Ambaliya ta kashe mutum 13 a Philippines
Akalla mutum 13 sun mutu a ambaliyar ruwa hade da zabtarewar kasa sakamakon mamakon ruwan da ake shekawa a kudancin Philippines, wanda ya janyo guguwar Nalgae.
Jami'ai a yankin sun ce wadanda lamarin ya ritsa da su sun fito ne daga garuruwan Datu Blah Sinsuat da Datu Odin Sinsuat a yankin Maguindanao.
Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutane a wuraren da aka ba da rahoton an samu ambaliyar ruwan.
Tun da fari masana yanayi sun ce za a fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya, kuma guguwar Nalgae za ta kara janyo zabtarewar kasa a ranakun karshen mako.