya ba balle su nuna wa wani - Tinubu

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. 'Makaman Rasha sun faɗa cikin Poland'

    Rahotanni na cewa wasu makaman Rasha sun faɗa ƙasar Poland inda suka yi sanadiyyar rayukan mutum biyu da ke aiki a gona.

    Bayanan sun ce makaman sun faɗa ne a wani yankin Poland da ke dab da kan iyakarta da Ukraine.

    Idan har bayanan suka zama gaskiya, zai zama karon farko da makaman Rasha suka faɗa cikin wata ƙasa da ke da wakilci a ƙungiyar NATO tun bayan ɓarkewar faɗa tsakanin Rasha da Ukraine.

    Sai dai ma’aikatar tsaro ta Rasha ta ce babu wani hari da aka kai kamn iyakar Poland da Ukraine.

    A wata sanarwa da ta fitar, Rasha ta bayyana rahotannin a matsayin wani mataki na ingiza wutar rikicin da ke gudana.

    Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka ya nanata cewa ƙasarsa za ta kare duk wani yanki na ƙasashen NATO.

  2. Kwamitin wanzar da zaman lafiya ya ja kunnen ƴan takarar shugaban Najeriya, Daga Mustapha Musa Kaita daga Abuja

    Kwamitin wanzar da zaman lafiya na Najeriya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasar Abdulsalam Abubakar, ya yi kira ga ƴan takarar shugabancin ƙasar da su mayar da hankali wurin ganin an gudanar da zaɓe lami lafiya ba tare da wani rikici ba.

    Kwamitin ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake samun ƙaruwar rikice-rikice a wuraren gangamin yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar.

    Kwamitin, wanda aka kafa domin tabbatar da an yi zabe cikin zaman lafiya da lumana wato NPC ya bayyana cewa akwai matsaloli da ke barazana ga zaɓen da ke tafe, hakan ne ya sa kwamitin ya bukaci a yi wa tufkar hanci.

    Kwamitin ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban kasar Abdulsamai Abubakar ya yi kira ga ƴan takarar shugabancin ƙasar a duka jam'iyyu da su ja kunnen masu magana da yawunsu da magoya bayansu da tabbatar da cewa sun yi iya bakinsu domin gudun tayar da zaune tsaye a lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin zaben kansa.

    Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake amfani da munanan kalaman da ba a taunawa da barazana da kuma yadda ake samun arangama tsakanin magoya bayan jam'iyyu.

    Haka kuma ya ce ƴan Najeriya sun damu matuƙa kan yadda wasu ƴan siyasa suke wasu abubuwan da ba su dace ba a cikin ƴan kwanakin nan.

    Haka kuma kwamitin ya ce idan ba a shawo kan wadannan matsalolin ba, za su iya kawo cikas ko kuma tasgaro ga yarjejeniyar zaman lafiyar da duka ƴan takarar shugabancin kasar suka rattaɓa wa hannu a watan Satumba.

    Wannan kiran da kwamitin ya yi na zuwa ne bayan shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmood Yakubu ya zargi ƴan siyasa da cewa suna ƙara zafafa fagen siyasa da kuma rashin bin dokoki.

    Haka kuma ƙasashen Birtaniya da Amurka sun nuna damuwa kan yadda ake ƙara zafafa hare-hare kan ofisoshi da kayayyakin hukumar zaɓen Najeriya inda suka ce duka waɗannan za su iya kawo tasgaro ko naƙasu ga zaɓen 2023.

    Ko a makon da ya gabata sai da wasu da ake zargin ɓata gari ne suka ƙona ofisoshin na Inec a jihohin Ogun da Osun.

    INEC din ta ce tsakanin Fabrairun 2019 zuwa Mayun 2021, an kai hare-hare kan ofisoshinta da kayayyakinta sau 41 a jihohi 14 na kasar.

  3. Ƴan tawayen Congo sun dumfari birnin Goma

    Ana ci gaba da mummunan gumurzu tsakanin dakarun jamhuriyar Demokraiyyar Congo da an tawayen M23 a wuri mai nisan kilomita 20 daga birnin Goma na gabashin asar.

    Wakilin BBC ya ce ƴan tawayen na M23 na so ne su ƙwace babban birnin yankin domin tursasa wa gwamnatin ƙasar ta yi yarjejeniya da su.

    Yanzu haka dai ƴan tawayen na riƙe da yanki mai faɗi da ke kan iyakar Uganda da Rwanda.

    Shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta ya je birnin na Goma domin tantance halin da ake ciki.

    Ya tattauna da shugaban DR Congo Felix Tshekedi kan hanyoyin da za a kawo ƙarshen tashin hankalin.

  4. Wani mutum 'ya rataye kan shi bayan an zarge shi da yin sata'

    Rundunar ƴan sanda ta jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar wani mutum a yankin Girei da ke jihar Adamawa.

    Bayanai na cewa mutumin ya kashe kan sa ne saboda zargin da aka yi masa na satan kuɗi, wanda ya sha musantawa.

    Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya ce yanzu haka hukuma ta fara bincike kan lamarin domin gano yadda mutuwar tasa ta samo asali.

    A bayanin da ya yi wa BBC, SP Suleiman ya ce sun samu rahoto ne na cewar wani mutum ya rataye kan shi a dajin ƙaramar hukumar Girei.

    Sai dai ya ce a lokacin da jami'ai suka isa wurin, gawar ta fara ruɓewa, amma sun samu wata takarda a gefensa, inda aka rubuta sunanasa da ƙaramar hukumar da ya fito.

    Ya ƙara da cewa takardar na ƙunshe da cewa an zarge shi ne da satan kuɗi naira 400 ko 40,000.

    "Hakan ne ya ɓata masa rai ya ɗauki matakin da ya ɗauka."

  5. Ƴan takarar jam'iyyun adawa ba su san hanya ba balle su nuna wa wani - Tinubu, Daga Ibrahim Isa a Abuja

    Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi alwashin magance matsalolin da ke damun kasar idan ya samu nasarar karbar mulki a babban zaben da ke tafe.

    A yau ne dan takarar ya kaddamar da yakin neman zaben nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda Shugaba Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka halarta.

    Mista Bola Tinubu ya lissafa mafi yawan matsalolin da ke damun Najeriya, ciki har da ƙarancin abubuwan more rayuwa, da durƙushewar masana’antu, da rashin aikin yi a tsakanin matasa.

    Kana ya yi alwashin magance su ta hanyar haɗa ƙwararru kuma gogaggu a cikin gwamnatinsa idan ya samu nasarar kafawa.

    “Mu a jam’iyyar APC, wato Tinubu da Shetima da yardar Allah mun yi wa ƴan Najeriya alkawarin yin shugabanci nagari a karakashin wannan yunƙuri na farfadowa ko sabunta fatan alheri a zuƙatan al’umma, sakamakon goyon bayan da kuke ba mu. Za mu hada ayarin jarumai don ciyar da kasa gaba.”

    Kazalika, dan takarar shugaban kasar ya caccaki abokan hamayyarsa… musamman ma na jam’iyyun adawa da ke gaba-gaba, wani lokaci har da kiran suna yana gugar-zana, yana cewa ba su san hanya ba, ballantana su yi wa wani jagora.

    Shi ma abokin takararsa, wato tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shetima da ya hau dandamali, bai ragar wa abokan hamyayyar nasu ba, yana cewa idan ka ji mutum ya ce zai ba ka riga to ka dubi ta wuyansa.

    Duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci wajen taron amma bai ce komai ba, face danƙawa ɗan takarar tutar jam’iyya da ya yi.

    Sai dai daya daga cikin gwamnonin da suka yi jawabi, Gwamna Nasiru ElRufai na jihar Kaduna, ya mayar da raddi ga masu kushe dan takarar yana cewa shi ne zabin manya.

    Da dama da suka yi jawabi sun nuna suna da kwarin gwiwa APC za ta kai labari a zabe mai zuwa.

    Amma Shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya shawarci ƴan jam’iyyar da ka da su shagala, su bari mulki ya ruɗe su, su yi wa jam’iyya aiki idan suna so su ga alheri.

    “Kasancewa a kan karagar mulki ba ya sa a dauwama a kan mulki. Ba zai hana faduwa ba idan ba mu dage mun yi abin da ya kamata mu yi da zai ma samu karbuwa a zukatan masu kaɗa ƙuri’a ba.

    “Wannan ne ya sa nake jaddada cewa mu kasance masu himma. Mu hada kai ta yadda za mu gudu tare mu tsira tare.”

    An dai kammala taro ana ta annashuwa, amma wani suɓul-da-baka da dan takarar shugaban kasar ya yi ta janyo ce-ce-ku-ce, lokacin da zai yi fatan alheri ga jam’iyyar a karshen jawabinsa sai ya ɓuge da ambaton sunan jam’iyyar adawa!

    Sai dai nan take ya gyara.

  6. EFCC ta kama ɗan canjin da BBC ta tattauna da shi kan farashin dala

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ce ta kama ɗaya daga cikin shugabannin ƴan canji na Abuja Mustapha Muhammed, wanda aka fi sani da Mustapha Naira.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, EFCC ta ce ta kama Mustapha Naira ne ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamba a cibiyar musayar kuɗi ta Zone 4 da ke Abuja.

    Sanarwar ta ƙara da cewa kamen ya biyo bayan yunƙurin da hukumar ke yi ne na tsaftace harkar canjin kuɗi, da kawar da masu hasashe da kuma yin zagon ƙasa ga tattalin arziƙin ƙasa.

    Ta kuma ce ya zuwa yanzu wanda aka kaman ya yi bayanai masu amfani, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

    Wannan dai na zuwa ne bayan wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da Mustapha game da farfaɗowar farashin naira a kan dala a ƙarshen makon da ya wuce.

  7. 'Sojojin Najeriya sun yi ruwan wuta kan ƴan bindiga a dazukan Kaduna', Daga Abdou Halilou

    Gwamnatin jihar Kaduna ta ce dakarun Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama da ƙwato makamai masu ɗinbin yawa a wani samame da suka kai a wasu dazukan jihar.

    Gwamnatin ta ce an samu nasarar hakan ne sakamakon hare-haren da sojojin suka kai ta sama.

    Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewar an kai hare-haren ne a ƙananan hukumomin Igabi, da Giwa, da Chikun da Kajuru.

    Kwamishinan ya ƙara da cewa a lokacin waɗannan hare-hare an samu nasarar kashe ƴan bindiga da dama, da kuma tayar da daba-daba na masu garkuwa da mutane.

    Sai dai kwamishinan ya ce har yanzu babu takamaiman alƙaluma na waɗanda aka kashe ko kuma makaman da aka ƙwato daga ƴan fashin.

    Ya kuma tabbatar da cewa jami'an tsaron sun samu nasarar ceto mutane da dama da ake garkuwa da su.

  8. An kai hare-haren makami mai linzami 85 Ukraine - Zelensky

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce an ƙaddamar hare-haren makami mai linzami har 85 a yau Talata, inda ya ce an sa ran za a sake kai wasu 20 a faɗin ƙasar.

    A wani saƙon bidiyo a shafin Telegram ya gargaɗi mutane da su kasance a cikin gidajensu.

    Wani babban jami'i a fadar shugaban ƙasar Kyrylo Tymoshenko, ya ce yanayin da ake ciki a ƙasar ya yi muni sosai bayan da makamai masu linzamin suka ragargaza muhimman wurare tare da lalata wutar lantarki, abin da ya sanya wasu sassan babban birnin ƙsar Kyiv cikin duhu.

    "Ƴan ta'addan Rasha sun sake kai wani shiryayyen harin kan cibiyoyin makamashi," ya ce.

    Ya ce yanayin da ake ciki a birnin Kyiv ya yi tsanani da muni matuƙa gaya.

  9. Wasu jiga-jigan NNPP da dama sun koma APC a jihar Zamfara, Daga Ibrahim Isa a Abuja

    Wasu shugabanni da jiga-jigan jam'iyyar NNPP daga kananan hukumomin jihar Zamfara goma sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

    Sun dai yi zargin cewa jaga-jigan uwar jam'iyyar ne suke musu kama-karya har ta kai ga jam'iyyar ta rasa dan takarar gwamnan da jama'a ke goyon baya, don haka ne suka gwammace su fice daga jam'iyyar.

    Amma shugabannin NNPP a matakin tarayyar sun musanta wannan zargin suna cewa sayen su aka yi.

    Shugabannin jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmarin sun bayyana cewa da shugabanni da jiga-jigan jam'iyyar na kananan hukumomi 10 daga cikin kananan hukumomi 14 da ke jihar ne da ƙwansu da kwarkwata suka yi hijira daga NNPP zuwa APC mai mulki sakamakon zargin kama-karya da suka ce ana yi musu.

    A cewarsu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu sun yi babakere a jam'iyyar sun hana kowa sakat.

    Hon Babangida Haruna Damba shi ne tshon sakataren tsare-tsare na jam'iyyar NNPP a jihar Zamfara da suka jagoranci wannan hijira.

    Sai dai shugabannin jam'iyyar NNPP a matakin tarayyar sun musanta wannan zargin suna cewa sayen masu sauya shekar aka yi, kuma tafiyarsu ba za rage wa NNPP komai ba.

    Injiniya Buba Galadima na cikin wadanda ake zargi da takura shugabannin jam'iyyar, wanda ya ce NNPP na da ɗan takarar gwamna a jihar Zamfara.

    Mako uku kenan da zuwan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Injniya Rabiu Musa Kwankwaso jihar Zamfara, inda rahotanni ke cewa ya zauna da shugabannin jam'iyyar domin ya ji koke-kokensu da nufin share musu hawaye.

    Amma sai ga shi kwatsam wadannan shugabanni da magoya bayansu sun sanar da ƙaurar da rikiɗar da suka yi daga NNPP zuwa APC.

    Kuma duk da jaga-jigan jam'iyyar na cewa Allah raka taki gona, masu sharhi a kan harkokin siyasa na cewa hakan babban koma-baya ne!

  10. Rasha ta yi watsi da kiraye-kirayen ƙasashen duniya kan biyan diyya

    Ƙasar Rasha ta yi watsi da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya ke yi mata na biyan diyya kan ɓarnar da ta yi wa Ukraine.

    Hakan na zuwa ne bayan da babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ƙuri'ar cewa dole Rasha ta fuskanci hukunci game da yaƙin Ukraine ciki har da biyan diyya ga abubuwa da ta lalata.

    Shawarwarin da ake cimmawa a babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na da ƙima, to amma zauren ba ya da ƙarfin tursasa ƙasashe su yi aiki da su.

    Rasha ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta dakatar da ƙasashen yamma daga yuƙurin amfani da kuɗaɗenta da ke ajiye asusunta na ƙetare domin biyan diyyar.

    Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov ya zargi ƙasashen na Turai da ƙoƙarin 'halasta sata' da kuma karya dokokin duniya kan mallakar kadarori

  11. Labaran rana cikin minti ɗaya

    Abdulallahi Bello Diginza da Haruna kakangi ne suka karanta labaran.

  12. Ivory Coast za ta janye dakarunta daga Mali

    Ƙasar Ivory Coast ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa za ta janye dakarunta daga ƙawancen Dakarun kiyaye zaman lafiya da ke Mali.

    Ta ce za ta fara janye dakarun nata sannu a hankali daga watan Agustan 2023.

    Ƙasashen biyu sun shiga takun-saƙa tun bayan da ƙasar Mali ta tsare sojojin Ivory Coast ɗin 50 a watan Yuli inda ta zarge su da kasancewa sojojin haya.

    Ƙasashe da yawa sun janye dakarunsu daga Mali sakamakon juyin mulki biyu da kuma alaƙar sojojin mulkin ƙasar da rundunar sojojin hayar Rasha ta Wagner

    A ranar Litinin ne dai, Birtaniya ta ce za ta janye dakarunta da ke aikin kiyaye zaman na Majalisar Dinkin Duniyar. A baya-bayan nan ne dai Faransa bayyana kawo ƙarshen aikin sojinta a Malin

  13. Kotu ta soke zaɓen fitar da gwanin gwamna na APC a Taraba

    Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja babban birnin Najeriya ta soke zaɓen fitar da gwanin gwamna na jam'iyyar APC a jihar Taraba.

    Alƙalin kotun mai shari'a Obiora Egwatu ya ce la'akari da hujjoji da shaidu da aka gabatar a gaban kotu, sun nuna cewa zaɓen fitar da gwanin da ka gudanar ranar 26 ga watan Mayun wannan shekara - wanda ya ayyana Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin ɗan takarar - ba halastacce ba ne.

    A watan da ya gabata ne dai wata kotun tarayya a birnin Jalingo ta soke zaɓen fitar da gwanin da jam'iyyar ta yi wa mista Bwacha, sakamakon ƙarar da ɗaya daga cikin 'yan takarar ya shigar a gaban kotun yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen.

    Duka kotunan biyu a hukunce-hukuncen da suka yi sun bayar da umarnin ga uwar jam'iyyar da ta sake shirya wani sabon zaɓen fitarda gwani a jihar.

  14. Ɗaruruwan matasa sun amsa kiran shiga aikin soji a DR Kongo

    Ɗaruruwan matasa ne suka amsa kiran shugaban ƙasar DR Kongo Felix Tshiseked dan shiga aikin soji domin yaƙar 'yan tawayen M23

    Kiran ɗaukar sabbin sojojin na zuwa ne bayan faɗa tsakanin dakarun sojin ƙasar da 'yan tawaye ke ƙara zafafa a yankin gabashin ƙasar.

    An ɗauki hotunan matasan zaune cikin jirgin sama lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa cibiyar bayar da horo

    A yanzu 'yan tawayen M23 ne ke riƙe da ikon mafi yawan garuruwan da ke yankin Goma, bayan ƙaddamar da jerin hare0hare.

    Ƙungiyar 'yan tawayen M23 wadda aka kafa kusan shekaru goma da suka gabata, na ikirarin kare 'yan kƙabilar Tutsi mazauna DR Kongo daga hare-haren 'yan tayar da ƙayar baya na ƙabilar Hutu.

    Matasan na ciƙe da ƙwarin gwiwwa da zummar game da yunƙrinsu na shiga aikin sojin domin fatattakar 'yan tawayen.

    Mafiya yawa daga cikin matasan da aka ɗauka sun fito ne daga lardin arewaci na Kivu. Ba a dai san tsawon lokacin da za a ɗauka ana horar da matasan kafin a kai su fagen yaƙin ba.

    Matasan sun yi machi a kan titunan birnin Goma kafin su isa zuwa filin jirgi domin ɗaukarsu zuwa cibiyar bayar da horon.

  15. Firaministan Rwandan ya sauka daga mulki saboda zargin shan barasa yayin tuƙi

    Firaministan Rwandan ya sauka daga muƙaminsa tare da neman afuwar 'yan ƙasar saboda shan barasa a lokacin da yake tuƙi.

    Gamariel Mbonimana ya ajiye muƙaminsa kwana guda bayan da shugaban ƙasar Paul Kagame ya soke shi kan yin tuki a lokacin da ya sha barasa.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter mista Mbonimana ya nemi afuwar 'yan ƙasar da kuma shugaban ƙasar yana mai alƙawarta cewa ''ba zai sake shan giya ba''.

    Tuƙi yayin da aka sha barasa laifi ne a ƙasar, da tararsa ta kai dala 140, tare da ɗaurin kwana biyar idan an kama shi.

    Yayin da yake wani jawabi a ƙarshen mako shugaban ƙasar Paul Kagame ya soki 'yan sandan ƙasar kan rashin kama firaministan, saboda ''kariyar'' da yake da ita.

    Mista Mbonimana shi ne firaministan ƙasar tun shekarar 2018, mamba ne a jam'iyyar Liberal Party wadda ke kawance da jam'iyyar RPF ta shugaba Kagame mai mulkin ƙasar.

  16. Buhari ya yi Allah wadai da kisan Basarake a jihar Imo

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa sarkin Obudi-Agwa, Eze Ignitus Asor tare da wasu fadawansa a fadarsa da ke yankin ƙaramar hukumar Oguta ta jihar Imo.

    A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu, shugaban ya umarci jami'an tsaro a jihar da su binciko waɗanda suka aikata wannan mummunan ta'asa domin su fuskanci shari'a kan laifin da suka aikata.

    Sannan shugaban ƙasar ya jajanta wa iyalai da 'yan uwa da kuma al'ummar garin na Obudi-Agwa bisa wannan iftila'i da ya auku.

    Haka kuma shugaba Buhari ya yaba da ƙoƙarin da jihar Imo ke yi wajen inganta sha'anin tsaro, yana mai kira ga al'ummar jihar da su bai wa jami'an tsaro haɗin kai wajen kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan da jihar ke fama da su.

  17. Gobara ta tashi a kasuwar Singa da ke Kano

    Gobara ta tashi a kasuwar kayan masarufi ta Singa da ke Kano a arewacin Najeriya.

    Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin wutar ba, to sai dai wani mai shago a kasuwar ya shaida wa BBC cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar

    Kawo yanzu wutar na ci , yayin da jami'an kashe gobara ke kokarin shawo kan wutar

  18. Yara miliyan 1.8 ba sa zuwa makaranta a Borno saboda rikicin Boko Haram

    Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce akwai yara kimanin miliyan 1.8 da ba sa zuwa makaranta a fadin jihar sakamakon rikice-rikicen ƙungiyar Boko Haram.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Abba Wakibe na bayyana haka a lokacin bikin ƙaddamar da horo kan wani shiri da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi kan fadakarwa game da illar rashin zuwa makaranta.

    Ya jaddada cewa tashe-tashen hankula masu alaƙa da ayyukan ƙungiyar Boko Haram sun shafi ɓangaren ilimi, ciki har da yawan yaran da ke zuwa makaranta.

    Ya ƙara da cewa ''muna da marayu 56,000 da zawarawa 49,000, to amma ba su san adadin yawan yaran da ba sa tare da iyayensu''.

  19. 'Dole a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine’ Zelensky ya faɗa wa shugabannin G20

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya gaya wa taron shugabbanin ƙasashen G20 a Bali cewa dole a kawo ƙarshen yaƙin da Rasha ke yi a ƙasarsa.

    Mista Zelensky wanda ya gabatar da jawabinsa ta bidiyo ya yi kira da a tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsi daga ƙasarsa zuwa ƙasashen waje.

    Ya ƙara da cewa ''Ina ganin yanzu ne ya kamata a kawo ƙarshen ɓarnar da Rasha ke yi mana a ƙasarmu da sunan yaƙi''

    Shugaban Rasha Vladimir Putin wanda mamba ne a ƙungiyar ta G20 ya ƙi halartar taron, inda ya tura ministan harkokin wajen ƙasar Sergei Lavrov domin ya wakilce shi.

  20. Sojojin saman Najeriya sun kashe 'yan fashin daji tare da lalata sansanoninsu a Kaduna

    Dakarun sojin saman Najeriya sun ƙaddamar da hare-hare kan wasu sansanonin 'yan fashin daji a wasu yankunan ƙananan hukumomin jihar Kaduna, tare da kashe 'yan fashin daji masu yawa.

    A wata sanarwa da kwamishinan al'umuran tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan a fitar ya ce an kai hare-hare kan wasu sansanonin 'yan fashin daji a wasu ƙauyuka da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi.

    Ya ƙara da cewa a yayin wannan hari an samu nasarar kashe 'yan fashin daji uku tare da kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su a sansanin''

    ''Haka kuma a Walawa da ke ƙaramar hukumar Giwa an kai farmaki kan wani sansanin 'yan fashin da wasu yankunan a ƙaramar hukumar Chikun'', in ji Kwamishinan.

    Haka kuma ya ce dakarun sojin saman sun hangi wasu 'yan fashin kilomita hudu a arewa mao yammacin Godani, inda nan take aka kashe su.