Naira na daga cikin kuɗaɗen da darajarsu ta fi faɗuwa a duniya - Bloomberg
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi murna da sakin yaran da aka sace a Katsina
Asalin hoton, Getty Images
Majlisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da sakin yara 21 waɗanda masu garkuwa mutane suka sace su a jihar Katsina da ke Najeriya.
An sace matasan ne a lokacin da suke aiki a wata gona da ke ƙaramar hukumar Faskari.
A wata sanarwa da ya fitar, asusun tallafa wa yara na majalisar ɗinkin duniya (UNICEF) ya ce duk da ana murnar sakin yaran, to amma bai kamata a ce an sace su ba tun farko.
Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya a jihar Katsina Gambo Isa ya shaida wa BBC cewar an saki matasan ne a jihar Zamfara mai maƙwaftaka bayan tattaunawa da ƴan bindigan.
Sai dai bai fayyace ko an biya kuɗi kafin sakin nasu ba.
Za a bai wa ƴan sandan Najeriya sabbin kayan sawa da na aiki
Asalin hoton, @PoliceNG
Sifeta janar na ƴan sandan Najeriya Usman Alkali ya bayar da umurnin bai wa ƴan sandan ƙasar sabbin kayan sawa da na aiki domin su samu damar gudanar da aikin zaɓen shekara ta 2023 yadda ya kamata.
Baya ga sabbi kayan sarki, sauran kayan da za a bai wa jami'an ƴan sandan sun haɗa da na korar masu zanga-zanga, da rigar surke, da hular kwano, da hayaƙi mai sa hawaye da sauran su.
Sifeta janar na ƴan sandan ya ce waɗannan kaya za su taimaka wa ƴan sandan wajen gudanar da ayyukansu gabanin babban zaɓen ƙasar na 2023, da lokacin zaɓen da kuma bayansa.
Wannan umurni na zuwa ne bayan kayan da aka sayo na ƴan sanda domin inganta walwalar jami'an hukumar, yayin da ake ci gaba da ganin yadda za a tabbatar da ƙwarewa wurin aiki.
Sai dai IGP Usman Alkali ya buƙaci jami'an hukumar da su kare martabar aikinsu da kuma kare hakkin al'umma.
An rantsar da alƙalan da za su saurari ƙorafe-ƙorafen zaɓen 2023
Asalin hoton, STATE HOUSE
Shugaban
alƙalan Najeriya Olukayode Ariwoola ya rantsar da ƴan kwamitin da
zai saurari ƙararrakin zaɓen 2023 da za’a gudanar a ƙasar.
Shugaban mai shari’a Olukayode ya ce an ƙaddamar da
kwamitin ne domin fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen ƙasar da ke karatowa.
Da
yake rantsar da ‘yan kwamitin, mai shari’a Olukayode
Ariwoola ya ce an samar da kwamitin ne domin kawo ƙarshen, shari’u da ka
iya cin karo da juna.
Sai dai ya ja hankalin ƴan kwamitin sauraron zaɓen, da kar su
yi wa aikin da aka ba su riƙon sakainar-kashi.
Sannan ya garggi ƴan kwamitin da cewar ko kaɗan ba za su amince da
gangancin masu shar’ia a lokacin gudanar da aikin nasu ba.
Kotu ta yi wa mai gadi ɗaurin wata shida saboda barci a bakin aiki
Wata kotu a birnin Jos da ke jihar Filato a Najeriya ta yanke wa wani mai gadi hukuncin ɗaurin wata shida
saboda samunsa da laifin bacci a bakin aiki.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa a yayin yanke hukuncin a yau Litinin, kotun ta ce baccin da mai gadin Abubakar Haruna ke yi a bakin aiki yana bai wa ɓarayi hanyar satar rodi da rufin kwano da sauran abubuwa.
Alkalam da suka saurari karar da suka haɗa da Malam Sadqi Adam da kuma Mr Hyacenth Dolnanan, sun yanke hukuncin ne bayan da Haruna ya amsa laifinsa na yin ko oho da aiki.
Sai dai mutumin ya roƙi kotu da ta sassauta masa.
Alkalan sun yanke hukuncin ɗaurin wata shidan ne ko kuma tarar naira 10,000.
Sannan an buƙaci mai gadin da ya biya wanda yake ƙarar tasa naira 50,000.
Tun da fari, lauyan mai shigar da ƙarar, Ibrahim Gowkat ya shaida wa kotu cewa wani Adamu Ismail ne ya fara shigar da ƙarar ran 25 ga watan Agusta a ofishin ƴan sanda da ke Nassarawa Gwong.
Earlier, the Prosecution Counsel, Inspector Ibrahim Gowkat told the court that the case was reported at the Nassarawa Gwong Police Station on August 25, by Mr Adamu Ismail.
Ya ce Haruna yana gadi ne a gidan ƴar uwar Isma'il.
Baccin da mai gadin ya yi ya jawo ɓarayi sun shiga sun sace janareta da rufin kwano da rodi wajen 25.
Naira na daga cikin kuɗaɗen da darajarsu ta fi faɗuwa a duniya - Bloomberg
Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto
da jaridar Bloomberg da ke Amurka ta fitar ya bayyana takardar kudin Najeriya
wato Naira a zaman daya daga cikin wadanda darajarsu ta fi faduwa a duniya
yanzu.
A cewar rahoton darajar Nairar ta fadi da kusan kashi 37% a wannan
shekarar kawai.
A cewar
rahoton, Naira ita ce takadar kudi kasa ta biyu darajarta ta fi faduwa a
Nahiyar Afrika inda ka cire takardar kudin Cedi ta Ghana wadda darajarta ta
fadi da kashi 55% a bana.
Wadanda ke
bi ma Nairar wajen faduwar darajar a Afrika sun hada da Leone ta kasar Saliyo
wadda darajarta ta fadi da kashi 36% da kuma Fam din kasar Masar wadda ta rasa
kashi 35% na darajarta.
Sai dai
wani akasi inji rahoton darajar Naira na da armashi sosai har yanzu a canjin
gwamnati domin darajar ta fadi ne da kashi 4% dari kawai kan dalar ta Amurka
duk karfinta a bana.
Wanda hakan
ke nufi Naira tana gaba da dalar kasar Canada da Franc ta kasar Siwizland wajen
rike darajarta a kan kudin na Amurka.
Babban
bankin Najeriya dai ya kayyade yawan dalar yake sayar wa kowane rukuni na masu
bukatarta a kasar, abin da ya sa kamfanoni da daidaikun jama’a komawa nemanta a
kasuwar da ba ta hukuma ba.
Wannan in
ji rahoton shi ya sa aka samu bambacin kashi 90% dari tsakanin yadda gwamnati
ke canzar dalar a Najeriya da kuma yadda ake canza ta a wuraren canjin kudi
masu zaman kansu.
Rahoton ya
ambato wani dan canji a babban birnin kasuwanci kasar Legas na cewa an rufe
kasuwar canji a hukumance dalar na kan Naira 442 da kobo 75, a daidai lokacin
da take canza ta kan naira 890 a gefe titi.
Darajar
Naira ta fara rikitowa ne kwana daya bayan da babban bankin ya sanar da cewa
zai canza kudin kasar a wani yunkuri na rage yawan takardun kudi a bainar jama’a.
Jaridar ta
ambato wani masanin tattalin arziki a kasar na cewa mai yiwuwa darajar kudin
kasar ci gaba da faduwa saboda raguwar kudaden shiga da kasar ke samu daga
sayar da danyen mai da kuma karuwar fitar da kudi daga kasar saboda rashin
tabbas da ke tattare da zaben shugaban kasa da za a yi a watan Febrairu.
Wani makusancin Putin ya amince Rasha ta yi katsalandan a zaɓen Amurka
Asalin hoton, Reuters
Ɗaya daga cikin makusantan Shugaba Putin, Yevgeny Prigozhin ya amince cewa Rasha ta yi katsalandan a zaɓen Amurka.
Sakon da Mista Prigozhin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ana jajiberin zaɓen tsakiyar wa’adin mulki a Amurka da alama shi ne karon farko da wani fitaccen ɗan Rasha ya nuna amincewa da tsoma bakin da Rasha ta yi a zaben.
Amurka na zargin Mista Prigozhin da kula da wata hukuma wadda ta buɗe shafukan sada zumunta na bogi domin sauya ra’ayin jama’a.
Kuma a baya-bayan nan ne ya fito ya bayyana cewa shi ne ya ƙirƙiri ƙungiyar nan ta Wagner ta sojojin haya.
Jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna zai koma aiki a cikin Nuwamba
Asalin hoton, NRC
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a dawo da zirga-zirgar jiragen ƙasa na Abuja zuwa Kaduna a wannan watan na Nuwamba da muke ciki.
Ministan sufuri na ƙasar Mu’azu Sambo ne ya sanar da hakan a yau Litinin a yayin da yake faɗar nasarorin ma'aikatarsa a Abuja.
A ranar 28 ga watan Maris din 2022 ne aka dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasan Abuja zuwa Kadunan, bayan da ƴan bindiga suka kai wa jirgin hari suka kashe mutum 10 tare da sace wasu da dama.
Ministan ya ce an ɗauki tsauraran matakan tsaro don kare rayuwan fasinjoji kafin sanar da dawowar zirga-zirgar jiragen, sai dai bai faɗi taƙamaimai ranar da jiragen za su fara aikin ba.
Ministan ya ce ma'aikatar tasa ta koyi ɗumbin darasi daga harin da aka kai na watan Maris din da ya janyo dakatar da sufurin.
Wani fursunan siyasa na son a tattauna batun take hakkin mutane a Masar
Wani fitaccen ɗan fafutukar kare haƙƙin bil adama a Masar kuma tsohon fursunan siyasa ya buƙaci shugabannin duniya su yi amfani da taron sauyin yanayi na COP27 a matsayin kafa ta tattauna yadda ake take haƙƙoƙin bil adama a Masar.
Da yake magana da BBC, Hossam Bahgat ya buƙaci waɗanda suke halartar taron su yi magana don nuna damuwa ga mutanen da ake cin zarafinsu.
Akwai wasu da suke ganin kuskure ne a gudanar da irin wannan muhimmin taron na Majalisar Dinkin Duniya a ƙasar da ke da tulin bayanan cin zarafin bil adama.
Ya kuma buƙaci a gaggauta sakin Alaa Abd el-Fattah, wani ɗan gwagwarmayar siyasa da ke zaman shekara biyar a gidan yari bisa zarginsa da yaɗa labaran ƙarya.
Ana ci gaba da nuna damuwa game da lafiyarsa bayan da Mista el Fattah ya yanke shawarar daina shan ruwa baya ga yajin cin abinci na wata bakwai da yake yi.
Za a fara sauraron shari'ar Ekweremadu ranar 31 ga watan Janairu a Birtaniya
Asalin hoton, others
Kotun hukunta manyan laifuka da ke birnin Landan, a Birtaniya, ta sauya ranar fara sauraron shari'ar da take yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu daga watan Mayun 2023 zuwa 31 ga watan Janairun 2023.
An dai kama mista Ekweremadu tare da matarsa Beatrice ranar 23 ga watan Yuni da laifin safarar dan adam domin cire sassan jikinsa, abin da ya saba wa dokokin bautarwa na 2015.
Duk da cewa mista Ekweremadu bai halarci zaman na ranar Litinin ba, matarsa tare da wasu mutum biyu sun halarci zaman kotun.
A makon da ya gabata ne dai alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin kwace wasu kadarorin mista Ekweremadu, bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar da bukatar hakan a gaban kotun.
ASUU ta shiga ganawar sirri ta gaggawa
Asalin hoton, Asuu
Shugabannin Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ASUU sun shiga ganawar sirri ta gaggawa.
Jaridar Daily Trust Najeriya ta ruwaito cewa kungiyar ta shiga ganawar sirrin ne da tsakar ranar Litinin, a harabar sakatariyar kungiyar da ke jami'ar Abuja.
Ganawar karkashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke, za ta duba batun biyan malaman rabin albashin watan Oktoba.
Iyayen yaran da maganin tari ya kashe sun yi watsi da tayin diyyar dala dubu 20,000
Iyayen yara 70 da suka mutu sakamakon cutar koda, da ake zargin sun kamu da ita saboda shan wani maganin tari da aka yi a kasar Indiya, sun yi watsi da tayin diyyar dala 20,000 da gwamnati ta yi musu.
Ma'aikatar kula da cigaban al'umma ta kasar ce ta yi tayin bayar da diyyar dala 20,000 ga iyayen yaran domin su raba tsakaninsu.
Shugaban kungiyar iyayen yaran Ebrima Sanyang ya ce karbar tamkar kudin 'cin mutunci' ne ga yaran da suka mutu.
Ya ce karbar kudin na nuna cewa ba da gaske suke nema wa yaran adalaci ba.
Iyayen na bukatar hukumar da ke kula da magungunta kasar da ta janje kalaman da ta yi tunda farko, inda ta ce yaran sun mutu ne sakamakon ambaliyar ruwa, ba daga shan maganin tarin ba.
Suna kuma bukatar a hana hukumar kula da magungunan, gudanar da binciken da shugaban kasar ya yi kira da a gudanar.
A watan Oktoba Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi ga kasashen duniya cewa akwai wasu nau'in magungunan tari hudu da ke kawo lalacewar koda, bayan da aka samu rahotonnin da ke cewa an samu yaran Gambiya da matsalar cutar kodar bayan shan maganin.
To sai dai kamfanin da ke samar da magungunan mai suna 'Maiden Pharmaceuticals' ya ce yana bin matakan ingancin magunguna da duniya ta amince da su.
Za a dawo da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna cikin watan nan – Gwamnatin tarayya
Asalin hoton, NIGERIAN RAILWAY
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dawo da sufurin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna cikin wannan wata na Nuwamba.
Ministan sufuri na kasar Mu’azu Sambo ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja babban birnin kasar, yayin bayyana ayyukan da ma'aikatarsa ta yi
Ya ce an shirya jami'an tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji , to sai bai bayyana takamaiman ranar da za a fara jigilar ba.
Ministan ya ce hukumarsa ta koyi darussa daga harin da aka kai wa jirgin kasa a watan Maris, lamarin da ya sa aka dakatar da sufurin jiragen kasa tsakanin manyan biranen biyu.
Haka kuma ministan ya ce an yi wani tsari da zai rika lura da zirga-zirgar jiragen kasan da kuma titin jirgin.
Ya kara da cewa tsarin zai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ma'aikatu da hukumomin gwamnati da jami'an tsaro damar ganin abun da ke wakana a kan titin jirgin ba tare da bata lokaci ba.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da zirga-zirga jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna, bayan da mayakan Boko Haram suka kaddamar da hari kan jirgin kasan tare da sace fasinjoji masu yawa ranar 28 ga watan Maris 2022.
An nada alkalan da za su saurari korafe-korafen zabukan 2023 a Najeriya
Asalin hoton, others
Alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Olukayode Ariwoola ya rantsar da alkalan da za su jagoranci sauraron korafe-korafen zabukan kasar na 2023
An yi bikin rantsar da alkalan ne ranar Litinin a harabar hukumar da ke kula da harkokin shari'a ta kasar a Abuja babban birnin kasar
Yayin da yake nada alkalan babban alkalin alkalan kasar ya umarce su, da su dauki aikinsu da matukar muhimmanci, yana mai gargadinsu da cewa ba zai lamunci wasa da aiki ba.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da shugabar kotun daukaka kara ta kasar mai shari'a Monica Dongban-Mensem, da shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmood Yakubu, da kuma sauran alkalan kotun daukaka kara ta kasar.
Kotu ta yanke wa su Mubarak Uniquepikin hukuncin bulala ashirin
Asalin hoton, Mubarak unique pikin/TikTok
Wata kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa masu wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook bulala ashirirn-ashirin tare da hukuncin biyan tara ta naira dubu ashirin kowannensu da kuma share kotun na tsawon wata guda.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kokarin tada fitina a cikin al’umma, sannan kuma kotun ta umarcesu su koma kan dandalin na tiktok din su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje hakuri kan bata masa suna.
Matasan Mubarak Isa Muhammad da aka fi sani da Mubarak uniquepikin, da Nazifi Muhammad Bala, na shirya gajeren bidiyon barkwanci, inda akasari suke kwaikwayon muryoyin wasu fitattun mutane.
Mabarak Uniquepikin da abokinsa za kuma su share harabar kotun Norman Silance baki dayanta har na tsawon wata guda.
Lauyan da ya shigar da kara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa BBC cewa, na gurfanar da matasan ne a gaban kotun saboda laifukan da suka hada da bata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma kokarin tayar da fitina,
Inda kuma suka amsa laifinsu al’amarin da yasa aka yanke musu hukuncin, Lauya mai gabatar da kara ya ce an kama matasan tun makon jiya inda aka gurfanar da su a gaban kotun, kafin daga bisani kuma aka aika su gidan yari.
Matasan dai suna hannun jami’an tsaro har sai sun cika wadannan ka’ido kafin a sake.
Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci shi ne lauyan matasan ya kuma gode wa kotun majistaren bisa sassaucin da ta yi musu game da hukuncin, don haka ma basu kalubalanci hukuncin ba.
Hotunan Yadda fari ke kashe namun daji a Kenya
Mummunan fari mafi muni cikin shekara 40 da kasar Kenya ke fuskanta, ya sanya rayuwar namun dajin kasar musamman wadanda- da ke cikin gandun dajin Amboseli, gandun daji na biyu mafi girma a kasar - cikin hatsari
Tawagar wakilan BBC ta ga daruruwan dabbobin da ke shan wahala, yayin da wasu ke mutuwa saboda tsananin yunwa da kishi.
Mazauna garin sun shaida wa BBC cewa gomman dabbobin daji ne ke mutuwa a kowacce rana.
Tawagar ta BBC ta ga wata giwa da ta mutu bayan shafe gomma shekaru a gidan adana namun dajin.
Mazauna yankin sun ce wannan lamari na faruwa a kulli yaumin, kuma abu ne da suke fargabar yadda karshensa za ta kasance.
“Ba ma jin dadi. Saboda al'umar Maasai sun yi imanin cewa mutuwar manyan dabbobi irin su giwaye babbar masifa ce mai cike da hatsari'', in ji wani mazaunin yankin.
Duk da farin da ake fuskanta, mnasu yawon bude ido na cigaba da zuwa gidan namun daji a ranakun bukukuwan safari. Bukukuwan Safari na daga cikin manayn bukukuwan da ke jan hankalin masu yawon bude ido zuwa gabashin Afirka.
A makon da ya gabata ma'aikatar kula da masu yawon bude ido ta kasar Kenya ta ce kasar ta yi asarar giwaye 205, da rakumin dawa 400 da bauna 50 da kuma wasu dangogin dabbobin dawa da ake kira (wildebeest) 500, sakamakon mummunan farin.
A wannan makon gwamnatin kasar ta fara rarraba busasshiyar ciyawa da ruwa zuwa ga gidajen adana namun dajin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Sojoji sun kashe 'yan bindiga lokacin da suke girbi a gonakinsu
Asalin hoton, Getty Images
Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da rundunar Operation Hadarin Daji, sun ce sun kashe 'yan bindiga a kauyen Yar Tashar na Karamar hukumar Maru a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotonni sun ce an kashen 'yan bindigar ne a lokacin da suke girbe kayan amfanin gona da suka shuka a gonakinsu da ke kauyen.
Daraktan yada labarai na na hukumar tsaron kasar Manjo janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin da safe.
Ya ce a lokacin harin dakarun sojin sun kwato babur daya, tare da makamai da wasu kayayyaki daga wajen 'yan bindigar.
Jami'in sojin ya kuma ce dakarun kasar sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindigar a kauyen Gamraki na gundumar Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu a jihar.
Uganda ta kai hari ta sama kan 'yan tawaye a DR Congo
Kasar Uganda ta harba bama-bamai ta sama kan maboyar 'yan tawayen ADF a DR Congo a wajen yankunan da ba sa cikin inda kasar tare da kwabciyarta jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ke fada da 'yan tawayen ba.
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya cesai da Kasar Dr Kongo ta amince kafin aka kaddamar da hare-haren ranar 4 ga watan Nuwamba, tare da lalata babban sansaninsu.
Mista Museveni, wanda ya yada hotunan bidiyon hare-haren a shafinsa na Tuwita, ya ce 'yan tawayen sun fice ne daga inda ake gwabza fada su, sakamakon matsa musu da dakarun kawancen kasashen biyu ke yi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
“Jahilan 'yan tawayen ba su san cewa a cikin 'yan mintuna kalilan, za mu iya kashe su da ruwan wuta, a ko'ina suka shiga ba za su tsere wa bama-bamai ba'', in ji Museveni.
Mista Museveni ya alkawarta aiki tare da jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo wajen dakile ayyukan 'yan ta'adda, wadanda ya zarga da kai hare-haren bama-bamai a birnin Kampala kusan shekara guda da ta wuce.
Somaliya ta haramta amfani da kalmar 'al-Shabab' kan kungiyar 'yan ta'adda
Asalin hoton, AFP
Hukumar da ke kula da al'amuran addini ta Somaliya ta haramta amfani da kalmar al-Shabab - wadda a harshen Larabci ke nufin 'Matasa' - kan kungiyar 'yan ta'addan kasar.
Hukumar ta yi kira ga al'umar kasar da su kira kungiyar da sunan “Khawarij” wato wadanda suka yi tawaye.
Gwamnatin kasar ta ce umarnin kiran al-Shabab da “Khawarij” na daga cikin manufofinta na yaki da kungiyar.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Somaliya ke sanya wa al-Shabab wani suna ba.
A shekarar 2015 ma gwamnatin kasar ta shaida wa kafofin yada labarai da su rika kiran kungiyar da suna 'Ugus" wata inkiya da 'yan kasar ke yi wa 'kungiyar da ta yi wa 'yan kasar kisan kiyashi''.
A martanin da ta mayar, kungiyar ta yi gargadin hukunta duk wanda ya bi umarnin gwamnatin cikin har da 'yan jarida wajen kiranta da sabon sunan.
A watan da ya gabata, hukumomin kasar suka haramta wa kafofin yada labaran kasar yin labaran da suka shafi ayyukan kungiyar.
ICPC ta fara balaguro a wasu jihohin Najeriya
Asalin hoton, Website/ICPC
Hukumar da ke yaki da almundahana da sauran lafukan da suka shafi cin hanci ta ICPC a Najeriya ta ce ta fara sabon bincike kan yadda aka aiwatar da ayyukan mazabu 712 a fadin johohin kasar 20.
Mai magana da yawun hukumar Azuka Ogugua ta ce jihohin da za a gudanar da binciken ayyukan mazabun sun hadar da Kaduna da Jigawa da Sokoto da Katsina da Kwara da Niger da Kogi da wasu jihohin.
Ta kara da cewa ''a yayin da hukumar ta fara binciken tun shekarar 2019, manufar wannan sabon binciken shi ne bibiya game da hanyoyin da aka bi wajen bayar da kwagilar wasu zababbaun ayyukan mazabu a fadin kasar''.
"Manufar binciken shi ne tabbatar da cewa duka ayyukan da gwamnati ta fitar da kudi a kansu, an aiwatar da su a wuraren da aka tsara gudanar da su'', in ji Azuka
Ana ci gaba da neman goyon bayan masu kada kuri'a a zaben rabin wa'adi na Amurka
Jiga-jigan jam'iyyar Republican da takwarorinsu na Democrat a Amurka na kara azama domin ganin sun samu goyon baya yayin da ya rage kasa da sa'o'i 48 a kada kuri'a a zaben rabin wa'adi na 'yan majalisun dokokin kasar.
Zaben na da muhimmanci ga Shugaba Joe Biden da kuma wanda ya gada Donald Trump.
Kuri'ar jin raayi ta nuna cewa Republican za ta sake samun rinjaye a majalisar wakilai .
Yayin da hasashe kuma ya nuna cewa sakamakon wasu jihohin da ba a da tabbas game da wanda zai yi rinjaye a cikinsu,
shi ne zai tabbatar da jamiyyra da za ta samu rinjaye a majalisar dattawa.
Masu kada kuri'a sun bayar da fifiko kan batun tattalin arziki, ‘yan Democrat na mayar da hankali kan batun zubar da ciki da mallakar bindiga, yayin da 'yan Republican ke mayar da hankali kan karuwar miyagun laifuka, da kwararar baki da hauhawar farashi