Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Shugaba Buhari ya gana da sarki Charles III na Birtaniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. Zinace-zinace na haifar da yawaitar mutuwar aure a Zambia

    Matsalar mutuwar aure a lardin gabashin Zambia na ƙaruwa cikin shekara biyu a jere, kamar yadda jaridar Zambia Daily taruwaito.

    Lardin shi ne cibiyar harkokin noma na ƙasar.

    A watanni takwas da suka gabata kimanin ma'aurata 3,400 ne suka shigar da neman a raba aurensu, a lardin.

    Kuma akasarin waɗanda suka shigar da buƙatar kashe auren sun kafa hujja ne da zargin zina a ɓangaren mijin ko kuma matar.

    A bara an samu mutuwar aure 4,441 ne, amma an yi hasashen cewar mace-macen auren na bana zai zarta na shekarar da ta gabata.

    Sauran dalilan da ke haifar da mutuwar auren sun haɗa da cin zarafin abokin zama da kuma zaluntar juna.

    Jaridar ta ce a kashe aurarraki da dama a yankin domin kauce wa cin zarafin juna da ke iya kai wa ga kisan kai.

  2. Tirela ta kashe mutane da dama a Jimeta

    Mutane da dama ne suka mutu, wasu kuma suka samu raunuka bayan da wata babbar motar dakon kaya ta kufce ta faɗa kan mutane a garin Jimeta na jihar Adamawa.

    Wani da lamarin ya faru a gabansa ya shaida wa BBC cewa mutum 11 ne suka mutu.

    Sai dai shugaban Hukumar kre afkuwar haɗurra ta Najeriya reshen jihar Adamawa ya ce gaba ɗaya mutane 15 ne lamarin ya rutsa da su.

    Ya ƙara da cewa sun gano cewa lalacewar burki ne ya haifar da haɗarin.

    Motar ta ƙwace ne ta haye kan wasu motoci kafin ta faɗa wani garejin kanikawa a mahaɗar Vunoklang.

    Rundunar ƴan sanda a jihar ta Yola ta ce an kai mutanen da suka samu raunuka asibiti.

  3. 'Mutane na ci gaba da mutuwa a Tigray duk da yarjejeniyar da aka cimma'

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce babu abinci da magungunan da suka isa yankin Tigray na Ethiopia duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka rattaba hannu a makon da ya gabata.

    Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, wanda ya fito daga Tigray, ya ce ya sa ran kayan jin ƙai su fara isa yankin ba tare da ɓata lokaci ba amma shiru.

    Ya ce "mun ji daɗin yadda aka bai wa zaman lafiya dama amma za mu so mu yi kira a gaggauta isar da abinci da magunguna zuwa Tigray."

    Ya ƙara da cewa mutane suna mutuwa sanadin yunwa inda ya yi kira da a sake buɗe kamfanonin sadarwa da bankuna.

    Wani jami’in ƙasar ya ce abinci da magunguna suna isa Tigray kuma tuni aka buɗe kamfanonin sadarwa a wasu yankunan.

  4. Fafaroma ya soki matakin amfani da sojojin haya a yaƙin Ukraine

    Fafaroma Francis ya soki matakin yin amfani da sojojin haya a yaƙin da ake yi a Ukraine.

    Da yake magana a Fadar Vatican, Paparoman ya ce sojojin hayar na azabtar da mutane.

    Bai fito ya bayyana kungiyar da yake magana a kai ba amma ya sha yin Allah-wadai da yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine.

    Ƙungiyar tsaro ta Rasha, Wagner, tana taka muhimmiyar rawa a yaƙin da ake ci gaba da yi.

    Jami’an Ukraine sun ce Rasha ta kai hari cikin dare a birnin Dnipro har mutum huɗu suka mutu.

  5. Shugaba Buhari ya gana da sarki Charles III na Birtaniya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da sarkin Ingila Charles na uku a fadar Buckingham da ke birnin London.

    Wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Buhari da basaraken tun bayan hawan sa kan karagar mulki.

    Bayanai na cewa ganawar ta bai wa shugaban na Najeriya damar taya sarkin murnar hawa mulki.

    Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan sada zumunta a shafukan intanet Bashir Ahmad ya wallafa hotunan ganawar a shafinsa na tuwita, sai dai babu ƙarin bayani kan tattaunawar da ta wakana tsakanin shugabannin biyu.

  6. Gobara ta ƙona shaguna 80 a Onitsa

    Hukumomi a jihar Anambra sun ce shaguna 80 ne suka ƙone a gobarar da ta tashi a kasuwar sinadarai ta garin Onitsha.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Martin Agbili.

    Koda yake babu wasu alƙaluma daga hukumomi kan adadin waɗanda suka mutu, to amma wasu rahotanni na cewa an samu salwantar rayuka.

    Hukumomi sun ce sun fara gudanar da bincike kan musabbabin fashewar sanadaran da suka haifar da gobarar.

  7. Najeriya za ta rage cunkoson gidajen yari

    Gwamnatin Najeriya ta ce tana son ƙara rage yawan fursunonin da ke cikin gidajen gyara hali da ke faɗin ƙasar domin rage cunkoso.

    Mai bai wa Ministan harkokin cikin gida na ƙasar shawara kan harkokin watsa labarai Sola Fsure ne ya tabbatar wa manema labarai hakan inda ya ce tuni ministan wato Rauf Aregbesola ya aika takarda ga gwamnonin ƙasar domin neman haɗin kansu.

    Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Rauf Aregbesola ya bayyana cewa yana so ya tattauna da gwamonin ƙasar domin sakin aƙalla kashi talatin cikin ɗari na fursunonin da ke gidajen gyaran hali a fadin ƙasar.

    Ya bayyana cewa akwai buƙatar yin hakan sakamakon kashi 90 cikin 100 na fursunonin ƙasar an tsare su ne sakamakon saɓa dokokin jihohi inda ya ce akwai kimanin fursunoni 75,635 da ke zaman jiran shari'a.

    Mista Aregbesola ya bayyana cewa jimillar waɗanda suka saba dokokin gwamnatin tarayya da ke tsare a gidajen gyaran hali ba su wuce kashi 10 cikin 100 ba inda ya ce sauran waɗanda ke tsare duk suna da alaƙa ne da saɓa dokokin jihohi.

    Gwamnatin ƙasar dai ta sha kokawa kan yadda gidajen gyaran hali a ƙasar suke ci gaba da cika da masu laifi inda akasarin wasu gidajen an saka fursunonin da suka wuce adadin da suke ɗauka.

  8. Farashin kaya na ci gaba da tashi babu ƙaƙƙautawa a Ghana

    Tashin farashin kayan masarufi a Ghana ya kai kashi 40.4% a watan Oktoba, daga kashi 37.2% da yake a watan Satumba.

    Wani bayani daga hukumar ƙididdiga ta Ghana ya ce farashin kayan abinci, da na mai da kuma kayan masarufi sun yi tashin da ba a taɓa ganin irin sa ba.

    A ranar Asabar ɗaruruwan masu zanga-zanga ne suka yi tattaki a kan hanyoyin Accra, babban birnin ƙasar suna kira ga shugaban ƙasar Nana Akufo Addo, da mataimakinsa Mahamudu Bawumia da kuma ministan kuɗi na kasar da su sauka daga muƙamansu.

    Darajar takardar kuɗin ƙasar ta cedi ta yi mummunan faɗi a watan da ya gabata, idan aka kwatanta da dalar Amurka, kuma an bayyana cedi ɗin a matsayin wanda darajarsa ta fi kowace takardar kuɗi faɗi a duniya.

  9. Ba zan yarda laifin wani ya shafe ni ba - Shugaban EFCC

    Shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC AbdulRasheed Bawa ya ce ya daukaka kara dangane da hukuncin da wata kotun birnin tarayya ta yanke masa ranar Talata a Abuja.

    Kotun yanke hukuncin tura shi gidan yari sakamakon kama shi da laifin raina umarnin kotu.

    Tun da farko dai kotun ta umarci shugaban da ya mayar da wasu kudi da suka kai naira miliyan 40 da wata motar alfama da hukumar ta karba daga wani mutum da ta zarga da laifin rashawa.

    Shugaban EFCCn ya ce shi a karan kansa bai yi watsi da umarnin kotun ba a matsayinsa na shugaban hukumar, ballantana ya fuskanci fushin kotu, saboda a saninsa kotun ta bayar da umarnin ne tun a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018.

    Wato shekara uku kenan kafin ya zama shugaban hukumar ta EFCC, dan haka ba shi aka bai wa umarnin ba kuma a cewarsa babu yadda za a yi laifin wani ya shafe,

    Ya kara da cewa ''Mun riga mun daukaka kara game da wannan hukunci, dan haka za mu jira domin ganin yadda shari'ar za ta kasance''

    Amma ya ce duk da haka ya bayar da umarni a mayar da wannan motar alfarma ga mai ita tun a ranar 27 ga watan Yunin wannan shekarar, tare da bayar da umarnin bin hanyar da ta dace wajen mayar da kudin naira miliyan 40 ga mai su.

  10. Mataimakin gwamnan Kherson ya mutu a hatsarin mota

    Kafar yada labaran Rasha ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan birnin Kherson Kirill Stremousov - wanda Rasha ta nada - ya mutu a wani hatsarin mota.

    An nada Mista Stremousov mai 45 a matsayin mataimakin gwamnan birnin watanni biyu bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

    Ya kasance daya daga cikin mutanen da suka yi fice a lokacin mamayar, inda ya yi fice wajen fitar da kausasan sakonni a shafukan sada zumunta

    'Yan sanda Ukraine dai sun bayyana nemansa ruwa-a-jallo saboda zargin cin amanar kasa.

  11. Buhari ya taya 'yan Najeriya da suka lashe zabe a Amurka murna

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga asalin 'yan kasar mazauna Amurka su takwas da suka samu nasarar lashe kujeru daban-daban a zaben rabin wa'adi da aka gudanar a kasar.

    A jihar Georgia mutum biyar ne 'yan asalin Najeriya suka lashe kujerun majalisar dokokin jihar a gundumomin da suke zaune.

    Sannan kuma mutum guda-guda ya ci kujerun majalisa a jihohin Pennsylvania da Minnesota.

    Haka kuma an sake zabar Dakta Oye Owolewa a kujerar majalisar wakilan kasar daga birnin Washington D.C

    A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan kafofin yada labarai mista Femi Adesina ya fitar, Shugaba Buhari ya yi musu fatan alkairi a tsawon lokacin mulkinsu.

    Sannan kuma shugaban ya gode musu bisa taimakekeniya da hadin kai da suke nuna wa junansu a tsawon shekarun da suka kwashe a Amurka.

  12. Ba za a iya kutse a na'urar tattara sakamakon zabe ba - INEC

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta kara tabbatar wa 'yan kasar cewa ba za a iya yin kutse domin sauya bayanan da ke cikin na'urorin tattara sakamakon zabe ba.

    Babban mataimakin shugaban hukumar mai lura da sashen fasahar zamani Lawrence Bayode ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani shiri na gidan Talbijin din Channels TV .

    Yana mai cewa ba za a iya yi wa na'urar kutse a ranar zabe ba.

    ''Ina so in sake tabbatar da cewa mun yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa ba a yi wa na'urar kutse ba, za a kiyaye duka bayanan da ke cikin na'urar''.

    “Bayan zaben, idan za a turo da bayanan zuwa babbar na'urarmu, za a kiyaye bayanan a lokacin da ake turo su, sannan bayan sun zo babbar na'urarmu,za a ci gaba da lura tare da kiyaye su'', in ji shi

    Ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ba a yi kutse wa na'urorin ba.

  13. Kamfanin Meta mai mallakin Facebook zai kori ma'aikata 11,000

    Kamfanin Meta mai mallakin shafukan Facebook da Instagram da kuma WhatsApp, ya bayyana cewa zai rage kashi 13 cikin 100 na ma'aikatansa.

    Abin da ke nufin kamfanin zai kori ma'aikata 11.000 daga cikin ma'aikatansa 87,000 a fadin duniya.

    A wata sanarwa da shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya fitar, ya ce rage ma'aikatan na daga cikin wasu sauye-sauye masu tsanani da kamfanin ya gudanar a tarihinsa.

    Shi ma dai kamfanin Twitter ya bayyana rage rabin ma'aikatansa a fadin duniya.

    A wani labarin kuma kuma kamfanin na Twitter ya bayyana korar kusan duka ma'aikatansa a kasar Ghana.

    Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ma'aikaci daya ne kawai kamfanin bai kora ba, daga cikin ma'aikata kusan 20 da yake da su a kasar.

  14. Museveni ya yi Allah wadai da kasashen Turai kan batun sauyin yanayi

    Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ce soma amfani da kamfanonin ma'adinin coal da kasashen nahiyar Turai ke yi, a daidai lokacin da ake fuskantar karancin makamashi abin mamaki ne game da burin kasashen na cimma muradun sauyin yanayi.

    Daddaden shugaban kasar ya kuma soki sabbin dokokin da suka bayar da dama ga kasashen yamma wajen zuba jari a fannin ma'adinan makamashi a Afirka.

    Sharadin zuba jarin shi ne sai idan za a fitar da Man fetur da albarkatun iskar gas zuwa kasashen na Turai, abin da kuma shugaban ya kira 'tsantsar munafurci'

    Shugaban ya wallafa a shafinsa cewa 'Ba zamu amince da ikirarin samar mana ci gaba bayan da su kuma sun cimma muradun kasashensu kan batun sauyin yanayi ba''.

    Ya ce ''kiraye-kirayen da ake yi wa kasashen Afirka su rungumi amfani da makamashin da ba ya gurbata muhalli bai bar mu da komai ba sai rashin wutar lantarki''

    Ya kara da cewa rashin cimma muradun sauyin yanayi da kasashen Turai suka yi, ba zai zama matsala ga Afirka ba

  15. Faransa za ta janye sojojinta daga yankin sahel

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai yi jawabin kawo karshen ayyukan sojin kasarsa a yankin sahel

    Dakarun Faransa sun shafe shekara takwas suna yakar 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi a yankin.

    A watan Fabrairu ne dai Faransa ta bayyana aniyar janye sosojinta daga kasar Mali.

    Kimanin dakarun Faransa 5,500 ne ke aikin yaki da masu ikirarin jihadi a yankin na Sahel.

    A shekarar 2013 ne aka kaddamar da dakarun wadanda ake yi wa lakabi da 'Operation Barkhane' domin dakile yaduwar masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.

  16. Najeriya ta nemi hadin kan kasashen Afirka domin yakar miyagun kwayoyi

    Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA Manjo janar Buba Marwa mai ritaya, ya ce musayar bayanan sirri tare da karfafa hadin gwiwwa tsakanin kasashen Afirka zai taimaka wa kasashen nahiyar wajen yakar matsalar shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi.

    Buba Marwa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wajen taron shugabannin hukumomin yaki da miyagun kwayoyi na nahiyar Afirka da ke gudana a birnin Nairobi na kasar Kenya.

    Yayin da yake jawabi game da nasarar da Najeriya ta samu wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Buba Marwa ya ce ana bukatar hadin kan kasashen nahiyar wajen samar da hanyoyin da za a yaki dabi'ar safarar muggan kwayoyi a fadin kasashen nahiyar.

    Ya kara da cewa tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022, NDLEA ta kama mutum 21,302 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ciki har da manyan diloli 28.

    Haka kuma ya ce hukumar tasa ta kama miyagun kwayoyin da nauyinsu ya kai kilogiram miliyan 5.4, tare da sauya wa fiye da mutum 12,326 masu amfani da kwayoyin tunani.

  17. Amnesty ta soki hukunci da aka yi wa su Mubarak Uniquepikin

    Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da hukuncin da aka yanke wa matasan nan biyu masu amfani da shafin TikTok a jihar Kano saboda bata sunan gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

    Tun da farko dai matasan biyu masu suna Mubarak Muhammad alias wanda aka fi sani da Uniquepikin a shafin, da kuma Nazifi Muhammad, sun amsa laifinsu tare da neman sassauci daga kotu.

    An kuma yanke musu hukuncin bulala 20 kowannensu da kuma biyan tarar 10,000 tare da share kotu na tsawon wata guda.

    Kungiyar ta Amnesty International ta ce kama yaran tare da tsare su a gidan yari kafin a yanke musu hukunci abu ne da ya saba wa doka, ta kuma yi kira da a saki yaran ba tare da wani sharadi ba.

    Haka kuma kungiyar ta zargi alkalin da cewa mai bin umarnin gwamnatin jihar ne.

    Tuni dai aka fara zartar da wasu daga cikin hukunce-hukunce, inda aka yi musu bulalar a gaban jama'ar da ke harabar kotun, sannan kuma sun biya tarar.

    Lauyan matasan ya ce sun amince da hukuncin kotun, dan haka ba za su daukaka kara ba.

  18. El-Rufa'i ya yi amai ya lashe kan biyan kudin makaranta

    Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce tsarin biyan kudin makaranta ga daliban sakandiren jihar da ma'aikatar ilimin jihar ta bullo da shi ya ci karo da tsare-tsaren gwamnatin jihar.

    A baya dai ma'aikatar ilimin jihar ta fitar da sanarwar da ke cewa daliban sakandire a jihar za su fara biyan kudin makaranta

    A wata sanarwa da mataimakin gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu gwamnan ya bayyana tsarin ilimi kyauta a matsayin babban burin da gwamnatinsa ta sanya a gaba.

    Sanarwar ta ce gwamatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da tsarin ilimi kyauta ga daliban sakandire a fadin jihar.

  19. 'Yar madigo ta farko da ta zama gwamna a Amurka

    An zabi Maura Healey mace ta farko da ke bayyana kanta da cewa 'yar madigo ce a matsayin gwamna a jihar Massachusetts ta Amurka

    Ms Healey mai shekara 51 ta kayar da abokin karawarta na jam'iyyar Republican Geoff Diehl, wanda ke samun goyon bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump.

    Tana daya daga cikin 'yan madogo biyu da suka tsaya takarar kujerar gwamna a zaben bana.

    Daya 'yar madigon da ke takarar kujerar gwamnan ita ce Tina Kotek ta jihar Oregon.

    Can kuma a jihar Maryland Wes Moore na jam'iyyar Democrat ya zama bakar fata na farko da aka zaba a matsayin gwamnan jihar.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da wannan safiya ta Laraba da ake yi wa take da ta Bawa ranar samu.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu a wannan shafi domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sunana Abdullahi Bello Diginza, kuma ni zan ja ragamar wanna shafi a daidai wanna lokaci.