Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Amira Souley ita ce gwarzuwar gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2022

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad, Umar Mikail and Haruna Kakangi

  1. Zan tattauna da 'yan IPOB idan na ci zabe - Peter Obi

    Dan takarar shugaban kasa a Najeriya na jam'iyyar Labour Party (LP), Mr Peter Obi, ya ce zai tattauna da 'yan haramtacciyar kungiyar nan ta masu fafutukar neman 'yancin Biafra (IPOB) da sauran masu fafutuka domin maido da zaman lafiya kasar, idan aka zabe shi.

    Mr Obi ya bayyana hakan ne a hira ta musamman da kafofin gidan jaridar Daily Trust, a Abuja yayin da yake amsa tambaya a kan matsalar tsaro a Najeriya.

    Dan takarar na jam'iyyar Labour wanda tsohon gwamnan Jihar Anambra ne, ya ce salonsa zai zama daban da na takwarorinsa kan wannan matsala idan har aka zabe shi a ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara mai kamawa 2023.

    Obi ya ce, ya sha nanatawa ba sau daya ba ba sau biyu ba, cewa Najeriya ba ta da masu fafutuka fiye da kasar Brazil.

    ''Idan kana so zan nuna maka kasashen da suka yi fama da masu fafutuk a baya, ko Brazil ce ko Mexico ce, ko wannan ce.

    ''A kudu maso gabashinmu abu ne mai sauki, zan yi tattauna, zan tattauna, dumukuradiyya ce kuma a mulkin dumukuradiyya kana mulki ne da cimma matsaya. Idan wani ya ce ba ya jin dadi, sai ka kira shi ka zauna da shi ka tattauna da shi,'' in ji Mista Obi.

    a

  2. Shugaba Bolsonaro na Brazil da ya sha kaye ya roki direbobin manyan motoci da suka datse tituna su yi hakuri

    Shugaba Jair Bolsonaro, wanda ya sha kaye a zaben Brazil, ya yi kira ga daruruwan direbobin manyan motoci da suka toshe hanyoyi su janye sannan su koma gida.

    Tun ranar Lahadi direbobin suka fara zanga-zangar kin amincewa da nasarar tsohon shugaba Luiz Inacio Lula da Silva.

    Matakin direbobin ya janyo karancin abinci da man fetur a kwanakin da suka dauka suna toshe hanyoyin, kodayake tun ranar Talata jami'an tsaro suka fara bude hanyoyin.

    Shugaban ya ce, ''na san kun fusata, ba abin da kuke so kuka gani ba. Ni ma haka nake ji da bakin ciki, amma dole mu yi taka tsantsan.

    Kuna da 'yancin yin zanga-zanga kamar yadda dumukuradiyya ta ba ku dama, amma toshe hanyoyin na cutar da jama'a.''

  3. Birtaniya ta janye shirinta na mayar da ofishin jakadancinta na Isra'ila Birnin Kudus

    Gwamnatin Birtaniya ta tabbatar cewa ba ta da niyyar mayar da ofishin jakadancinta na Isra'ila daga Tel-Aviv zuwa Birnin Kudus.

    Kakakin sabon Firaiminista Rishi Sunak, ne ya tabbatar da hakan a taron manema labarai.

    A watan Satumba da ya wuce, tsohuwar Firaiminista Liz Truss ta sanar da duba yiwuwar sauya mazaunin ofishin, lamarin da ya fusata Falasdinawa da suka ce hakan ya saba wa dokokin duniya

    Kuma hakan suka ce zai janyo karin tashin hankali a yankin wanda ya kasance ana fama da shi shekara da shekaru.

    Isra'ila na kallon birnin Kudus a matsayin bbban birninta, yayin da Falasdinawa ke ganin gabashin Kudus a matsayin nasu, inda Yahudawa 'yan kama wuri zauna suka mallake, da kuma suke fatan ya kasance babban birninsu nan gaba.

  4. Kotu ta daure kwamandan 'yan tawayen Liberia rai da rai

    Wata kotu a birnin Paris ta yanke wa tsohon kwamandan 'yan tawayen Liberia daurin rai da rai, kan laifin kitsawa da aikata laifukan take hakkin dan adam a lokacin yakin basasar kasar.

    Kunti Kamara ya kasance babban jami'i a kungiyar 'yan tawayen ULIMO, da ta jagoranci kashe-kashe da ayyukan ta'addanci a arewa maso gabashin kasar Liberia a shekarun 1990.

    Wannan ya kawo karshen makonni ukun da aka dauka ana shari'ar, inda shaidu sua bayar da bayanin tashin hankalin da suka gani.

    Sun bayyana yadda Kamara, ya kashe wani malamin makaranta a bainar jama'a, tare da cinye zuciyarsa. Ya kuma bar mayakansa suna ta yi wa wasu 'yan mata biyu fyade.

  5. Barkanmu da saduwa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis. Muhammad Annur Muhammad ne ke farin cikin kasancewa tare da ku a wannan lokaci, da muke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye.

    Bari na fara mana da wannan karin maganar; Raguwar Tsanya Ke Fara Tila