Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Naira na daga cikin kuɗaɗen da darajarsu ta fi faɗuwa a duniya - Bloomberg

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Wani mutum ya cinna wa dakin 'ya'yan matarsa wuta

    Rundunar 'yan sanda a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta kama wani mutum bisa zargin kunnawa 'ya'yan matarsa wuta.

    Jami'in hulda da jama'a a rundunar 'yan sandan jihar SP Funmilayo Odunlami ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran kasar faruwar lamarin a Akure babban birnin jihar.

    Ya ce lamarin ya faru ne ranar Asabar, inda ya ce jami'an 'yan sanda suna gudanar da bincike, yayin da yaran ke samun kulawar likitoci a babban asibitin Owo.

    Ya kara da cewa an mayar da batun zuwa ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar 'yan sandan jihar, domin gudanar da bincike yadda ya kamata.

    Wani shaida ya fada wa kamfanin dillacin labaran kasar NAN cewa mutumin ya kunna wuta a dakin da yaran ke kwance ne sakamakon samun 'yar rashin jituwa da matar tasa.

    Majiyar ta kara da cewa daya daga cikin yaran ya rasa ransa, sakamakon wutar.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiyar ranar Litinin, wadda ake yi wa kirari da Mande tushen aiki.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu a wannan shafi domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sunana Abdullahi Bello Diginza, kuma ni zan ja ragamar wanna shafi a daidai wanna lokaci.