Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Wasu mutane sun kai wa mijin Nancy Pelosi hari a gidansa a Amurka

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Halima Umar Saleh

  1. Mu kwan lafiya

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa. Da fatan kun ji dadin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Halima Umar Saleh ke cewa asuba ta gari.

  2. Saudiyya za ta buɗe katafariyar makarantar koyon tuƙin mita a Makkah

    Nan ba da dawa ba za a kafa katafariyar makarantar koyon tuƙin mota a birnin Makkah na Saudiyya ƙarƙashin kulawar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa Muroor, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

    Girman makarantar koyon motar zai kai murabba'in kilomita 200,000, kuma ana sa rana za a kammala aikin a cikin wata takwas da fara shi.Injiniya Rami Yaghmour, mai sa ido kan makarantun koyon tuƙin mota na Saudiyya, ya tabbatar da cewa wannan aiki shi ne irinsa na farko da za a yi a Makkah kuma mafi girma a ƙasar.

    Makarantar ba gama garin motoci kawai za ta mayar da hankali wajen koyar da tuƙinsu ba, har ma da motoci na aikin musamman kamar na ɗaukar marasa lafiya da na ƴan sanda da na ƴan kwana-kwana, in ji Injiniya Yagmur.Kazalika za a dinga bayar da horo kan tuƙin babura da tasi da bas da kuma manyan motocin ɗaukar kaya.

  3. Ku saurari shirin Ra'ayi Riga na yau da ake yi a kan wayar da kai kan kansar nono

    Ku saurari shirin Ra'ayi Riga na yau da ake yi a kan wayar da kai kan kansar nono.

    Muna tare da likitoci da kuma wasu da ke fama da cutar.

  4. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce DSS ta ci gaba da riƙe Nnamdi Kanu

    Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja a Najeriya ta tabbatar da buƙatar da gwamnatin tarayya ta shigar ta neman hukumar tsaro ta farin kaya ta ci gaba da riƙe jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu.

    Hakan na nufin kotun ta sauya hukuncinta na farko na cewa a saki Kanu.

    Gwamnatin Najeriya ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli ne bayan da Kotun Daukaka Kara a ranar 13 ga watan Oktoba ta ba da umarnin sakin Kanu.

  5. DSS ta musanta kai samame wani gida a Abuja tare da sojojin Amurka

    Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya ta yi watsi da labarin da ke cewa jami’anta ƙarƙashin hadin gwiwar sojojin Amurka sun kai samame wani gida a Abuja, babban birnin ƙasar.

    Mai magana da yawun hukumar Dr. Peter Afunanya ne ya tabbatar wa kafofin yaɗa labarai wannan batu a ranar Juma’a.

    Rahotanni sun fara yaɗuwa a farkon wannan makon cewa jami’an DSS da sojojin Amurkan sun kai samamen ne wani gida a unguwar Lugbe inda suka kama wasu mutane da ake zargin ƴan Boko Haram ne tare da abubuwan fashewa da dama.

    Hakan na zuwa ne bayan da a farkon makon nan Amurkan ta fitar da sanarwa tana gargaɗin cewa akwai yiwuwar za a kai hare-haren ta’addanci a sassan Najeriya musamman Abuja.

    Kafar yaɗa labaran PR Nigeria ta ruwaito Dr Afunanya yana cewa “Ina shaida mkuku cewa babu wani samame da muka kai tare da sojojin Amurka kamar yadda ake yaɗawa.

    “Duk da cewa dai mun kai samame wani rukunun gidaje a Abuja tare da sauran hukumomi abokan aiki, to babu dakarun tsaron ƙasashen waje ko ɗaya a ciki,” ya ce.

    PR Nigeria ta ce a wani binciken ƙwaf da ta aiwatar kan zargin dakarun ƙasashen waje sun kai samame rukunin gidaje na Trademore, ya gano cewa “babu wasu ƙwararan hujjoji cewa sojojin Amurka sun kama wani a Abuja.

  6. Kenya za ta gabatar da tuhuma kan manyan ƴan sanda 12 a ƙasar

    Hukumomi a Kenya sun ce shirya tsaf don gabatar da tuhuma kan manyan ƴan sanda 12, bisa rawar da suka taka wurin haddasa tashin hankalin da ya faru yayin zaben kasar na 2017.

    Babban mai shgar da ƙarar, Noordin Haji ya ce manyan sojojin ke da alhakin azabtarwa da cin zarafi ta hanyar lalata har ma da kisa, da aka yi a Kisumu.

    Ya ce an yi aika-aika a yankin na Yammacin Kenya ciki har da kisan jariri ɗan wata shida.

    Sai dai kawo yanzu ba a bayyana sunayen ƴan sanda ba.

    A kalla mutum 12 aka kashe aka kuma jikkata ɗaruruwa a rikicin zaben.

  7. Kowa ya kasance cikin shiri amma a kwantar da hankula - Shugaba Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shawarci hukumoin tsaron ƙasar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka tsantsan da kula kan sha’anin tsaro, amma kuma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a guji tayar da hankula.

    A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a yau Juma’a, shugaban ya nemi ƴan ƙasar da su kwantar da hankali. “Sabbin matakan barin ƙasar da Amurka da Birtaniya ke ɗauka ba za su zama dalilan tayar da hankali ba.”

    Wannan magana ta shugaban ƙasar na zuwa ne a yayin da hankula ke ci gaba da tashi kan batun tsaro a Najeriya, tun bayan gargaɗin da Amurka da wasu ƙasashen yamma suka yi cewa akwai yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a ƙasar.

    “Najeriya ba ita kaɗai ce ƙasashen duniya ke bai yi wa gargadi kan barazanar ta’addanci da kuma bai wa ƴan ƙasashensu shawarar tafiye-tafiye ba.

    Amurka da Birtaniya na kuma yin gargaɗi kan yiwuwar hare-hare a ƙasashen yammacin Turai. Sannan sun bai wa ƴan ƙasarsu irin shawarwarin da suka fitar a Najeriyar.

    “Abin takaici ne cewa batun ta’addanci ya mamaye duniya.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa sai dai gargaɗin ba yana nufin lallai za a kai hare-haren ba, don tun bayan harin daka kai gidan yarin Kuje an sake tsaurara tsaro a ciki da wajen Abuja.

    “An daƙile hare-hare. Jami’an tsaro ne bankaɗo barazanar da ake fuskanta don tsaron ƴan ƙasa – sai dai mafi yawan ayyukansu ba a gani saboda ana buƙatar sirri.

    “Zaman lafiyar ƴan Najeriya shi ne mafi ƙololuwar burin gwamnati. Jami’an tsaro na aiki babu dare babu rana,” in ji sanarwar.

    Kazalika shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin cewa gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro.

  8. Wasu mutane sun kai wa mijin Nancy Pelosi hari a gidansa a Amurka

    An garzaya da mijin Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi asibiti, bayan wasu mutane sun kutsa kai gidansa.

    Rahotanni sun ce mutanen sun raunata Paul Pelosi mai shekara 82 a gidan nasa da ke San Francisco da safiyar yau.

    To amma jami'an tsaro sun yi nasarar kama su, duk da kawo yanzu ba a san dalilinsu na afka masa ba.

    Mai magana da yawun iyalin Mr Pelosi ya ce yana samun sauki kuma suna fatan zai warke sarai.

  9. Mahaifin ɗan sandan da abokin aikinsa 'ya kashe' shi a Kebbi yana so a bi masa hakkinsa

    Mahaifin ɗan sandan nan da ake zargin abokin aikinsa ya kashe shi a jihar Kebbi da ke Najeriya sanadiyyar saɓani tsakaninsu, ya nemi hukumomin ƙasar su bi wa iyalinsa hakki.

    Sani Shua’aibu Malumfashi, a tattaunawarsa da BBC kan kisan ɗan nasa ya ce a shirye yake ya bi kadin lamarin har sai an yi wa iyalan nasa adalci.

    Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar ta Kebbi dai ya tabbatar wa BBC cewa tuni aka kai batun kisan na ASP Shu’aibu Sani sashen binciken manyan laifuka na rundunar da ke Kebbi, domin gano gaskiyar abin da ya faru.

  10. 'Yan sandan Imo sun daƙile hari tare da kashe ɗan bindiga

    Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo a kudancin Najeriya ta samu nasarar murkushe wani yunkuri da ‘yan bindiga suka yi na kai hare-hare a jihar.

    'Yan sandan na zargin maharan da kasancewa mambobin kungiyar IPOB da ke neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya.

    Jami’an sun samu nasarar kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar shida da kuma kwato makamai da bindigogi da albarusai.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman:

  11. Ƙarin ƙasashe biyar sun bayyana fargabar harin ta'addanci a Abuja

    Ƙarin ƙasashe biyar sun bi sahun Amurka da Birtaniya wajen bayyana fargabar kai harin ta'addanci a Abuja babban birnin Najeriya tun daga ƙarshen makon da ya gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Amurka ce ta fara bayyana damuwa a ranar Lahadi, tana mai cewa akwai yiwuwar kai hari kan gine-ginen gwamnati da wuraren taruwar jama'a, kafin a ranar Juma'a ta umarci wasu ma'aikatan difilomasiyyarta su fice daga binin tare da iyalansu nan take.

    Jim kaɗan bayan haka Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya ma ya gargaɗi 'yan ƙasarsa da su ankare kuma su guji yawo a Abuja tare da kauce wa shiga taron jama'a.

    Ƙasashen Jamus da Bulgeriya da Ireland da Kanada da Denmark sun bi sahu, inda suke cewa akwai yiwuwar 'yan ta'adda za su kai hare-hare sannan suka nemi 'yan ƙasashensu su yi taka-tsantsan ko kuma su fice daga birnin.

    Sai dai Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya jaddada cewa babu wata fargabar kai hare-hare a Abuja, bayan ya umarci jami'ansa da su tsaurara tsaro a kewayen Abuja.

    "Saboda haka IGP na kwantar wa da mazauna Abuja hankali tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yayin da aka shirya tsafi don daƙile barazanar tsaro da kuma amsa kiran gaggawa a kan lokaci," in ji sanarwar da kakakin 'yan sandan ya fitar ranar Alhamis.

  12. Wani maganin tari ya kashe yara 157 a Indonesiya

    Gwamnatin Indonesia ta ce akalla kananan yara 157 ne suka mutu kawo yanzu, bayan sun kamu da cutar koda a dalilin shan wani maganin tari.

    Ma'aikatar lafiya ta ce 73 sun rayu bayan yi musu magani a asibiti.

    Mafi yawansu ƴan ƙasa da shekaru biyar ne.

    Yanzu haka hukumomi sun dakatar da kamfanin har sai an kammala binciken gano yadda aka yi hakan ta faru.

    Makonni uku da suka wuce ma Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin a daina amfani da wani maganin tari da ya fito daga Indiya, wanda ke da alaƙa da mutuwar yara 70 a Gambia.

  13. Amurka ta shiga tsakani a rikicin Isra'ila da Lebanon

    Isra'ila da Lebanon sun ƙulla wata yarjejeniya mai cike da tarihi da Amurka ta shiga tsakani, wadda za ta shafe wa kasashen hanyar tono albarkatun gas aka daɗe ana kai ruwa rana kansu.

    Arzikin na shimfiɗe ne a kan iyakar kasashen biyu, kuma a yanzu shugabanninsu sun saka hannu don ganin kowa ya cika lalitarsa.

    Kadan ya rage yaƙi ya ɓarke tsakanin Lebanon da Isra'ilan kan ikon mallakar yankin da gas din yake.

    Ba a jima ba da kungiyar Hezbollah ta yi barazanar kai wa Israila hari matsawar ta yadda ta fara hakar gas din ba tare da amincewar Lebanon ba.

    Sai dai duk da kulla yarjejeniyar cin arzikin, har yanzu kasashen biyu ba sa huldar diflomasiyya, kuma ba a shiri ko kadan.

    Kowane ɓangare ya saka hannun ne a kasarsa, daga nan aka yi musayar takardun amincewar a kan iyaka, alamar da ke nuna cewa zaman doya da manja na nan.

  14. Kotu ta ɗaure matashi ɗan kirifto a Kaduna saboda zamba ta Instagram

    Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ɗaure matashi mai harkokin kuɗi ta intanet wato Cryptocurrency tsawon wata uku a gidan yari bayan ta kama shi da laifin zamba.

    Mai Shari'a Darius Khobo ya yanke wa Emmanuel Simon hukuncin ne a ranar Alhamis bayan hukuamr EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da shi a gaban kotunsa bisa zargin aikata zamba ta intanet.

    An tuhumi Mista Simon da yin amfani da shafin dandalin zumunta na Instagram ɗauke da sunan Hakc4ord da kuma Mrs Gina daga jihar California ta Amurka.

    Rahoton shari'ar da EFCC ta wallafa ranar Juma'a ya ce matashin kan tura wa mutane saƙon cewa su zuba jari a harkar kirifto tare da yi musu alƙawarin za su samu riba cikin kwana bakwai.

  15. Gwamnatin Tanzania ta fara kasafta ruwan sha a Dar es Salaam

    Hukumomi a Tanzania sun fara kasafta ruwan sha a Dar es Salaam babban birnin ƙasar saboda janyewar da Kogin Ruvu ya yi.

    Kogin ya yi ƙasa sosai, abin da ya jefa mazauna birnin cikin rashin lita miliyan 166 na ruwan sha a kullum.

    Mazauna Dar es Salaam za su shafe awa 24 ba tare da ruwan famfo ba a ranakun da ba ranarsu ba ce har sai ruwan kogin ya ƙaru.

    Shugaban da ke kula da birnin, Amos Makalla, ya ce an ɗauki matakin kasafta ruwan ne sakamakon tsawon lokaci da aka ɗauka cikin yanayin fari.

  16. Imran Khan zai jagoranci tattakin kilomita 400 a Pakistan

    Nan gaba a yau ake sa ran tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan zai jagoranci tattaki ko kuma maci da magoya bayansa suka shirya daga kudancin Lahore zuwa Islamabad.

    Mista Khan ya ce za su tsaya a biranen da ke kan hanya kafin su kammala tattakin na kusan tafiyar kiliomita 400 a mako mai zuwa.

    Wakiliyar BBC ta ce tsohon firaiministan ya sake yunkurowa domin matsa wa gwamnati lambar gudanar da zaɓe.

    Tun bayan sauke shi daga kan mulki a watan Afirilu, Imran Khan ya kara zage damtse don faɗaɗa siyasa da magoya baya da gangamin siyasa.

    Gwamnatin Pakistan ta sha alwashin hana su shiga Islamabad tare da girke jami'an tsaro 30,000 a sassa daban-daban na birnin.

  17. 'Yan sandan Jihar Sokoto sun kama mutum ɗauke da katin zaɓe 101

    Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen Jihar Sokoto ta yi kira ga mazauna jihar da su je su duba katikan zaɓensu bayan ta kama wani mutum ɗauke da katin zaɓe 101.

    Kakakin 'yan sandan jihar ya faɗa wa BBC Hausa cewa kwamashinan 'yan sanda ne ya gabatar da Ahassan Idris bayan sun kama shi a yankin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.

    A baya-bayan nan akan kama mutane da ɗumbin katin zaɓe da ake zargin 'yan siyasa ne masu yunƙurin amfani da su don yin maguɗin zaɓe watanni ƙalilan kafin babban zaɓen ƙasar na 2023.

    DSP Sanusi Abubakar ya yi wa Umaymah Sani Abdulmumin ƙarin bayani a wannan sautin da ke ƙasa:

  18. Babu barazanar tsaro a Abuja - IGP Usman Alkali

    Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya jaddada cewa babu wata fargabar kai hare-hare a Abuja babban birnin ƙasar.

    A ranar Lahadi ne Amurka da Birtaniya suka gargaɗi 'yan ƙasashensu cewa 'yan ta'adda na shirin kai hare-hare a birnin, inda suka shawarce su da su ankare. Sauran ƙasashe kamar Jamus da Australiya da Kanada da Ireland duk sun bayyana fargabar kai hari a birnin.

    A ranar Juma'a kuma Amurka ta umarci jami'an diflomasiyyarta da iyalansu su gaggauta ficewa daga Abujar sakamakon fargabar da ake da ita ta kai harin ta'addanci.

    Cikin wata sanarwa daga kakakin 'yan sandan Najeeriya Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Alhamis, IGP Alkali ya tabbatar wa 'yan ƙasar wajen da ma mazauna Abuja game da tsaron lafiyarsu, yana mai umartar jami'ansa da su tsaurara tsaro a kewayen Abuja.

    "Saboda haka IGP na kwantar wa da mazauna Abuja hankali tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yayin da aka shirya tsafi don daƙile barazanar tsaro da kuma amsa kiran gaggawa a kan lokaci," in ji sanarwar.

    • Haɗarin takaddama tsakanin Najeriya da ƙasashen waje kan batun tsaron ƙasar
  19. Buhari ya koma Najeriya daga Koriya ta Kudu

  20. Amurka ta umarci ma'aikatan difilomasiyyarta su fice daga Abuja

    Amurka ta buƙaci wasu daga cikin jami'an diflomasiyyarta da iyalansu su gaggauta ficewa daga Abuja babban birnin Najeriya sakamakon fargabar kai harin ta'addanci a birnin.

    Ofishin jakadancin Amurka a ke Abujar ya bai wa Amurkawa shawarar kar su yi balaguro duk da cewa babu cikakken bayani kan ainahin irin hatsarin da za a fuskanta.

    A ranar Laraba Amurka ta fitar da gargaɗi irin wannan a kasar Afirka ta Kudu. Sanarwar ta bukaci Amurkawa mazauna yankin Sandton na masu kuɗi a birnin Johannesburg su guji shiga taron jama'a a karshen makon nan.

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce abin takaici ne a ce Amurka ba ta tuntube shi ba kafin ɗaukar wannan matakin.