Birtaniya za ta janye sojojinta daga Mali
Birtaniya ta sanar da cewa za ta janye sojojinta da ke taimaka wa ƙasar Mali wurin yaƙi da masu iƙirarin jihadi a ƙasar.
Sojin na Birtaniya dai suna aiki ne ƙarƙashin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke a ƙasar wadda zaman lafiya ya yi wa ƙaranci.
Matakin Birtaniya na janye sojojin nata na zuwa ne shekara ɗaya gabanin ƙarewar ayyukan nasu a ƙasar ta Mali.
Minsitan dakarun Birtaniya ya shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewar juyin mulki na baya-bayan nan da aka samu a Mali, da kuma alaƙar da ke ƙara ƙarfi tsakanin gwamnatin sojin ta ƙasar da kamfanin sojin haya na Wagner na ƙasar Rasha na yin cikas ga ƙoƙarin ƙasashen duniya na gyara al'amuran kasar.
Dakarun Birtaniya sun kasance suna gudanar da sintiri a ƙasar ta Mali tsawon shekaru biyu da suka gabata, a wani ɓangare na ayyukan samar da zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya da ake wa taken MINUSMA.