Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An rufe rukunin shagunan Jabi Lake a Abuja saboda fargabar rashin tsaro

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Mahara sun kashe masu ibada 15 a Iran

    Hukumomi a Iran sun ce aƙalla mutum 15 ne suka mutu a loƙacin da aka kai hari wani wurin bauta da ke kudancin kasar.

    Kafar yaɗa labaran Iran ta rawaito cewa wasu mutum 19 sun ji mummunan rauni lokacin da aka bude wuta kan masu ibada a yammacin Laraba a wurin bauta na Shah Cheragh da ke yankin Shiraz.

    Cikin hotunan da kafar talbijin ɗin ta nuna, an ga yadda jini yake malala ta kasan ginin, yayin da mutane ke ta gudu, wasu da rauni, wasu na kokarin taimakon wadanda suka fadi.

    Shugaba Ebrahim Raisi ya dora alhakin harin kan masu tsaurin kishin Islama mabiya Sunna.

    Ƙungiyar ISIS mai iƙirarin jihadi ta ɗauki alhakin kai harin.

  2. Assalamu Alaikum

    Ma'abota BBC Hausa, barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye da zai kawo rahotanni daga sassan duniya tare da Umar Mikail.

    Za mu fi mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Da fatan kun wayi hantsin Alhamis lafiya.