Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Amira Souley ita ce gwarzuwar gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2022

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad, Umar Mikail and Haruna Kakangi

  1. Gwarazan gasar ƙagaggun labarai ta Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2022

  2. Amira Souley ce gwarzuwar gasar Hikayata ta 2022

    Amira Souley (hannun hagu) daga garin Maraɗi na Jamhuriyar Nijar, ta zama gwarzuwar gasar ƙagaggun labarai ta BBC Hausa wato Hikayata ta shekarar 2022.

    Ta samu nasarar ce da labarinta mai taken 'Garar Biki'.

    Ta kuma samu kyautar kuɗi dala 2,000.

  3. Wadda ta zo ta biyu a gasar ƙagaggun labarai ta BBC Hausa ta Hikayata a 2022 ita ce Hassana Labaran.

    Labarin Hassana Labaran mai taken 'Haihuwar Guzuma' shi ne ya zo na biyu.

    Ta samu kyautar kuɗi dala 1,500.

  4. Wadda ta zo ta uku a gasar ƙagaggun labarai ta BBC Hausa ta Hikayata a 2022 ita ce Maryam Muhammad Sani.

    Labari mai taken 'Al’ummata' da Maryam Muhammad Sani ta rubuta daga birnin Kanon Najeriya shi ne ya zo na uku.

    Ta samu kyautar kuɗi dala 1,000.

  5. Farfesa Umar Pateh, shugaban jami'ar tarayyar tarayya da ke Kashere a jihar Gombe

    Farfesa Umar Pateh ya gabatar da muƙala a yadda BBC ta shafi rayuwar al'ummar duniya.

  6. Farfesa Muhammad Aliyu Bunza ya gabatar da muƙala a kan gudumawar BBC Hausa ga al'ummar Hausawa

  7. Shu'aibu Ibrahim Muhammad ne zakaran gasar waƙar cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa

  8. Musa Abubakar Tunga ne ya zo na biyu a gasar waƙar cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa

  9. Zainab A Baba ce ta zo ta uku a gasar waƙar cikar BBC Hausa shekara 65

  10. Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau shi ne ya jagoranci alƙalan da suka tantance waƙokin da suka yi zarra a gasar waƙoƙin cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa.

  11. Bukin karrama zakarun gasar Hikayata da ta cikar BBC Hausa shekara 65

    An fara gudanar da bukin karrama waɗanda suka yi zarra a gasar ƙagaggun labarai da BBC Hausa ke shiryawa a kowace sheraka (Hikayata) karo na bakwai.

  12. Yadda baƙi ke isa wurin bukin karrama gwarazan gasar Hikayata da waƙar cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa

  13. Tsohon shugaban Guinea Alpha Condé na iya fuskantar tuhumar rashawa

    Tsohon shugaban kasar Guinea Alpha Condé na iya fuskantar tuhumar rashawa bayan da sojojin da suka hambarar da shi a shekarar da ta wuce, suka gaya wa masu gabatar da kara su fara shirye-shiryen gurfanar da shi.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP wanda ya ruwaito labarin ya ce akwai wasu mutane sama da 180 da suma za su iya fuskantar shari'ar.

    Sojoji sun ƙwace mulki ne a watan Satumban shekarar 2021, inda suka zargi Mr Conde da rashawa da kuma take haƙƙin bil'adama.

  14. Ana gab da fara bukin karrama gwarazan gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2022

  15. An samu karuwar nuna kiyayya ga Yahudawa in ji Tarayyar Turai

    Wani bincike da Tarayyar Turai ta gudanar ya nuna cewa an samu karuwar rahotannin kiyayya ga Yahudawa sosai sakamakon annobar Korona da yakin Ukraine.

    Rahotan ya nuna yadda ake ta samun karuwar nuna tsana da yada bayanai na karya ta intanet a kan Yahudawa.

    Binciken ya ce ana ta farfado da bayanan bata suna da labarai na karya, tare da musanta tarihin kisan kiyashi da aka yi wa Yahudawa.

    Nazarin da kasashen Tarayyar Turai suka yi ya ce an samu karuwar hare-hare kan Yahudawa a tsawon lokacin mamayen da Rasha ta yi wa Ukraine, wanda ta yi ta hanyar halatta shi ta amfani da kalmomi irin su Nazi da kisan-kiyashi wajen kwatanta gwamnatin Kyiv.

    Rahotan ya lura cewa a kasashen Turai da yawa ba a bayar da rahoto ko cikakken rahoto a kan abin da ya shafi kiyayyar Yahudawa.

    A kasashen Hungary da Portugal babu wasu bayanai na hukuma a kan irin rahotannin gaba daya.

  16. Jam'iyyar Labour ta musanta labarin saukar shugabanta

    Jam'iyyar Labour Party, ko LP a takaice ta musanta labarin da ake ta yadawa cewa shugabanta na kasa Barrister Julius Abure ya sauka sannan kuma ya yi watsi da dan takararta na shugaban kasa Peter Obi.

    A wani sakon Twitter da jam'iyyar ta sanya ta ce abokan hamayya ne suke yada labarin cewa shugaban ya ajiye mukamin.

    A jiya Laraba ne wasu kafafe suka rika yada labarin cewa shugaban ya ajiye mukamin sannan kuma ya yi watsi da Mista Peter Obi wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

    Jam'iyyar kamar sauran takwarorinta ta shiga yakin neman zabe na dan takarar tata a fadin kasar, domin tunkarar zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.

    Za a yi zaben na shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki na tarayya a wannan rana ta 25 ga wata.

    Yayin da za a yi zaben gwamnonin jihohi da kuma 'yan majalisun dokoki na jiha ranar 11 ga watan Maris na 2023.

  17. Yarjejeniyar fitar da abinci daga Ukraine ba za ta manta da Afirka ba - Erdogan

    Shugaban kasar Turkiyya ya ce yarjejeniyar fitar da tsabar abinci daga Ukraine zuwa kasashen duniya za ta yi la'akari da kasashen Afirka da ke fama da karancin abinci.

    Recep Tayyip Erdogan wanda ya sasanta yarjejeniyar bayan da Rasha ta yi barazanar ficewa tare da hana fitar da abincin ya ce shi da Shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine sun tattauna batun aika wa da kasashen Afirka abincin.

    A hirarsa da gidan talabijin na Turkiyya ATV, Erdogan ya ce, "Halin da ake ciki a Djibouti da Somalia da Sudan ba shi da dadin ji ko kadan.

    Idan akwai matsala a wasu kasashe da ba su kai ci-gabansu ba, za mu kai abinci ga wadanna kasashe.''

    Majalisa Dinkin Duniya da Turkiyya ne suka shirya yarjejeniyar a watan Yuli, wadda ta kawo karshen wata biyar da Rasha ta yi ta hana fitar da tsabar abincin daga tashoshin ruwa na Ukraine, inda aka jibge tarin tsabar abinci da man girki, wanda hakan ya janyo tashin farashin kayan abinci a duniya.

    Yanzu a ranar 19 ga watan nan na Nuwamba ne yarjejeniyar za ta zo karshe, kuma wadanda abin ya shafa sai sun tsawaita ta.

    A wannan makon ne Rasha ta yarda ta koma kan yarjejeniyar bayan da a baya-bayan nan ta yi barazanar fice daga cikinta.

  18. An kama 'yan kasashen waje 18 da katin zabe a Jihar Oyo

    Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, reshen jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar ta ce ta kama ta kuma fitar da 'yan kasashen waje 18 saboda mallakar katin zabe.

    Shugaban hukumar a jihar, Isah Dansuleiman, ne ya bayyana haka a lokacin taron wayar wa da masu ruwa da tsaki kai game da zabukan da za a yi na 2023, a jiya Laraba.

    Take shirin shi ne: ''Zabe mai inganci a Najeriya : Abin da ake tsammani daga baki kafin lokacin da kuma bayan zabe.''

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, wato News Agency of Nigeria, (NAN) ya ruwaito, shugaban na nbayanin cewa, sun kama bakin ne a lokacin farmakin da suka kai a sassan jihar ta Oyo.

    Ya ce kasancewar bakin sun saba dokokin Najeriya a don haka aka fitar da su zuwa kasashensu.

    Ya yi gargadin cewa ba wani bako komai matsayinsa a Najeriya da zai yi zaben, kuma duk wanda aka kama da katin zaben zai fuskanci hukunci.

    Ya bukaci baki a jihar su zauna tare da gudabar da harkokinsu bisa doka idan har suna da takardun zama, amma kada su kuskura su shiga harkar zabe.

  19. 'Yan bindiga sun sace matar kwamandan Civil Defence a Jihar Nasarawa

    Wasu 'yan bindiga sun sace matar babban jami'in rundunar tattara bayanan sirri ta rundunar tsaro da bayar da agaji ta Najeriya da aka fi sani da Civil Defence, (NSCDC) a Jihar Nasarawa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa barayin sun je gidan Mukaddashin Babban Kwamanda Apollos Dandaura a Lafia babban birnin jihar, dauke da bindigogi kirar AK-47, inda suka rika harbi domin tsorata jama'a kafin su yi gaba da matar.

    Bayanai sun nuna cewa maharan sun harbi kanin kwamandan wanda shi ma jami'in rundunar ne a jihar, lokacin da suka kai harin da mislain karfe 8:30 na dare jiya Laraba.

    Kakakin rundunar a jihar ta Nasarawa Mr Jerry Victor, wanda ya tabbatar wa da jaridar lamarin ya ce har yanzu ba a gano inda 'yan bindigar suke ba.

    Ya kara da cewa jami'ai sun bazama domin ceto ta ba tare da wata illa ba. Sannan ya ce zuwa yanzu barayin ba su tuntubi rundunar ko iyalin ba.

  20. CAN ta ayyana Juma'a a matsayin 'Ranar Addu'a ta Ƙasa' a Najeriya

    Ƙungiyar Kiristoci a Najeriya ta Christian Association of Nigeria (CAN) ta ayyana Juma'a, 4 ga watan Nuwamba a matsayin Ranar Addu'o'i ta Ƙasa don nema wa ƙasar mafita a al'amuranta yayin da ake tunkarar babban zaɓe na 2023.

    Ƙungiyar ta gayyaci dukkan 'yan takara Kiristoci a babban zaɓen zuwa wurin taron da za a gudanar a Cibiyar Kiristoci ta Ƙasa da ke Abuja.

    "Za mu nemi kariyar Allah daga fitina, da maguɗi, da harzuƙa masu jefa ƙuri'a da kuma sauran laifuka yayin zaɓe mai zuwa," a cewar sanarwar da CAN ta fitar ranar Laraba.

    Ta ƙara da cewa ta shirya taron addu'ar ne "saboda yadda ƙasarmu ke fuskantar ƙalubala a yanzu duk da irin baiwar da Allah ya yi mata na mutane da ma'adanai".

    Mutum fiye da miliyan 90 ne ke da rajistar kaɗa ƙuri'a a Najeriya, kamar yadda hukumar zaɓe INEC ta bayyana, yayin da 'yan ƙasar za su su zaɓi sabon shugaba a watan Fabarairu bayan kammala wa'adi biyu da Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC zai yi a watan Mayun 2023.