Ƴan bindiga sun kashe sarki da fadawa a Imo

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Birtaniya za ta janye sojojinta daga Mali

    Jagoran juyin mulkin Mali Kanar Assimi Goïta wanda ya nada kansa shugaban rikon-kwarya

    Asalin hoton, Getty Images

    Birtaniya ta sanar da cewa za ta janye sojojinta da ke taimaka wa ƙasar Mali wurin yaƙi da masu iƙirarin jihadi a ƙasar.

    Sojin na Birtaniya dai suna aiki ne ƙarƙashin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke a ƙasar wadda zaman lafiya ya yi wa ƙaranci.

    Matakin Birtaniya na janye sojojin nata na zuwa ne shekara ɗaya gabanin ƙarewar ayyukan nasu a ƙasar ta Mali.

    Minsitan dakarun Birtaniya ya shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewar juyin mulki na baya-bayan nan da aka samu a Mali, da kuma alaƙar da ke ƙara ƙarfi tsakanin gwamnatin sojin ta ƙasar da kamfanin sojin haya na Wagner na ƙasar Rasha na yin cikas ga ƙoƙarin ƙasashen duniya na gyara al'amuran kasar.

    Dakarun Birtaniya sun kasance suna gudanar da sintiri a ƙasar ta Mali tsawon shekaru biyu da suka gabata, a wani ɓangare na ayyukan samar da zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya da ake wa taken MINUSMA.

  2. Shugaba Buhari ya tura wa majalisa kasafin kuɗin Abuja

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Other

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tura wasu ƙudurorin doka uku ga majalisar wakilan ƙasar a zaman da ta yi ranar Litinin

    Cikin ƙudurorin har da na yin gyara ga dokar da ta kafa hukumar da ke sauraron koke-koken jama`a.

    Sauran ƙudurorin da shugaban ya tura sun haɗa da kasafin kuɗin Abuja, babban birnin tarayya.

    Sai kuma kasafin kuɗi na hukumar raya yankin Neja-Delta.

    Majalisar wadda ba kasafai take zama a ranar Litinin ba, ta yi zaman ne domin ta bai wa mafi yawan `yan majalisar damar halartar ƙaddamar da yakin neman zaɓen ɗan takarar jam'iyyar APC na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda za a yi ranar Talata.

  3. An ci tarar gidan talabijin na Arise saboda yaɗa 'labarin ƙarya'

    .

    Asalin hoton, FACEBOOK/NBC

    Hukumar kula da kafafen yaɗa labaru na Najeriya NBC ta ci tarar kafar yaɗa labaru ta Arise saboda zargin ta da yaɗa labarin ƙarya.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne Arise TV ya yi wani labari da ke cewa hukumar zaɓe na binciken ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, bisa dogaro da wani labarin da aka rinƙa yaɗawa a shafukan intanet.

    NBC ta ce abin da kafar Arise ta yi, "gagarumin karan-tsaye ne ga dokar yaɗa labaru ta ƙasa sashe na 5.1.3, da rashin iya aiki, da kuma rashin tunani a wannan lokaci da ake yaƙin neman zaɓe."

    Saboda haka sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar, Balarabe Shehu Illela, ta buƙaci Arise TV ya biya tarar naira miliyan biyu a cikin wa'adin mako biyu.

    A ranar Lahadi ne dai kafar Talabijin ɗin na Arise ya nemi afuwar ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar A.P.C, bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta fitar da wani bayani kan cewar labarin da ake yaɗawa da ke cewa tana bincike kan Bola Ahmed Tinibu ba gaskiya ba ne.

    Hukumar ta NBC ta kuma buƙaci kakafen yaɗa labaru da su rinƙa tantance duk wani labari da suka samu gabanin wallafa shi, musamman ma wanda aka samu a shafukan sada zumunta.

  4. Ƴan bindiga sun kashe sarki da fadawa a Imo

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Obudi Agwa a ƙaramar hukumar Oguta da ke jihar Imo, inda suka kashe mutam biyar, ciki har da basaraken garin Ignitus Asor.

    Bayanan da jaridar Punch ta tattara sun nuna cewar ƴan bindigan sun dira a ƙauyen ne lokacin da dattijan ƙauyen ke tattauna lamurran da suka shafi yankin a fadar mai gari.

    Mai garin da fadawa biyu da kuma wasu mutanen biyu ne aka kashe nan take, yayin da wasu suka samu rauni.

    Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar, Ijioma Ofili ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun yi masa bayani kan abin da ya faru.

    Ya kuma ce jami’an tsaro sun dawo da zaman lafiya a yankin.

  5. Ƙananan hukumomi huɗu kawai ke da bankuna a jihar Yobe - Gwamna Buni

    Mai Mala Buni

    Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce ƙananan hukumomi huɗu ne kawai ke da bankuna daga cikin 17 da ke jihar, da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Kamfanin dillancin labaru na Najeriya NAN, ya ruwaito gwamnan a ranar Litinin yana kira ga bankunan ƙasar da su samar da rassa a faɗin jihar domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

    Mr Buni ya yi wannan kira ne a birnin Damaturu a yayin da yake ƙaddamar da wuraren cire kuɗi na POS da bankin UBA ya yi domin inganta shigar kuɗaɗen haraji.

    Ya ce samar da ƙarin rassa a faɗin jihar zai ƙarfafa hada-hadar kuɗi ta bankuna a tsakanin mazauna yankunan karkara.

    Gwamna Buni ya ce buɗe ƙarin rassa da bankuna za su yi zai taimaka wajen bin sabon tsarin da babban bankin Najeriya ya samar na sake fasalin kuɗi.

    "Ina kira ga bankuna da su zage damtse wajen wayar da kai a kan wannan tsarin tare da samar da hanyoyin da mutane za su iya canza tsofaffin kudaɗensu a natse kafin 31 ga watan Janairun 2023 da gwamnati ta ce," in ji gwamnan.

  6. An kashe ɗalibi ɗan Zambia da ke yi wa Rasha yaƙi a Ukraine

    .

    Asalin hoton, EPA

    Wani ɗalibi ɗan asalin Zambia wanda ke karatu a Rasha, ya rasa ransa a fagen yaƙi a Ukraine, a wani yanayi mai ɗaure kai.

    Ministan tsaro na Zambia ya shaida wa manema labaru a Lusaka cewa, dama dai ɗalibin yana zaman kaso ne a ƙasar ta Rasha.

    Ɗalibin mai suna Lemekhani, mai shekara 23, yana karantar ilimin nukiliya ne ne a Moscow Engineering Physics Institute, amma a shekarar 2020 an yanke masa ɗaurin shekara tara bayan samun sa wani laifi da ba a fayyace ba.

    Ministan harkokin wajen na Zambia, Stanley Kakubo ya faɗa wa manema labaru a yau Litinin cewa Nyirenda, wanda ɗaya ne daga cikin ɗaliban da gwamnati ke ɗaukar nauyin karatunsu a ƙasar ta Rasha, an kashe shi ne tun cikin watan Satumba, amma sai yanzu ne hukumomin Rasha suka sanar da ƙasar ta Zambia.

    Ya ce saboda haka "gwamnatin Zambia ta buƙaci Rasha ta yi mata bayani dalla-dalla kan yadda aka yi ɗalibin da ke zaman kaso ya samu kansa cikin aikin soji kuma aka tura shi yaƙi a Ukraine, inda ya rasa ransa."

    Ya ce yanzu haka ana shirye-shiryen mayar da gawar ɗalibin gida daga Rasha.

    Ya ƙara da cewa "ina tattaunawa da iyalan mamacin, kuma zan ci gaba da tattaunawa da su domin bayyana masu duk bayanin da muka samu game da mutuwar ɗan'uwan nasu."

    Ba a dai san yadda aka yi Nyirenda ya fito daga gidan yari ba, amma Rasha ta rinƙa yi wa fursunoni tayin sakin su idan suka amince za su fafata a faɗan da take yi da Ukraine.

  7. Sarkin Saudiyya ya ba da umarnin yin sallar roƙon ruwa a masallatan ƙasar

    Sarki Salman

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdul'aziz ya bai wa masallatan ƙasar umarnin gabatar da sallar roƙon ruwa a ranar Alhamis mai zuwa.

    Shafin Facebook da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Makkah da Madina na ne ya sanar da hakan a yau Litinin.

    Sarki Salman ya ce cikin masallatan da za a yi sallar roƙon ruwan har da na Ka'aba da na Manzon Allah da ke Madina.

  8. Biden ya gana da Xi Jinpin a karon farko tun bayan hawansa mulki

    Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da takwaransa na China, wani abu da ke nuna dawowar ƙyaƙƙyawar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

    Mista Biden da Xi Jinpin sun yi musabaha cikin raha a farkon haɗuwarsu a Bali gabanin taron manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G20 da za a gudanar a wannan shekarar.

    Shugaba Biden ya ce bai kamata ƙasashen biyu su bari gogayya ta kai su ga rikici ba.

    A nasa ɓangaren, Mista Xi ya ce duniya na fatan ganin alaƙarsu tana tafiya dai-dai.

  9. Kotu ta soke zaɓen fidda gwanin gwamna na jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom

    APC

    Asalin hoton, Apc

    Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Uyo babban birnin Akwa Ibom ta soke zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a jam'iyyar APC wanda ya bai wa Akan Udofia nasara.

    Kotun ta yanke hukuncin cewa Akan Udofia ba halastaccen ɗan jam'iyyar APC ba ne.

    Yayin da take yanke hukuncin mai shari'a Agatha Okeke ta bayar da umarni ga jam'iyyar da ta sake gudanar da wani zaɓen fidda gwanin a jihar cikin mako biyu masu zuwa.

    Tsohon mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin Niger Delta Ita Enang ne ya shigar da ƙara a gaban kotun yana ƙalubalantar takarar mista Udofia.

    Mista Enang ya yi zargin cewar Udofia ba ɗan jam'iyyar APC ba ne a lokacin da aka gudanar da zaɓen fidda gwanin, kasancewa ya shiga takarar fidda gwani da jam'iyyar PDP ta gudanar ranar 25 ga watan Mayu, kafin daga bisani ya shiga takara a zaɓen fidda gwanin da jam'iyyar APC ta gudanar ranar 26 ga watan na Mayu.

  10. Taliban ta bayar da umarnin yin hukunci da shari'ar musulunci a kotunan Afghanistan

    AFGHAN ISLAMIC PRESS

    Asalin hoton, AFGHAN ISLAMIC PRESS

    Shugaban Afghanistan Haibatullah Akhundzada ya bayar da umarni ga alkalan ƙasar da su fara amfani da hukunce-hukuncen musulunci kamar jifa da yanke hannu kan masu aikata laifuka a ƙasar.

    Mai magana da yawun jagoran ƙungiyar ya ce laifuka irinsu fashi, da garkuwa da mutane dole a riƙa yin hukuncinsu bisa tsarin addinin musulunci.

    A lokacin da ƙungiyar ke mulki a shekarun 1990, an yi ta sukarta game da irin waɗannan hukunce-hukunce, da suka haɗar da hukunci kisa a bainar jama'a

  11. Minti ɗaya da BBC

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraron labaran
  12. Kotu ta ɗage shari'ar Nnamdi Kanu sai abin da hali ya yi

    Nnamdi Kanu

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar kotun tarayya ta ɗage shari'ar da take yi wa jagoran fafutikar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu kan alaƙa da ta'addanci da gwamnatin tarayya ke zarginsa da shi.

    Mai shari'a Binta Nyako ta ce ta ɗage shari'ar ne har zuwa lokacin da za a yanke hukunci game da ɗaukaka ƙarar da gwamnatin tarayya ta yi kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 13 ga watan Oktoba, wadda ta wanke shi daga zarge-zargen alaƙa da ta'addanci.

    Gwamnatin tarayya ta ɗaukaka ƙara ne a gaban kotun ƙolin ƙasar tana mai neman kotun da ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka ƙarar.

    Nnamdi Kanu dai bai halarci zaman kotun na ranar Litinin ba.

  13. Majalisar wakilai ta gayyaci hukumomin gwamnati 63 kan kashe tiriliyan biyu ba bisa ƙa'ida ba

    Majalisa

    Asalin hoton, other

    Kwamitin Majalisar wakilan Najeriya da ke sa ido kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati ya gayyaci ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 63, domin bayar da bahasi game da aiwatar da wasu ayyukan da ba sa cikin kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar a gaban majalisar, abin da kwamitin ya ce ya haddasa kashe kuɗi ba bisa ƙa'ida ba da yawansu ya kai sama da tiriliyan biyu.

    Shugaban kwamitin Oluwole Oke, ya rubuta wasiƙa zuwa ga babban daraktan hukumar kasafin kuɗi ta ƙasar yana mai bayyana buƙatar neman hujjar majalisar wakilan kasar kan yin hakan.

    Shugaban ƙasa ne ke miƙa kasafin kuɗin ma'aikatu ga hukumomin gwamnatin zuwa ga majalisar wakilan ƙasar, yayin da Akawun majalisar zai mayar wa shugaban kasar kasafin da majalisar ta amince da shi domin aiwatarwa.

    Yayin da yake ƙarin haske kan wasiƙar mista Oke ya ce ''An kashe sama da tiriliyan biyu ba bisa ƙa'ida ba. Shugaban ƙasa bai kawo kasafin kuɗinsu ba. Dole su faɗa wa 'yan Najeriya me yasa suke aiwatar da kasafin kuɗin da bai bi matakan shari'a ba''.

    ''Shugaban ƙasa bai gabatar da kasafinsu a majalisa ba. Haka kakakin majalisa da shugaban majalisar dattawa ba ɗaya daga cikinsu da ya gabatar da wannan batu a harabar majalisun dokokin ƙasar biyu. Dan haka mun gayyaci hukumomin da su zo su yi bayani'', in ji shi.

  14. Zelensky ya ziyarci Kherson karon farko tun bayan ƙwace birnin

    Zelensky

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ziyarci birnin Kherson kwanaki bayan dakarunsa sun ƙwato birnin daga hannun sojojin Rasha.

    Ya kuma yi jawabi ga dakarun da suka taru a birnin inda ya bayyana cewa ƙasarsa na samun ci gaba, kuma a shirye take domin samun zaman lafiya.

    Ƙwace birnin Kherson, wanda ke hannun Rasha tun farkon mayayar, wani babban koma-baya ne ga ƙasar ta Rasha.

    A baya dai Rasha ta bayyana birnin a matsayin cibiyar mulkin yankin da ta kwace tun farkon mamayar.

    Dakarun Ukraine sun shiga birnin a ranar Juma'a, karon farko tun cikin watan Maris.

    A 'yan kwanakin nan dai an yi ta ganin mazauna birnin na ta murna sakamakon sake ganin juna da suka yi karon farko cikin watanni.

    Mista Zelensky ya gode wa ƙungiyar tsaro ta NATO da sauran ƙawayensa saboda goyon baya da suka bai wa ƙasarsa a lokacin yaƙin.

  15. Kare ya kashe wani ƙaramin yaro a Afirka ta Kudu

    Kare

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana samun ƙarin kiraye-kirayen haramta kiwon karnukan Turawa a Afrika ta kudu

    Wannan na zuwa ne bayan da rahotonni suka ce wani karen ya kashe ƙaramin yaro mai shekara takwas ranar Asabar a ƙasar.

    Ƙasar Afirka ta kudu na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake yawaitar samun mace-macen da ke da alaƙa da farmakin karnuka, kamar yadda rahotonni suka nuna.

    A watan Oktoba ma dai wani karen ya kashe wani yaro mai shekara 10 a gidan da ake kiwonsa.

    Fiye da mutum 50,000 ne suka saka hannu a kan takardar korafin haramta kiwon karnukan a yanar gizo a faɗin ƙasar.

    Gidauniyar Sizwe Kupelo wadda ita ce ta shirya ƙorafin, ta ce yunƙurinta na haramta kiwon irin waɗannan karnuka ya zama dole ne sakamakon yadda ake samun yawaitar farmakar yara da karnukan ke yi.

  16. ASUU za ta ware ranar da ba za ta shiga aji ba

    ASUU

    Asalin hoton, TWITTER/HOUSEOFREPS

    Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya ta ce za ta ayyana ranar da ba za ta shiga aji ba a jami'o'in ƙasar domin bayyana rashin jin daɗinsu game da zargin da take yi wa gwamnatin tarayya na riƙe musu albashin wasu watanni.

    Babban jami'in ƙungiyar mai lura da shiyyar Kano Farfesa Abdulkadir Muhammad ya shaida wa BBC cewa ƙungiyar ASUU ta yanke shawarar ne domin bayyana ɓacin ranta kan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na ƙin biyan mambobin ƙungiyar albashinsu na wasu watanni bayan sun janye yajin aiki.

    Ya ce ''kowane reshe zai zaɓi rana guda da zai gudanar da taro tare da zanga-zangar lumana, domin nuna ɓacin ransu da rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin mayar da malaman jami'o'i ma'aikatan wucin gadi''.

    Ya ƙara da cewa ''ASUU za ta gudanar da taro a kowane reshe na ƙungiyar, inda kuma duka mambobin ƙungiyar za su hallara, bayan gabatar da laccoci a wajen taron, mambobin ƙungiyar za su gudanar da zanga-zangar lumana a cikin kowacce jami'a, sannan kuma a ranar ba za su shiga aji domin koyawa dalibai karatu ba'

    A cikin watan Oktoba ne ASUU ta janye yajin aikin da ta kwashe wata takwas tana gudanarwa.

  17. Shugabar Tanzaniya ta kira taron ministoci kan hatsarin jirgin sama

    .

    Asalin hoton, AFP

    Shugabar ƙasar Tanzaniya Samia Suluhu za ta gudanar da taron gaggawa da ministocin ƙasar domin tattauna batun faduwar jirgin saman da ya auku a makon da ya gabata tare da kashe mutum 19.

    Jirgin saman fasinjan ya faɗi ne cikin tekun Victoria ranar shida ga watan Nuwamba, a lokacin da ya yi yunƙurin saukar gaggawa.

    Masu bincike daga kamfanin jirgin da ƙwararru daga Faransa na garin da lamarin ya auku domin gano musabbabin faruwar hatsarin.

    Jirgin saman mallakin Precision Air, kamfanin jirgin sama mai zaman kansa mafi girma a Tanzaniya, wanda ke zirga-zirga a ƙasar tun shekarar 1994.

  18. Biden zai gana da shugaban China Xi Jinping

    Biden  Xi Jinping

    Asalin hoton, Getty Images

    Nan gaba kaɗan ne shugaban Amirka Joe Biden zai gana da takwaransa na China Xi Jinping a karon farko tun bayan zama shugaban kasa.

    Za su tattauna kan batun tsuburin Bali na Indonesia, gabannin taron ƙolin kasashen G20 masu karfin tttalin arziki.

    Mai magana da yawun fadar White Hause ya ce abin da shugabannin za su maida hankali a kai shi ne share hanyar alaƙar ƙasashen biyu nan gaba.

    Dangantaka tsakanin kasashen na ƙara yin tsami, musamman kan batun mallakar yankin Taiwan ga China.

  19. Assalamu alaikum

    Diginza

    Asalin hoton, AB Diginza

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, wadda Bahaushe ke yi wa kirari da Mande tushen aiki.

    Abdullahi Bello Diginza ne zai kasance tare da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhara kan labaran da muke wallafawa.